GARIN YALWAN ƊAN ZIYAL
Sadiq Tukur Gwarzo
Daga tsoffin matsugunan da suka yi shura a ƙasar Hausa musamman cikin ƙasar Kano, ananiya cewa garin 'Yalwan Ɗanziyal' na daga gaba-gaba.
Akwai ababen tunawa da dama game da wannan gari.
Marigayi Maje Ahmad Gwangwazo ya ruwaito a littafinsa 'Tarihin kano kafin Jihadi,: wangarawa sunzo kano' cewa sai da Wangarawa (waɗanda suka taso daga Mali tare da isar da addinin musulunci a kano a zamanin sarkin kano Yaji) suka sauka a garin Yalwan Ɗanziyal na lan wani lokaci kafin daga bisani su ƙarasa garin kano.
Kafuwar Garin Yalwan Ɗanziyal
Kafuwar wannan gari mai tsohon tarihi ya samo ne tun lokacin da masu sarautar kano (na gidan Bagauda) suka karya gunkin Tsumburbura, abin bautar da Barbushe da sauran magoya bayansa da suka gabace shi suka kasance suna yiwa bauta a saman dutsen Dala.
Littafin Tarihin kano (Kano chronicle) ya kawo mana labarin yadda abin ya faru da cewa:-.
" Sarki na Tara, Tsamiya ɗan Shekarau (1307-1343)
Sa'ar da yaci sarauta ya tara kafirai yace dasu "soyayya ana gadonta, ƙiyayya ana gadonta, babu wani abu tsakani na daku sai baka da mashi da takobi, da garkuwa ba yaudara, domin babu mayaudari sai matsoraci"
Domin ya haɗa abubuwa biyar:- sadaukantaka, kwarjini, zabura akan abokan gaba, tsananin fushi da ƙarfi.
A daren alhamis suka taru a gaban gunkinsu birni da ƙauye, jama'a masu yawa , masu ƙuru- da gunduwa da tsintsima dubu arbamiyya, sarakunan baka arbamiyya da tsiraru, basu gushe ba suna kewaye gunkin tun daga magariba har hudowar alfijir.
Yayin da alfijir ta hudo sarki ya fito daga ɗakin sa ya nufi wurin gunkin.
A gabansa akwai mutum saba'in, kowanne cikin su yana riƙe da garkuwar fatar giwa. Yayin da yakai wurin sai kafirai suka hanashi shiga ɗakin da gunkin yake. Aka ɗaura yaƙi.
Wani mai suna Bajere aka ruwaito ya riƙe mashi bisa umarnin sarki yana kashe abokan gaba har sai da ya sadu da ginin ya shiga cikinsa, ya samu wani mutum ya jingina da bayansa da itaciyar gunkin, akwai jar maciya a hannunsa, (Bajere) ya soke shi.
Mutumin ya zabura yayi kururuwa , hayaƙi ya fita daga bakinsa ya gama gari duka. Ya fito yana gudu zuwa kofar Ruwa, sarki ya bishi ya kutsa a cikin ruwa. Sarki ya zauna tare da rundunar sa suna ta neman sa cikin ruwa. Daga nan ya fita zuwa Dankwai, suka barshi, dalili kenan da kowanne taron yaƙin da yasha ruwan Ɗankwai ba ya samun nasara cikin yaƙin sa.
Sa'an nan sarki ya komo ƙarƙashin itaciyar ya rushe ginin, ya tattara dukan abin dake karkashin itaciyar na Cibiri. Dukkan kafirai suka gudu, sai Makare ɗan Samagi da Dunguzu ɗan Dorini kaɗai.."
Don haka, ire-iren waɗannan mutane ne suka kafa wannan tsohon gari mai suna 'Yalwan Ɗanziyal'.
Matsugunin Garin Yalwan Ɗanziyal
Asalin garin ya kafu ne a gabas da inda na yanzu yake cikin karamar hukumar Rimin gado ta jihar kano, wanda ana iya cewa can ne ainihin garin Yalwa, daga bisani akace annobar wata aljanna mai suna 'Kun taru' wadda ke halaka mutane ta sanya suka koma sabon gari na farko, wanda yanzu yake yamma da inda garin yanzu yake.
Acan kuma cin ruwa ya sanya mutanen sake yin hijira zuwa inda suke a yanzu. Sai dai babu takamaimen shekarun da waɗannan hijirori suka wakana. Amma dai akwai alamomin zama da ake iya gani har yanzu.
Bisa ainihi, Yalwa ne sunan garin, sabili da albarkar da Allah ya ba shi na noma da kasuwanci ga duk wanda ya ziyarce shi.
Wani mai suna Ɗanziyal ya zamo shahararren jagoran garin ne tsawon zamani bayan kafuwar sa, har kuma ya zama ana danganta sunan garin da sunan sa.
A mafi shaharar zance, Ɗanziyal mutum ne masanin ɗibbu, watau mai bayar da maganin waraka daga cututtuka wanda ya riski garin Yalwa da zama a zamanin da wata ɗiyar Sarkin kano ke fama da lalurar rashin lafiya, anyi magani amma abun ya faskara.
Cikin sa'a sai aka kawo ta wajen Ɗanziyal dake zaune a garin YALWA, wanda ya yi mata magani har kuma ta samu sauƙi. Sarkin kano na zamanin (ba a faɗi sunan sa ba) ya nemi Ɗanziyal ya faɗi ladan sa na wannan aiki, amma sai Ɗanziyal yace duk abinda aka bashi ya wadatar.
Wannan ne ya sanya sarki ya baiwa Ɗanziyal sarautar garuwa uku manya na wannan yankin. Na ɗaya shine garin Yalwa da shi Ɗanziyal yake zaune, sai Madobi da kuma wani gari mai suna Cunkoso.
Akwai zance mai nuni da yawaitar ƴaƴan sarkin kano a wannan garin na Yalwan Ɗanziyal musamman a zamanin mulkin fulani a kano, watakila garin yana daga cikin garuruwan da ake tura ƴaƴan sarki koyon ilimi da jarumta. Don haka ake yiwa garin kirari da 'Yalwa ta Ɗanziyal, garin ka taka mallam' (akan ambaci ɗan sarki da Mallam). Wannan ya sa baƙi ke taka-tsan-tsan a garin don gudun kada su yi wani abu ga wani daga ƴaƴan sarki cikin rashin sani.
Sannan kuma ana ganin zuriyar marigayi Sarkin Kano Muhammadu Tukur can suka koma da zama bayan kammala yakin Basasar kano...