TARIHIN HAUSA DA HAUSAWA: MAHANGA TA 7
Sadiq Tukur Gwarzo
Littafin 'Hausawa da Maƙwabtan su' wanda turawan mulkin mallaka da haɗin guiwar wasu hausawa suka samar mai ƙunshe da tarin zantuka game da tarihin Hausawa da maƙwabtan su ya danganta asalin Hausawa ga Borno.
Aka ce Sarkin Borno na da wani bawa mai suna Bawo, babu wanda ya san asalin sa, ko dangin sa. Amma abinda aka sani shine Sarkin Borno ya jiɓanta shi a kan biranen Hausa guda bakwai da ake kira Hausa bakwai yana mai riƙe dasu yana tattara haraji tare da kula da lamurorin su, har ya haifi ƴaƴa bakwai.
A zamanin da ya ga alamun mutuwa sai ya sarautar da waɗannan garuruwa ga ƴaƴayen nasa. Kowannen su ya bashi birni guda.
Har aka ce wanda ya sa a Daura ba namiji bane, mace ce mai suna Daura. Saboda haka ake ambaton garin da sunanta.
Haka kuwa itace babba a cikin ƴaƴansa, itace ƴaruwar sarkin katsina da sarkin Kano da sarkin Gobir, domin dukkan su uwarsu ɗaya.
Kuma sarkin Burmi da Sarkin Zazzau uwarsu ɗaya. Sarkin Rano kuwa shi kaɗai ne wurin uwarsa.
Saboda haka sai ya zamana ƴaƴayen sun cigaba da bayar da harajin ƙasashen su zuwa Daura, daga nan kuma ana aikawa Borno zuwa ga Sarkin ta.
Sarkin Gobir Bawa kaɗai ne ya ƙi bada harajin nan, sai kuwa yaƙoƙi suka rinƙa aukuwa tsakanin garuruwan da Borno, daga bisani ya ƴamtar da ƙasashen Hausa daga Borno.
Wannan abu tabbatacce ne a cikin labarun da aka faɗe su, haƙiƙa asalin su ƴaƴa ne, su ne ragowar Kibɗawa. Su kuma Kibɗawa sune jama'ar Fir'auna da suka tafo daga Misira suka cika garuruwan Ahira har suka tafi Gobir suka fitad da waɗanda suke cikinta, sune waɗanda suka mallake ta daga ƴaƴan Bawo suka karɓe sarauta daga hannun mutanen wajen. Suka rinƙa yin aiki daga abinda suka iske ƴaƴan Bawo suna yi, suna masu biyan haraji har zuwa lokacin da Bawo ya hana biya.