Monday, 12 August 2019

TARIHIN NUFE: KAFUWAR ƘASAR NUFE Kashi na huɗu

TARIHIN NUFE: KAFUWAR ƘASAR NUFE
Kashi na huɗu
SADIQ TUKUR GWARZO
    Marubuci Buhari Daure ya ruwaito a littafinsa 'Tarihi da Al'adun Mutanen Najeriya' cewa kafuwar ƙasar Nufe ya wanzu a wajajen ƙarni na goma sha shidda ne. Inda yace asalin Nufe dana Igala ɗaya ne, sai wani ɗan sarkin masarautar Idah mai suna Tsoede yayi gudun hijira tare da kafa masarautar Nupe wadda ta haɗe ƙauyukan Beni, Bidda, Benu, Debo, Tafiya, Doka, Gaba, Dibo da Kupa.
Amma binciken Dr. Sidi Tiwugu Shehi ya kawo ra'ayoyin masana da yawa  saɓani da wannan.
Daga ciki akwai masu cewa asalin Nufawa zuriyar wani balarabe ne mai suna Uqba bn Nafiu wanda ya baro ƙasar su ta larabci tare da zama a ƙasar Nupe.
Wasu kuma suka ce Nufawa sun fito ne daga wani Mafarauci balaraben Misira mai suna Abdulaziz wanda ya gudo daga ƙasar sa ya sauka a Doko Dazi cikin ƙasar Nufe dashi da ahalinsa. Daga nan aka sanya musu suna 'Nefiu' da yaren ƙabilar Beni daya tarar, wanda ke nufin 'wanda ya gudo daga wani wuri' .
Sannu a hankali sai sunan ya sauya zuwa Nufe ko Nupe.
Wasu kuma sunce Asalin Nufawa daga ƙasashen Katsina, Kano da wasu makusanta suke. Har ma Clapperton yace sunan Sarkin su Tsoede, kuma sun zo ƙasar Nupe ne daga wani birni da ake kira Attah Gara.
   Shikuwa Ndagi Abdullahi ya tafi akan cewa Nufawa suna kakannin Hausawa, Yarabawa da Inyamirai. Inda yace zuriyar Nufawan ce ta fantsama tare da samar da waɗannan yaruka (ko ace ƙabilu)
Amma dai masani S.F Nadel ya raba Nufawa gida huɗu daga abinda ya kawo a littafinsa mai suna 'Social Symbiosis and Tribal Organisation'. Ga rukunan kamar haka:-
Rukuni na ɗaya sune Ndachezhi, watau Mafarauta kuma asalin mazauna ƙasar Nupe waɗanda akace suna zazzaune a ƙauyuka sama da shekaru dubu da suka gabata.
Rukuni na biyu sune Esozhi, suma asalin Nufawa ne waɗanda suka jima a ƙasar Nufe har ma suka  kafa birnin Kutigi.
Rukuni na uku sune Benu, waɗanda suka yo hijira daga ƙasar Bornu. Su kuwa da yawansu malaman addinin Islama ne da masu fatauci, daga baya ne suka samu ikon wasu yankunan Kutigi.
Sai Rukuni na huɗu waɗanda ake kira Konu, waɗanda asalinsu bayi ne da aka kamo wurin yaƙi daga ƙasashen Yarabawa, daga baya aka ƴantar dasu tare da basu mazaunai a ƙasar Nupe.
Sannan binciken masana kimiyya da aka gudanar a yankunan Jebba, Giragu, Tada, Oyo-ile, Esie-oba da wasun su ya nuna cewar ƙasar Nupe tana ɗauke da mutane tun sama da shekaru 3000 zuwa dubu 10,000 kafin haihuwar Annabi Isah A.S.
Wannan yasa ake hasashen cewar asalin ƙabilun da suka rayu a wannan yanki wanda ya mamaye yankin Abuja da wasu yankunan tsakiyar Nigeria, sune suka haifar da ƙabilun Yarabawa, Inyamirai, Nupawa, Igala, Idoma, Ebira da Gbayi.