Sunday, 30 May 2021

LABARIN MAI ASIGIRI ƊAN SAMAME

 LABARIN MAI ASIGIRI ƊAN SAMAME

  Cikin zamanin sarkin Katsina Muhamman Bello, anyi wani mutum wanda ya dami Katsinawa da fitina, yana kama musu ɗiya yana kai su ƙasar Arewa yana sayarwa. Sa'an nan sai sarkin  Katsina ya tara manyan malamai duka na katsina, ya basu dukiya mai yawa, yace su taimake shi don a kama wannan mutumi; idan an kama shi, sai a kaishi kasuwa a sare masa  kai.

  Nan take malamai suka duƙufa ƙoƙari, aikuwa dai ba'a yi kwana goma ba, sai Mai-asigiri ya zo ya kama wata budurwa a ƙofar sami da daddare. Tayi hargowa, daga nan masu tsaron garke suka ji ana ihu, kowa ya ɗauko kwari da baka da kunkeli, suka zo gudummawa.

 Ko da ya ji su sai ya yi ta kirari, yana cewa "A gayawa yaro ga Mai-asigiri!" Ko da fulani suka ji Mai-asigiri ne, sai suka ce ashe yau daga zamuyi a wurin nan. Sai suka yi ta hargowa,   suka fito daga gidajensu, suka zo bakin ƙofa amma tana rufe, shi kuwa sai kirari yake yi daga waje. 

Mutane suka koma gida, Gulbi Bikwaine ya fito fadanci daga gidan Durɓi, sai  yayi kichiɓus da wannan hargowa, Mai-asigiri yana ta kirari. 

   Daga nan sai Gulbi ya ɗauko alkilla yai ɗamara da ita, ya ɗauko garkuwa da takobi ya fito ya zo bisa ganuwa, ya aza garkuwarsa, ya hau daga nan, sai ya darza waje. Ya nufi inda Mai-asigiri yake, koda isar sa sai shima yayi kirari yace "A gayawa yaro ga Gulbi"

  Sai mai asigiri yace yau ƙarya ta ƙare tunda ga baraden katsina sun fito su da kansu, sai ya zabura da gudu don ya tsira sai kuwa Gulbi ya bi shi ya banke, ya kamashi ya ɗaure shi da asalwayi, ya shiga gari dashi sannan ya baiwa waɗannan mutane dake wajen yace musu "kada ku sanarwa da kowa nine na kama shi, kuyi shiru, kuce kune kuka kamashi". Sai suka tafi dashi wurin Durɓi.

  Durɓi ya tafi dashi ga sarki acikin dare tsaka anan Nasarawa. Sarki ya tambayi Durɓi wanda ya kama shi, sai Durɓi yace Ƴan garke ne. Sarki yace da safe a kawo su yana son ganin su. Durɓi ya tafi gida, sa'annan Mai asigiri yace "ni babu wanda ya kamo ni sai Gulbi Bikwaine".

   Da gari ya waye, Sarki ya kawo kenkendi goma da dawaki goma da zambar dubu ya baiwa Gulbi kyauta, ya yanki ƙasa cikin kaita ya bashi. Sa'annan sarki ya tara manyan sarakunan katsina ya ce "Yau ga azzalumin nan an kawo shi, ina dabara?"

  Suka che "A sare kansa a kasuwa", Sarki yace "to sai gobe in Allah ya yarda".

  Da dare ya yi, sarki yasa ƴan batakulki suka zo da  Mai-asigiri, sarki yace "Kai, Kaɗo, na yi shawara da sarakuna, sun ce a kashe ka. To ni ba zan kashe ka ba, zan sallame ka, amma kada ka ƙara kama kowa a ƙasar Katsina, kuma duk labarin da ka ji na arewa ka faɗa mani nan da nan in sani." 

Sarki ya kawo kyauta mai-yawa ya ba shi ya che yaransa su raka shi har ƙofar Guga, a buɗe masa ya fita.

