Tuesday, 15 May 2018

TARIHIN SARKI MOULAY ISMAIL SHARIF

TARIHIN SARKIN MOROCCO, MOULAY RASHID ISMA'IL.


Daga Sadiq Tukur Gwarzo, RN.
        08060869978
   An haifi Moulay Ismail Rashid a wajajen shekarar 1646 a birnin Fez na kasar Morocco. Ya gaji mulkin Morocco ne tun yana da shekaru 26 a duniya bayan da ɗan uwansa mai mulki ya faɗo daga kan doki ya mutu.
   A wancan lokacin Moulay Ismail ya samu daular Moroco rarrauna saboda yawaitar faɗace-faɗace tsakanin kabilu gami da rikicin sarauta da yayi tsamari a daular. Baya da haka ma, birnin Marrakesh yayi bore ga shugabancinsa, inda mutanen garin suka shiga biyayya ga ɗan amminsa mai suna Ahmad ibn Muhriz.
    Don haka da fara mulkinsa, sai ya jagoranci runduna zuwa Marrakesh dake kudancin birninsa, ya faɗawa garin da yaki har kuma yaci nasarar kwace ikonsa, amma sai shugaban boren Ahmad bn Muhriz ya tsere ba tare da an kame shi ba.
   Sarki Moulay Ismail na ɗaya daga cikin sarakuna masu karfin iko waɗanda duniya ba zata taɓa mancewa da sunansu ba.
 Da fari dai, ya ɗauke cibiyar daularsa daga birnin Fez zuwa Meknes, sannan ya umarci a kawata ganuwar birnin da kawunan sojojin abokan hamayya guda dubu goma.
  Ance akalla a kusan shekaru hamsin dayayi yana mulki, ya kashe mutane sama da dubu talatin waɗanda yawancinsu barorinsa ne, ɓata masa rai sukayi kurum, ko kuma ace lalacinsu ne ya isheshi sai yasa a kashe su.
  Wasu kuma ya sanya a kashe sune saboda ayyukansu bai gamsar dashi ba. Domin ance shi makarancin littafin alkurani mai girma ne, kuma indai yana bisa doki, yana umartar barori su bishi ɗauke da alkurani a buɗe yana mai karantawa, amma fa da zarar sun aikata abinda ya sosa masa rai sai ya sare kawunansu.
 Sarki Moulay Ismail ibn Sharif ya shahara wajen gwabza yakuna da makwabtansa, sannan ya ciri tuta wajen kawata babban birninsa, domin shine sarkin daya umarci ayi gine-gine masu kayatarwa a birnin Meknes, misalin makarantu, masallatai, lambuna da wuraren hutawa da kuma ganuwa ga wannan birni.
  Haka kuma yayi gagarumin faɗa da daular Ottoman wadda cibiyarta ke kasar Turkiyya, anan ne har ya samu nasarar 'yantar da kasar Morocco daga karkashin wannn daula.
  A shekarar 1981 Sarki Moulay Ismail ya gwabza yaki da turawan Kasar Spain tare da karɓe ikon birnin 'La Mamora' mai ɗauke da tashar teku, inda ya sauyawa birnin suna izuwa al Mahdiya.
