Friday, 7 July 2023

JIDAL

 JIDAL


Ance SARKI  RANAU ne ya soma zama a wurin. Wasu na cewa yazo daga Gaya ne ko yankin Rurum.

Daga ɗansa BAJADALI aka samo sunan JIDAL.

JIDAL tsohon birni ne da mutane suka rayu a cikinsa, akwai fadoji da sarakuna suka zauna, sannan garin zagaye yake da manyan duwatsu.

An rinƙa samun saɓani da rashin jituwa tsakanin Sarakin Jidal Bajadali da waɗansu fadawansa waɗanda suka yi rayuwa da iyayensa.


Ance BAJADALi yayi sarauta da ƙasaita bayan gushewar Ranau, ya zauna a fadar cikin kogo. Watakila shine akewa laƙabi da 'Zamna Kogo'.


Wani basarake ya zama abokin hamayyarsa, wanda bisa tallafin fadawansa aka hilace shi aka halaka shi.


Wani zamanin kuma, anyi wata sarauniya a JIDAL mai suna MAIRAMU, itama a saman dutse ta rayu.

Da akwai gagarumin tsaro da sarƙaƙiya kafin zuwa fadar zamna kogo da ma duk fadojin da sarakunan JIDAL suke rayuwa.

Har yanzu kufen JIDAL yana nan a ƙasar RANO, kuma da akwai abubuwan ban mamaki na tarihi da akan iya gani acan.

Wednesday, 5 July 2023

TARIHIN KAFUWAR KATSINA

 ASALIN KAFUWAR KATSINA DAGA LITTAFIN TARIHIN KATSINA


Sadiq Tukur Gwarzo


KAFUWAR Birnin Katsina

Ga abinda yazo daga littafin tarihin Katsina

(Kitabu Taarikh Ummaratu Hazihil Qaryatu Al-mashhuratu bi- Katsina min binaaiha ila yaumina haza” 


Da sunan Allah Mai Rahama Mai  jinkai, godiya ta tabbata ga Sarkin Sarakuna. Mun fada, Amma Allah ne mafi sami. Tabbas, Wannan ne tarihin Wannan  shahararren birni Mai  suna Katsina tun daga kafuwarsa kawo yanzu. Wasu masanan tarihin sun ruwaito cewa tsohon birnin ya gabaci Adaamus (ance wani shahararren Sarki ne da aka taba yi a Kasar Hausa) da shekaru 4. Sannan masanan sun tafi akan cewa  BAGANI JARGO wanda ya Gina ganuwar birnin ya sarauci Katsina tare da zuriyarsa har tsawon shekaru dubu uku da hamsin kafin zuwan  SANAWU (Wanda a zamaninsa Musulunci ya shigo Katsina) wanda ya dauki gabarar sarautar birnin. 

 To Amma, Sanawu, da Bagawu da Katsina, sun kasance shahararrun 'ya'yan Bawo ne, Kuma sun wanzu a mulkin Katsina na tsawon lokaci. Sun yi mulki na tsawon shekaru dari Tara.

Daga nan sai MUHAMMADU JANHAZO, dashi da zuriyarsa sun shimfida mulki na tsawon shekaru dari biyu da ashirin.  

  Har ila ya, an ruwaito cewa TSAGA RANA ya shafe shekaru hamsin da bakwai (  Masani Dr Yusufu Bala Usman ya ambace shi a matsayin Sarki na bakwai, ya yi sarauta a wuraren 1767-68)

Sa'annan ya baiwa babban dansa mulki, sunan sa WARI MAI-KYERAAYI, wanda ya shafe shekaru goma Sha uku Yana sarauta (ya mulki Katsina daga 1649-1660. 

(A zamanin mulkinsa ne ya yaki Kano, Abdullahi Yana sarautarta. Ance sai da ya taba rarakar Kanawa har sai daya tuke dasu zuwa kofar Kansakali ta birnin Kano sannan ya juyo).

 Sannan ya Mika mulki ga GIMA da ga Daqaasariy, shima ya shafe shekaru talatin da biyar yana sarauta, daga Nan sai AGWARAGI ya karba Wanda yayi mulki tsawon shekaru arba'in da biyu. (Ance shine Sarkin Katsina na takwas, ya yi mulkiba wajajen 1778-96. Tarihi ya KIYAYE cewa Agwaragi shahararren Sarki ne, a zamanin sa.ne Katsina ta kwaci Wata takobindaga hannun Sarkin Gobir a zamanin da ake Karin battar yaki tsakanin Katsina da Gobir din, sunan takobin Bee-bee. Har yanzu, nasarar Katsinawa akan Gobirawa na daya daga ababen alfaharin Katsinawa;  a duba KATSINA: a historical document wanda Centre  Regional de Documentation Pour la Tradition Orale Niamey ta wallafa a 1970.)

 Daga shi sai GWOZO, maruwaitan tarihi sunce ya shafe shekaru talatin da bakwai Yana sarauta. Sauran shekaru Sha ukun da suka rage, sarakuna irinsu     MUHAMMADU AL-ZAAHID wanda bai Jima kan sarautar ba, har manya nesanta kansa daga  abubuwan duniya har ma Daya karshe ya yanke shawarar murabus yin daga sarauta, watakila shine silar lakaba Masa suna  Al-Zaahid (Mai gudun duniya). 

Akwai da yawansu wadanda muka manta sunayensu tare da lokutan da suka yi mulki kafin tukewarsu zuwa ga Mallam Umar (Ummarun Dallaje Wanda ya kafa tutar Shehu Usmanu a Katsina, Kuma Wanda aka wallafa littafin a zamanin sa 1807-1835). Karshe! (Godiya ga SALISU BALA Wanda ya alkinta Mana shi)


ASALIN Sunan Katsina

Labari mafi inganci shine, sunan tsohon birnin Katsina 'DURƁI TA KUSHEYI'. Sunan mutanenta Durɓawa. Wasu na cewa asalin Durɓawa maguzawa ne tsatson mutanen NOK da Kwatarkwashi dube da kaburburansu da aka samo masu tsayi kamar falwaya, amma waɗansu na cewa asalinsu Mallawa ne daga Mali suke.

Da akwai mabanbantan Ra'ayoyi dangane da ASALIN inda aka samo Sunan  KATSINA

1. Ra'ayi na farko na cewa, an samo sunan ne a zamanin Sarki MUHAMMADU Korao, a lokacin da ya Sanya wani makusancinsa mai suna Katsina ya ringa duba yadda ake Gina ganuwar Birnin a madadinsa. 

2.  Ra'ayi na biyu: Akace sunan Katsina ya samo asali ne daga Sunan wata mace mai suna matar sarki Mai suna KATSI wadda ta fito daga  Durbawa, mazaunan birnin na farko. Ance ta bar tsohon garin Katsina ne zuwa inda sabon birnin yake, a lokacin Yana matsayin karamin kauye, ba tare da an sani ba, da aka bazama nemanta sai aka risketa, shine mazaunan garin suke cewa 'Ai KATSI NA NAN'.

3. Ra'ayi na uku na cewa Sunan Katsina  ya samo ne daga wani Sarki da aka taba yi Mai suna Katsina Dan Bawo. Amma marubuci Tijjani Lawal Ingawa yace Sarki Katsina dan Kumayo ne a wani rubutunsa.