Amma ya che, "Kar ku gaya wa mutane." Da gari ya waye, fagachi ya chika, Sarki ya che, "Mai-asigiri ya gudu, an bi shi, ya tsere."

Kwanchi tashi kwanchi tashi ran nan Sarki ya tafi Modoji shan iska tare da iyalinsa, Danbaskore ya ji labari, ya nemi sa'a ya che za shi yaki wajên Sokoto. Mallamai suka ba shi sa'a don ya zo ya mamayi Sarkin Katsina ya yanka shi.

Mai-asigiri ya ji labari, sai da ya bari yaƙi yayi yamma, ya dakako ya nufo Katsina, dare kuwa ya yi-masa a kan hanya.

Da ya zo ƙofar Guga ya che a buɗe kofa. Mai-tsaron kofa ya ƙi, sai ya che shi manzon Sokoto ne, ya nufi ƙofar Samri, ya tambayi sarkin ƙofa, ya che, "Durɓi na nan ?" Ya che, "I." Ya che, "A faɗa masa ga manzo daga Sokoto." Durbi ya taso ya zo gare shi ya che, "Wanene kai, mutumin Sokoto ?" Mai-asigiri ya che, "Ni manzo ne." Durɓi yace "Ina takardarka a kai ma sarki, kana ka shigo?". Sai ya che, "Durɓi, matso nan in yi maka raɗa". Ya che, "NI ne Mai-asigiri, labari na samo mai-girma, ka faɗa ma sarki jibi warhaka karkarar adda'irar Katsina ta chika da yaƙi; ga su nan tafe jibi: sarakuna biyu, Gobir da Tasawa."

 Durɓi ya che, "Ashe ba magana ku buɗe kofa." Aka je aka amso mabuɗi wurin Ajiya aka buɗe, ya shigo, aka ba shi abinchi da goro. Durɓi ya che, "Sarki yana Modoji, bari in gama ka da mutun, shi kai ka." Suka tafi Modoji, suka buga Kofa, sarkin ƙofa ya che, "Wanene ?" Mai-asigiri  ya che, "Manzo daga Sokoto, ku fada ma sarki." Suka che, "A'a, sai ka bada takardarka, a kai wa sarki yanzu, kana ka shigo." Sai Ya che, "Kai, ku gayawa sarki maza maza akwai saƙo gareshi." Aka je aka fada ma sarki, ya fito chikin tsakad dare ya che a kira yaransa, kowa ya ɗauko takobi da mashi da ɗamara da sulke da garkuwa, kana a buɗe kofa manzo ya shigo. 

Sarki kuwa yai ɗamara, da shi da mutanensa a ƙofar birnin Modoji.

Sa'an nan sarki ya che ya shigo. Mai-asigiri ya shiga, ya che ma sarki, "Ni ne." Sarki ya che, "To, ina labarin Haɓe ? Ya che ma sarki, "Gobe warhaka nan tojiyar ta sha wuta, don haka na zaburo in shaida maka." Sarki ya che, "Na gode maka kwarai. Ta ina za su hudo ? Ya che, "Wajen yamma za su hudo." Sa'an nan sarki ya sallame shi.

 Da asuba ta yi sai sarki ya hau, da shi da mutanensa, ya tafo gida ya shiga, sa'an nan ya fito.

Ya che, "Ina manyan sarakunan Katsina ? Su zo, su shiga shirayi. Suka zo, sukai gaisuwa. Ya che masu, "Gobe warhaka muna da baƙi, sarkin Gobir da Ɗanbaskore suna tafe, sai mu yi ƙoƙari mu yi dabara." Durɓi ya che, ya sarki, abin da ya fi sai ka sa a tafi bakin sagagin nan a ƙulle gezozin nan duka, domin da Sun zo Sai su kasa wuchewa: kafin su kwanche gezojin mun chi su da yawa, mun yi masu ɓarna ƙwarrai.