  A lokacin wannan yaki, wakilin sarkin mai suna Kaid Omar ya faɗawa Sifaniyawan cewa idan suka mika wuya ba zasu bautar dasu ba, wanda hakan ya karfafa musu guiwar dakatar da gwabza yaki bisa tsammanin samun adalci, amma bayan anci nasara, sai Sarkin yaga cewa sam ba zai iya barin sifaniyawa sama da dubu biyu masu ɗauke da kyawawan mataye da kayayyaki masu daraja ba sasakai, sai kawai ya bada umarnin a taso keyarsu zuwa birnin Meknes a matsayin ganimar yaki.
 A shekarar 1684 Moulay Ismail ya kwace ikon birnin Tangier wanda a lokacin turawan Portugal ke iko dashi, haka kuma a shekarar 1689 ya sake karɓe ikon wani babban birni mai suna Larache daga hannun turawan sifaniya.
  Bunkasar wannan sarki takai yadda sai daya tara rundunar mayaka bakaken fata mai ɗauke da akalla soji dubu goma sha biyar, dasu ya haɗa da nashi wajen yaki ta yadda sai daya karɓe ikon ɗaukacin kasar Morocco daga hannun turawa idan aka ɗauke yankunan Ceuta da Melilla.
  Akwai labaru masu nuna gwagwarmayar daya buga da faransawa, tunda ance ya kame wasunsu masu zuwa leken asiri kasarsa tare da mayar dasu bayi, amma wasu na ganin kasancewar a lokacin sarkin Faransa Louis na 14 yana kiyayya da Sipaniyawa, ance akwai zumunta maikyau a tsakaninsa da Sarkin na Meknes.
  An kuma ruwaito cewa Sarki Moulay Ismail na Morocco ya taɓa aikewa da jakada mai suna Muhammad Temimin domin nema masa auren gimbiyar Faransa  mai suna Marie Anne de Bourbon amma sai taki amincewa, sai dai duk da haka alaka mai kyau taci gaba da ɗorewa a tsakaninsu.
   A iya tsawon rayuwar Sarki Moulay Ismaïl, ance ya haifi 'ya'yaye guda 867, maza guda 525 da mataye 342. Ance baya da mataye guda huɗu da yake dasu, akalla yana da kuyangi guda 2,000, kuma an ƙlisssafta cewar a kalla a tsawon shekaru tamanin da yayi a raye, a shekarunsa sama da hamsin bisa karagar mulki akullum yana jima'i sau biyu, ko kuma da mataye guda biyu.
 Don haka sunansa ya shiga tarihi a matsayin wanda yafi kowanne namiji yawan haihuwa anan duniya a iya abinda ya fito ga sanin masana zuwa yau.
  Bayan rasuwar Moulay Ismaïl a shekarar 1727, rikici ya kara ɓarkewa tsakanin 'ya'yansa bisa wanda zai gajeshi a mulki, daga karshe wani ɗansa Muhammad yayi galaba, tare da ɗorawa akan gine-ginen da mahaifinsa ya soma. Sai dai girgizar kasar data auku a birnin Meknes  cikin shekarar  1755 ce ta lahanta kusan ɗaukacin waɗannan gine-gine, daga karshe tilas Sarki Muhammad ya ɗauke cibiyar birnin daga nan inda ya maida ita zuwa birnin Marrakesh.


