HIKAYAR SAIFUL MULUKI DA ALJANNA BADI'ATUL JAMALI
NA BIYU
Bayana wata huɗu, mutane huɗu suka dawo, ba su samo kome ba, suka ba shi labarin binchiken su da isa matuƙa ga kokarin su. Allah bai rabbatar da wannan nufi da suka tasamma ba, sai ran attajiri ya dugunzuma matuƙa ainun.
Na biyar ɗin su shine wanda ya nufi ƙasar Sham, watau shine na huɗu a lissafi, bai zame ba sai Dimashƙu.
Ya same ta babbar alƙarya ce mani'imchiya, ya zamna nan yana tambaya, babu wanda ya ce masa ci kanka.
Yayi haramar fita ya sake tafiya zuwa ga wani garin sai ya hangi wani yaro yana famfala gudu, yana tuntuɓe da ƙafarsa.
Yace masa "kai samari, me ya faru kake gaggawa haka? ina zaka?."
Sai yaro yace "zani majalisar wa'azin wani tsohon Malami ne wanda yake zama rana mai kamar ta yau, yana bada labaru da daɗaɗan hikayoyi waɗanda daɗai mutum bai taɓa jinsu ba; don haka nike gaggawar in samu zuwa wurin da wuri don kada na rasa wurin zama, ina tsoron matsatsi."
Yace masa "in biyo ka?" Yaro yace ''in kana iya gudu zo mu je".
Sai kuwa ya ja ƙyauren ɗakinsa ya kulle, ya bi saurayin nan a guje. Da suka isa sai suka tarar da dattijo zaune bisa kujerar sa, bai soma ko Basmallah ba. Suka zauna kusa dashi, suka kasa kunnuwan su gare shi.
Zuwa jimawa, sai Malamin ya shiga bada labarai, bai tashi ba sai da rana ta kusa faɗuwa.
Da gamawar sa, jama'a suka watse, sai magudancin nan ya kusance shi, yayi masa sallama; ya amsa masa suka gaisa da juna sannan yace "Allah ya bamu albarkacin Mallam, idan ka yarda ina so nayi tambaya". Mallam yace "Allah ya sanasshe mu, tambayi abinda kake so ya ɗana".
Sai yace "Ko Allah ya sa kana da labarin Saiful Muluki da Badiatul Jamali?"
Tsoho yace "kai kuwa a ina ka samu wannan zanche? wa ya gaya maka wannan labari?"
Yace "ji nayi, neman sa kuwa na fito, kuma shi ya taso dani daga nisan duniya zuwa nan. Idan kana dashi ina bara ka sanad dani don Allah da Annabin sa domin alherin ka. Abinda ka nema kuwa duk zan baka, da dai raina a hannu yake, in kache shi ka ke so wallahi da na baka."
Ɗan Tsoho yace " Yi farin ciki, buƙatar ka ta biya: amma bani faɗawa kowa bisa tafarki, ban kuwa taɓa faɗawa kowa shi ba daɗai. Idan kana son sa kazo gidana tare da dinari ɗari, zan gaya maka shi bisa sharaɗi biyar".
Yace "Zan baka dinare ɗarin da ka ambata, zan kuma baka goma kafin alƙalami, zan amshi wannan hikaya da dukkan sharaɗin da zaka ambata akanta."
Tsoho yace "tafi gobe da safe kazo da su ka riƙi buƙatar ka".
Ya tashi ya sunkuya yayi godiya gun tsoho ya tafi makwancin sa yana cike da murna, ya zuba dinari ɗari da goma a cikin rarita, da fitowar alfijir ya tashi yayi wanka ya sa tufafin sa ya ɗauki mayani ya tafi gidan malami yayi sallama, da fitowar sa sai ya gaishe shi sannan ya miƙa masa jaka.
Tsoho ya amsa yayi godiya ya shiga tare dashi zuwa shamakin sa, ya shiga ya fito masa da da tawada da alkalami da takardun rubutu, ya mika masa wani littafi yace "shine wannan littafi mai ɗauke da wannan hikayar".
Ya amsa ya duba ya rubuce shi, ya karance shi ga malamin, sannan tsoho yace masa
"Ya ɗana, farkon sharaɗin da zan gaya maka shine kada ka bayar da wannan labari akan tafarki, na biyu kada ka gayawa mata shi, na uku kada ka gayawa wawayen mutane shi, na huɗu kada ka gayawa yara, na biyar karatun sa sai a gun sarakuna." Bawan Attajiri Hassan Yace "to naji na karɓa", ya durkusa yayi godiya sannan ya tafi.
A wannan lokacin saura kwanaki goma wa'adin sarki ga ubangijin sa Hassan ya cika, don haka yayi saurin aikewa da mai bushara zuwa gareshi, sannan cikin hanzari ya haɗa kayan sa ya nufi komawa gida.
Sannu a hankali ya isa gida, koda attajiri yayi arba dashi sai ya rungume shi don murna, ya cire tufafin jikinsa na alfarma ya danƙa masa su, ya bashi ingarmun dawakai goma, taguwowi goma, alfadarai goma, bayi goma, waɗannan fa duk a matsayin barka da sauka ne ba a cikin ladan aikin sa ba.
Bayan haka, Hassan attajiri ya sake rubuta wannan hikaya da hannun sa, sannan ya tafi ya yiwa Sarki albishir da ita a ranar da wa'adin su ya cika.
Sarki ya cika da farin ciki, sannan ya aike a tara masa dukkan sarakunan sa, da malamai da mahankalta da masu duban tamrari duk na ƙasar sa, da suka gama taruwa sai Hassan attajiri ya labarta wannan hikaya a garesu.
Ɗaukacin jama'ar suka cika da mamaki, babu wanda ya taɓa jin wannan hikaya mai daɗin gaske daɗai, babu zato sai dinare da azurfa da jauharori ke ta zuba akan Hassan Attajiri, ana yi masa kyauta dasu..
Sarki ya shiga gida ya tuɓe tufafin jikin sa ya kawo masa su kyauta, ya mallaka masa yankin ƙasa guda, ya sanya shi wazirin dama. Yayi umarni a rubuta masa wannan labarin da ruwan dinari a taskance masa shi a taskar sa, a duk lokacin da ransa ya ɓaci sai Waziri Hassan ya karanta masa shi, kafin ya ƙare sai kaga farin ciki da annushuwa ya dabaibaye shi.
Ga yadda wannan hikaya take:-
A zamanin da anyi wani sarki a Masar, sunan sa Asimu ɗan Safwana...