Sarki ya che, "Dai-dai ne." Kuma Ƙaura ya che, "Dai-dai ne".

Aka je aka ɗaure geza sarai, sa'an nan Durɓi ya hau ya tafi bakin mashaya,  ya jera ƴan baka, kuma da azahar sai Sarki ya sa akai shela a kasuwa, aka gaya wa mutane su shirya sosai ga tawaye nan tafe. Kafin Danbaskore ya zo Katsinawa sun shirya, shikuwa sai murna ya ke yi ya wo dukake.

Gari na wayewa rana ta hudo kaɗan, sai aka jiwo hargowa arewa da gari. Durɓi ya che a faɗa wa Sarki tawaye Sunzo. Aka buga tambari da kuge, shi Danbaskore ba shi da labari an ƙulle gezoji sarai. Da ya zo kamin a kwanche geza, Sarkin Katsina ya zo, shi da mutanen sa. Akai ta daukekeniya

da mutane har wajen rana tsaka, sa'an nan aka fasa tawaga, dokin yaƙi ya fasu, akai ta kama mutane da dawakai, aka kama doki kamar hamsa, mutane kuma kamar talata.

Durɓi da ya ga Danbaskore, cha ya ke wani ƙaramin zarumi ne, ya bi shi ya che sai ya kashe shi; ya tarar dashi ya soke shi da mashi; shi kuwa ya sa garkuwa ya amshe, ya che ma Durɓi, "Kai, yaro kula da giwa!." Durɓi ya che, "Ai, giwa ta san mashi." Shi kuwa bai san Sarki ba ne. 

Sai da suka kai ga tasa mahara, dokin Ɗanbaskore ya tsallake tasa-mahara, dokin Durɓi kuwa ya kasa tsallakewa, sai ya tsaya. Danbaskore ya che, "Ni ke saye

da kaina, kai kuwa sai an ba ka." Durɓi ya che, "I, wanda a ke siyarwa ya kore ka da ƙyar ka tsere."

  Ɗanbaskore  Ya koma gida shi ɗaya, sai makaɗinsa don ba a kama makaɗi wurin yaki. Da ya isa gida ya che, "Sai na rama, sai mun gamu da Katsinawa. Ni bakin

bunsuru ne mai-wari, kowa ya chi ni, ya yi amai." 

 Yayi shekara guda bai nufo Katsina ba, sai dai sammu a ke kawowa, in an bisne sai Mai-asigiri ya zo ya faɗa wa Sarki, a je a tone. Duk inda ya nufa Mai-asigiri sai ya zo Katsina ya fadi. 

  Wata rana kuma Danbaskore ya kira wadansu mazaje, sukai lada tukuna, ya che, "In kun kawo Sarkin Katsina, na ba ku abin da zai ishe ku." Ya kawo zannuwa da kalluba ya ba su, ya sa akai masu kitso Kamar mata. Aka dubi wani mutumin Kano, aka gama kai da shi, aka che ya kawo ma Sarkin Katsina ya saya. Aka tsafe wukake, aka ba su, waɗanda in sun soki mutum nan take zasu kashe shi, aka kawo wani sammu kuma wanda za su sa a gidan Sarki.

   Ba-Kanon nan ya tafo da su. Sai wani mutum ya gayawa Mai-asigiri, ya che, "Ba ka bin mutumin nan gashi can zasu katsina tallan bayi na sammu?" Sai yace masa "I",

Sai ya yanko dare ya riga su, ya che ma Sarki, " Ana kawo tallan bayi daga arewa, to, maza ne akai masu siffar mata". Sarki yace "Har su zo, muna saurare". Ko da isowarsu sai aka kama su aka kai su gangi (shine wani rami kusa da ƙofar Guga) aka kashe su. Shi kuwa Ba-kano, akayi biyan bashi dashi.

To haka Mai-asigiri yai wa sarkin Katsina Muhammadu Bello alƙawali, har ya mutu bai warware ba.

  Sadiq Tukur Gwarzo