Macen da tarihi ya kiyaye a matsayin wadda tafi kowacce yawan haihuwa itace Mrs Vassillev  ta birnin Moscow, wadda ta rayu tsakanin shekarun 1725 - 1765.  Ance tayi nakuda sau 27,  sau 16 tana haihuwar tagwaye, ta haifi 'yan uku sau bakwai, ta haifi 'yan huɗu sau huɗu. Jimilla ta haifi 'ya'yaye 69 reras.. (Kimiyya ta tabbatar da haka)

Tuesday, 1 May 2018

TARIHIN KABILAR BABUR DAYADDA DABIUNSU NA AURE SUKE

BABUR MARRIAGE CULTURE AND RITUALS

TARIHIN KABILAR BABUR DA AL'ADUNTA NA AURATAYYA

DAGA SADIQ TUKUR GWARZO, RN

Kabilar Babur tana danganta asalinta ne da Mutanen Yamen, don haka aka ruwaito cewa rundunar wasu mutane ne sukaƴi hijira daga Yemen a wajajen shekara ta 600 miladiyya suka riski Kasar Sudan, sannan suka shigo cikin sahara tare da sauka a yankin da Kabilar Babur ke rayuwa a yanzu cikin kasar Borno.
   Ba iya kabilar Babur ba, har kabilun Kanuri da Luguda da wasunsu dake rayuwa a wannan yankin suna ikirarin asalin kakanninsu daga Yemen suke. Gusawar zamani ne kurum ya sanya takamaimen tarihinsu ya sauya.
   Zuwa yanzu dai, ana samun kabilar Babur ne a Jihohin Borno da Adamawa.
  A jihar Borno, akwai kabilar Babur a garuruwan Biu, Hawul, Kwaya kusar, Shani, Kwajaffa, Sakwa, Marama, Shaffa, Wandali, Kida, Miringa, Buratai, Zuwa, Yimirshika ,Hyera ,Dayar, Fumwa, Azare, Gwaski, Diragina, Yimana, Gwallam, Tiraku, Shindiffu, Goski, Pela Birni, Wangdang, Bula tawewe, Kogu Tashan Alade, Kida, da hang shang  da kuma Bayo, amma a jihar Adamawa kabilar Babur sunfi yawa a garin Garkida cikin karamar hukumar Gombi.
  Dukkan waɗannan garuruwa da Kabilar Babur ke zaune ciki nada nasu tarihin.
  Misali, ance jarumin daya kafa daular mulki ta Biyu mai suna Yamta, ɗane ga wata mace 'yar kabilar Mandara.
  Wai Tun tana da cikinsa aka ɗauke ta zuwa gidan Sarkin Borno, don haka acan aka haifeshi kuma acan ya taso da tarbiyar kanuri.
  Amma da Yamta ya girma, sai ya tumbatsa wajen jarumta. Shine fa harbya karɓe ikon yankin da Biu take ayau tare da kafa masarauta.
   Ana ganin ya fara kafa mazaunin masarautar sane a wani wuri mai suna 'Limbur' tsakanin chikorkur da Mandagarau. Har zuwa yanzu kuma ance kabarinsa yana nan a Limbur ɗin.
  Kabilar Babur, sune keda rinjaye a garin Biu da wasu garuruwan makwabta, amma akwai kuma kabilar Bura wadda ke zaune a makwabciyar kasar Babur ɗin, mai suna 'Babur Bura'. Dukkansu kusan da yare ɗaya suke amfani, kuma yaren yana da kamanceceniya dana garuruwan Chibok, Marghi, Higgi , Kilba and Bazza.
 Anfi samun kabilar 'Babur Bura' a jihohin gabashin Nigeria, watau Borno, Adamawa, Gombe da Yobe.
  AL'ADUN AURE
Mafi yawan kabilun Borno musamman Kanuri, Shuwa Arab da Babur nada kamanceceniya wajen al'adun auratayya. Watakila hakan ya faru ne saboda jimawar kabilun wajen zaman tare ko kuma ana iya cewa kakanninsu ne ɗaya, don haka daga garesu sukayo gadon ɗabi'un.
  Bisa al'ada ta Kabilar Babir, Idan namiji yaga mace yana so, to bazai sanar mata ba, sai dai ya nemeta da abota.
  A wannan abotar ne zai rinka bincikar halayyarta dana magabatanta, ba tare da ta sani ba, daga bisani kuma sai ya samu wani dattijo a danginsa ya ɗora masa alhakin kammala masa bincike akan yarinyar da zuriyarta duka.
  Daga wannan matakin kuma sai mai neman auren ya zaɓi maza uku da mata biyu akalla, daga danginsa su rakashi gidan su yarinya.
   Anan ne zasu haɗu da iyayenta ko 'yanuwanta, har kuma a tambayeta abinda ke tsakaninsu da wannan mai neman auren nata, da kuma muradinta akansa da sauransu.
  Idan an aminta a kulla auratayya, to daga nan ne za'a sanya ranar yin Baye, suna kiranta 'Yuyma'.
  Idan ranar tazo, dangi zasu haɗu daga ɓangaren namiji da mace maza da mata a gabatar da kayan ci dana sha, sanna a sanya ranar aure, watau “Mbwa Nyika”.
  Dangane da batun kuɗin aure ko sadaki, namiji na iya bayar da dukkan abinda ya samu gareshi ga iyayen wadda yake so ya aura, sukuma zasu ciri wani abu kaɗan su mayar masa da ragowar, (wasu ma ance basa cirar kome), to amma za'a gabatar masa da sunayen wasu abubuwa da akeso ya siya mata.
  A hakan ma, ba dole bane ya siyi dukkan komai ba, kawai dai yana iya zaɓar abinda yake da iko ne ya siya.
  Idan namiji ya haɗa kayan, sai ya tashi yan uwansa su tafi sukai gidan su yarinya. Daga nan kuma za'a saurarar ranar ɗaura aure.
  Daura aure kuwa ya danganta da addinin da mutum yakebi, kasancewar addini yayi tasiri cikin kabilar Babur, don haka kiristocin cikinsu sukanje chochi ne domin ɗaura aure, yayin da musulman cikinsu kan ɗaura aure a Masallatai ko gidaje, tare da aiwatar da al'adun aure kalar wanda musulunci ya halatta