Abubuwa tara muhimmai game da FASAHAR ChatGPT
Sadiq Tukur Gwarzo
(A.A Gwarzo Learning Institute @AAGHOLI)
-Kamfanin Amurka mai suna OpenAI mai bincike akan fasahar AI (Artificial Intelligence) ne ya samar da wannan fasaha a watan Nuwambar 2022, attajiri na ɗaya a duniya Elon Musk na daga waɗanda suka assassa kamfanin OpenAI a 2015
-An gina Fasahar AI (Artificial Intelligence) bisa sigar koyar da Na'ura mai ƙwaƙwalkwa wajen tattaro bayanai daga mabanbantan wurare tare da yanke hukunci gwargwadon abinda ta iya riska tamkar dai yadda ɗan Adam yake iya yi. Misalin fasahar AI shine shafin writesonic.com inda mutum zai iya umartar Na'ura ta samar masa da gamsasshen bayani daga ƙaramar saɗara.
-Fasahar ChatGPT (Chat Generative Pre-trained Transformer) na nufin wani ɗan mutum-mutumin (mai amfani da fasahar AI) na'ura mai ƙwaƙwalwa wanda mutum zai iya tuntuɓa domin zartar masa da wani aiki babba ko ƙarami a sigar mutum tamkar yadda ake sadarwa tsakanin mutum da mutum.
-Wannan fasaha ta ChatGPT ta kafa tarihi wajen samun karɓuwa sama da kusan ɗaukacin fasohohin da ake samarwa a duniya; a tsawon kwanaki biyar kacal da fara ta sai da mutane miliyan ɗaya sukayi rajista da ita, zuwa yanzu kuwa fasahar ta samu karɓuwa a wajen kimanin mutane miliyan 500.
-Mutum-mutumin ChatGpT na da basira matuƙa kamar ɗan adam, don haka akan iya umartarsa yayi rubutu akan wani lamari na ilimi, kuma zai iya yin hamshaƙin rubutu tamkar yadda ƙwararre a fannin zai iya yi, misalin; fayyace ma'anar wani abu, ko rubuta waƙa, ko yin zane, ko warware wata daga matsalar lissafi, ko kuma uwa uba rubuta kundin masarrafa mai ƙwaƙwalwa.
-Attajiri Bill Gates, mutumin da ya kafa kamfanin Microsoft, yayi gargaɗin cewa anan gaba fasahar ChatGpt na iya kawwame ɗumbin mutane daga samun ayyukan yi bisa ganin yadda fasahar take iya yin ayyukan da ƙwararru ke gabatarwa cikin ƙanƙanen lokaci.
-Tagomashi: Ana iya umartar fasahar da bayar da bayanai muhimmai game da abubuwan da ake da buƙata, misali;
"Explain quantum computing in simple terms" →
"Got any creative ideas for a 10 year old’s birthday?" →
"How do I make an HTTP request in Javascript?"
-Ƙalubale: Har yanzu fasahar jaririya ce, tana iya bayar da raunanan bayanai gaɓe da abinda aka tambayeta, ko ta bayar da bayanai masu hatsari ga lafiya a matsayin amsar wata tambayar da aka yi mata, sannan an haƙƙaƙe cewar tana da ƙarancin sani game da muhimman abubuwan da suka faru ƙasa da shekarar 2021.
- Akwai masarrafai da dama da mutum ke iya saukewa don amfanuwa da wannan fasaha, sai dai da yawansu na kuɗi ne. Hatta a zauren whatsapp ana iya shigar dashi ta yadda zai zamo tamkar abokinka da zaka rinƙa tambaya abubuwa ko ka sanya shi yayi maka rubutun zube, ko rubutun waƙa, ko zane, da makamantansu, amma dai babban shafin ChatGPT shine https://chat.openai.com