SHIN FIR'AUNAN DA YAYI ZAMANI DA ANNABI MUSA (A.S) BAHAUSHE NE?
Sadiq Tukur Gwarzo, RN.
08060869978
Kashi na ɗaya.
Babu jimawa, farfesa Umar Elzakzaky Al-Bahaushe yayi hasashen cewa kwayoyin halittun hausawa dana tsoffin misirawa sunyi kamanceceniya, har ma yace yana kallon kamar firaunan dayayi zamani da Annabi Musa A.S bahaushe ne.
A wani rubutu da Dan Jarida Ibrahim A. Waziri ya taɓa wallafawa a jaridar weekly Trust ta ranar 22, ga watan disambar shekara ta 2007, an ruwaito Farfesa Umar El Bahaushe yana cewa "Gaskiya ce bayyanan-niya cewar asalin kalmar 'Hausa' na iya samo tsatsone daga kalmar 'Habasha'" kalmar da ake amfani da ita wurin zayyana wani yanki wanda a yanzu ake kira Ethiopia.
Haka kuma, ya bada misalin koda kalmar nan ta Hausa 'kwankwaso' tana da ma'ana ɗaya a yaren Amharic na waccan kasa waɗanda akace sun samo salsala ne daga Sarauniya Kandace wacce Annabi Sulaimanu A.S ya aura har kuma suka haifi ɗa dashi.
Farfesa Umar El zakzaky Al Bahaushe yace" kwayoyin halittar Fir'auna Seti I, wannan daya yayyanka yahudawan zamaninsa, da kuma na magajinsa Fira'una Remesis II, wanda yayi zamani da Annabi Musa A.S sunyi kamanceceniya da kwayoyin halittar mutanen kano na yau, musamman ma na cikin kwaryar badala."
Sai dai Farfesa Munzali Jibrin, Farfesa Abdullahi Elkanawy da wasu masana da dama sunyi watsi da wannan bincike. Ga abinda ya fito daga makalar masanan kamar yadda suka gabatar a wani taro daya gudana a Arewa House dake kaduna:
"Kuskure ne a hada asalin wancan Fir'aunan da kano tunda Gawar Mornoptah, dan Fir'auna Remeses II, fir'aunan da aka halakar a ambaliyar ruwa yayin da yake bin sawun Annabi Musa A.S don ya halaka shi, wadda Masani Loret ya gano a shekarar 1898 a tsohon birnin Thebes ta nuna cewar kwayoyin halittar ta sunfi kamanceceniya dana mutanen egypt ne ba mutanen kano ba".
Koda yake, wasu daga shahararrun mutane a kasar Hausa sun rike a zuciyarsu cewar Tabbas akwai alaka tsakanin Habasha da Hausa, daga cikinsu kuwa akwai Marigayi Malam Aminu Kano da Marigayi Dan Masanin Kano Yusuf Maitama sule, amm waɗancan masana sunyi ikirarin cewar nwayoyin halittar jana'ar kano dai-dai da wani bincike da sukayi daga wata makabartar kano ɗin, ya nuna sunfi kamanceceniya ne da Sharifai, larabawan Madina ba Fir'auna Remesis ba.
Akwai kuma wani rahoton masana wanda ya taɓa nuni da cewa shi kansa Annabi Musa (A.S) da yayi zamani da firaunan Misira Remesis II, yana da alaka da Hausawa. Watakila an faɗi hakan ne saboda kasancewar kowa daga masana ya gamsu da cewa mahaifiyar Annabi Musa A.S bakar fata ce 'yar Habasha.
Koda yake, wasu na ganin ba abin mamaki bane don an samu alaka ta jini tsakanin Fir'aunonin Misira da hausawa, kasancewar yadda fir'aunonin suka rinka yin yake-yake da kasar bakar fata ta waccan lokaci da ake kira Nubia, kamar misalin firauna Seti I wanda ya gabaci firaunan Annabi Musa A.S, ana ganin yasha tura sojoji yin yaki da Nubia, ciki kuma har da'ya'yansa, tana iya yiwuwa ta hanyar kamen bayi mata da saduwar auratayya zuriya ta fita daga garesu.
To amma duk ba wannan ba, a shekarar 2013, Shafin DNA Tribes na yanar gizo ya wallafa cewa babban binciken da suka gabatar akan kwayoyin halittar Firauna Remesis II da ake tsammani dashi Annabi Musa A.S yayi zamani, ya nuna cewar kai tsaye kwayoyin halittarsa tafi kamanceceniya data mutanen tsakiyar Afirka.
Daga nan sai suka ce, kwayoyin halittar kuma suna kamanceceniya da mutanen da suka fito daga Kudancin afirka da kuma Yammaci, watau inda kabilar Hausawa suke kenan.
Amma kuma kwayoyin halittar gawar ɗansa dake kwance kusa dashi, ta nuna cewa yafi kamanceceniya kai tsaye da mutanen Afirka ta kudu, daganan sai Afirka ta tsakiya, sannan Afirka ta yamma inda hausawa suka fito.
Wannan duk ga waɗanda suka fahimci kimiyyar kwayoyin halityu, ba komai yake nunawa ba sai cewar tabbas, akwai wani yanki na jinin bahaushe daga fir'aunan dayayi zamani da Annabi Musa A.S da kuma ɗansa.
Idan kuwa haka ne, fahimtar mu ga kimiyyar kwayoyin halitta da kuma duban mu ga asalin Habasha, da alakokinta da wannan kasa ta Hausa ne kaɗai zai iya tabbatar mana shin akwai alaka tsakanin Fir'aunan da yayi zamani da Annabi Musa A.S da Hausawa ko Babu?

No comments:
Post a Comment