TARIHIN DAURA
Sadiq Tukur Gwarzo
Bisa tsohon Littafin tarihi na masarautar Daura da ake masa laƙabi da suna Girgam kamar dai sauran littattafan tarihin yawa-yawan masarautu, ana ganin cewar tun a wajajen shekaru dubu biyu kafin haihuwar Annabi Isah A.S wasu mutane ƙarƙashin jagorancin shugabansu mai suna Najib (Wasu sunce Nimroid ko Namarudu sunansa) suka yo hijira daga ƙasar su ta haihuwa Kan'ana tare da riskar inda ƙasar Daura take a yanzu.
Babu takamaimen dalilin tasowar su, amma dai ance akan hanyar su ta tafiya, sun yada zango a tsohuwar Misira tsawon wani lokaci har kuma daga bisani wasu Misirawan na dauri suka shigo cikinsu akayi hijirar tare dasu.
Ance kuma da suka baro Misira sai suka shigo cikin ƙasar Libya, inda suka sauka a birnin Tarabulus, a zamanin da wani Sarki mai suna Abdurdaar ke mulkinta har yaso ya mallake wannan runduna amma bai samu nasara ba, daga ƙarshe shi Najib ya cigaba da tafiya da mutanensa har suka riski wani wuri da ake kira Tsohon birni, inda suka fara kafa birnin Daura kenan kafin daga baya mazaunan birnin su koma sabuwar Daura.
Amma, manazartan wancan littafi irinsu M.G Smith a littafinsa 'Affairs of Daura' ya kawo cewar Najib shine sunan jagoran waccan runduna data taso daga Kan'ana zuwa Falasɗinu, a lokacin tana ƙarƙashin ikon Misira. Ɗansa Abduldaar shine wanda ya baro falasɗinu tare da tawaga zuwa Tarabulus ɗin ƙasar Libya.
Daga can kuma babu jimawa ya tashi zuwa tsohon garin Daura, a lokacin babu kowa a wajen, sai ya kafa gari.
Duk da cewar akwai ƙarancin sani matuƙa game da kafuwar daura ko kuma tsawon lokacin da tayi tana sharafi, amma wasu sunce ta kafu shekaru kimanin dubu huɗu da suka gabata, yayin da wasu ke ganin kafuwar garin ya samu ne a ƙarni na goma miladiyya.
Marubuci Zakariyya Adam Kabo ya kawo hujjojin cewa Daurawa misirawa ne da suka zo daga ƙasar su ta misira a littafinsa mai Suna 'Gamsasshen Tarihin Hausawa'. Ga kaɗan daga hujjojinsa akan haka:-
1. Da akwai wani takobi mai rubutu ajikinsa irin na mazauna kasar misira ada can wanda koda turawa suka zo sai da suka ce wannan takobin babu masu irinsa sai misirawa. Kuma ko yanzu kaje Daura ana iya ɗauko maka shi ka gani.
2. Yanayin tsarin gine-ginen fadar Daura ɗaya ne dana misirawan-da. Zakaga anyi soro, sannan katangun gida masu kaurin Gaske. Akan kuma yi manyan turaku da babban fili a matsayin tsakar gida da manyan zaurukan hutawar sarki.
3. Tamburan da ake zanawa a bangwayen gidan sarauta na Daura.
Haka shima Marubuci Maje Ahmad Gwangwazo ya tafi akan cewa tsoffin mazauna Daura Mangawa ne waɗanda basa jin Hausa, don haka koda Bagauda da ake cewa jikan Bayajidda ne, ya riski Kano sai daya shafe aƙalla shekaru biyu yana Koyon harshen Hausa na mazauna Kano.
Akwai kuma masu ganin cewa hijira biyu ko uku akayi daga can kan'ana zuwa Daura. Inda suka ce a hijira ta farko, Najib ne ya jagorance ta. Amma a hijira ta biyu, wata jaruma da ake kira Daurama ce ta jagorance ta. Kuma daga sunan tane aka laƙabawa birnin suna Daura, har kuma aka samu cewa an shafe tsawon lokaci mata ne ke jagorantarsa.
Ga sunayen Sarakunan farko da aka samu sun mulki Daura tun tsawon lokaci da ya gabata:-
1. Kufunu
2. Gufunu
3. Yakunu
4. Yakunya
5. Waizamu
6. Waiwaina
7. Gidir-gidir
8. Inna Gari
9. Daurama
A mulkin Daurama ne akace an tare a sabon birni mai kimanin tazarar mil goma a kudu maso gabashin tsohon birnin Daura tare da soma kiran birnin da sunan ta. Wani zane a masarautar Daura yayi hasashen aukuwar hakan a ƙarni na shidda, har kuma ake danganta zamanin ta da zuwan Abu Yazid (Bayajidda) wanda akace ɗan Abdullahi Sarkin Bagadaza ne, wanda ya baro gida da wata gagarumar tawaga bisa saɓani da mahaifinsa ko ƴanuwansa ko kuma bayan gwabza faɗa da Maguzawan Zidawa, inda ya soma sauka a Borno har Sarkin ƙasar ya aura masa ƴarsa Magira, daga baya ya ƙulla masa makircin rabashi da dakarunsa gami da yunƙurin halaka shi. Wannan yasa tilas ya gudo da matarsa mai ɗauke da juna biyu. Akan hanyarsa ya sauka a wani gari mai suna Biram ta gabas, ya ajiye matar tasa sannan yaci gaba da tafiya har ya riski tsaunin Dala na kano, inda akace ya riski wasu maguzawa maƙera masu suna Abagiyawa, waɗanda suka ƙera masa takobi, wadda da ita yayi amfani wajen kisan maciji mai suna 'Ƙi' ko 'Sarki' dake hana mutane ɗiban ruwa a rijiyar Kusugu bayan zuwansa Daura da dare a lokacin da yake buƙatar ruwan da zai shayar da dokinsa.
Akace Kashe gari sai Dauraman tasa aka nemo shi kuma har ta aureshi.
Sai dai wasu masu fashin baƙi sunce akwai tazarar aƙalla shekaru 150 tsakanin zamanin Dauraman da Abu yazid, wanda akace ɗansa Bawo ne ya gaje shi akan sarauta, don kuwa an samu ƙarin jerin sunaye sarakuna mata da suka mulki Daura bayan gushewar ta.
10. Ga-mata
11. Shatu
12. Fatatuma
13. Sai Da mata
14. Ja Mata
15. Ha-Mata
16. Sha-warata
An samu cewa kusan dukkan waɗannan sarakuna mataye ne, ana kiransu da suna 'Kabaras ' fassararsa shine Magajiya da hausa. Watau wadda tayi gadon mulki kenan.
Haka kuma, akwai maganganu na tarihi dake nuna cewar an samu ɓullar Shugabanni mataye masu laƙabin 'Kabara' a wasu masarautu na ƙasar Mali, da Isra'ila. Amma dai babu wanda ya tabbatar da wata alaƙa data kasance tsakaninsu da waɗannan Kabarori na Daura duk da cewar akwai hasashen yanayin bautar da akace Kabarorin sunyi yafi kamanceceniya da shigen wadda aka taɓa samu anyi a Isra'ila.
Zuwan Bayajidda akafi labartawa a matsayin tarihin asalin Hausa da Hausawa, amma a zahiri, labarai sun nuna cewar Bayajidda ya riski Daura ne a zamanin da ƙasar Hausa ke cike da mutane a sassan ta.