Saturday, 23 January 2021

01- HIKAYAR SAIFUL MULUKI DA ALJANNA BADI'ATUL JAMALI

 HIKAYAR SAIFUL MULUKI DA ALJANNA BADI'ATUL JAMALI

NA ƊAYA

A zamanin da, anyi wani sarki daga cikin sarakunan Ajamawa a Hurusan, sunan sa Muhammadu ɗan Sabbaki. Kowacce shekara yakan kai yaƙi ƙasashen Hindu, da Sindu, da Sinnu dama wasu ƙasashen na Ajamawa. Shi kuwa adalin sarki ne, ga shi kuma da jarumtaka kamar ache ya fi kowa. Al'adarsa kuwa itace yana matuƙar son labaru da hikayoyi da waƙoƙi da firarraki da labarun mutanen da ke gare shi.

A haka har sai da ya kasance duk wanda ya samu baƙon labari ba ya zamewa ko ina sai wurin sa, idan kuwa har labarin ya gamshe shi, sai aga ya cika mutum da kyaututtukan dinari da tufa guda dubu da ƙwarƙwara da taka-haye a matsayin sallamar sa.

  Labarin wannan sarki ya shahara a cikin alƙaryu.

  Sai dai kuma wannan Sarki, yana da wani mugun waziri, bahili, mai yawan hassada ga mutane. Idan sarki ya yi wa mutane alheri sai ya rinƙa yin hassada, ya riƙa cewa: "Irin abin nan da kake yi, shi yake ƙarar da dukiya, har gidaje su risbe". 

  Sarki kuwa ya kan mayar masa da martanin cewa " wannan hassadar kace waziri, al'amari dukkan sa ga Allah yake".

   Ana nan rannan Sarki yaji labarin wani malamin  mawaƙi, attajiri mai yawan alheri, sunan sa Hassan. Wanda darajar sa ta ɗaukaka, mutane sai yabon sa suke yi, suna cewa babu tamkar sa a wajen hikima da da-ɗa-ɗan hikayoyi. Sai kuwa Sarki ya aika aka kirawo masa shi.

   Da zuwan Hassan, sai sarki yace masa " Ya Hassan, kayi sani cewa waziri na ya saɓa mini alkawari, ya zama maƙiyina domin dukiyar da nake baiwa mawaƙa da masu hikayu. Ina son yanzu ka gaya mani wani baƙon labari mai-ban al'ajabi wanda ban taɓa jinsa ba.

 Idan har ya ƙayatar dani, zan baka yankin ƙasa ta guda ɗaya, kuma in sanya dukkan abin da na mallaka cikin hannun ka, in ɗora ka bisa kan waziri na dama gare ni, ka zamo mai yin hukunci ga talakawa.

  Idan kuwa baka zo mini da abin da na ce maka ba, zan washe ka, in kore ka daga ƙasata".

  Hassan yace "Ran sarki ya daɗe, an gama.. Amma idan ka yarda, kayi hakuri, ka bani jinkiri na shekara ɗaya tak. Bayan haka, zan baka labari wanda baka taɓa jin kamar sa ba, wanin ka ma bai taɓa jinsa ba daɗai a ƙasar nan idan Allah yaso".

Sarki yace "Jeka nayi maka wannan jinkiri, amma da sharaɗin banda fita, banda hawa, sannan kada kazo guri na sai bayan shekara ɗaya".

  Daga nan Hassan attajiri ya durƙusa yayi bankwana da saeki ya wuce gida.

   Da komawar sa gida sai ya zaɓi mutane biyar malamai marubuta mahankalta acikin bayin sa. Yace dasu " Ban neme ku ba sai don wannan rana mai kamar ta yau, ina so ku taimake ni bisa ga biyan buƙatar sarki, ku tsamar dani daga hannun sa"

  Suka ce " Rayukan mu fansa ne gareka ya sidi, me kake da buƙata a tare damu?".

  Attajiri Hassan yace " Ina son kowanne ɗayanku ya shiga ƙasashe, ya binciki malamai da ma'abota labaru da hikayoyi, ku tono mini labarin Saiful Muluki.. 

Ko a gurin wa kuka same shi, kuyi ƙoƙarin da ya baku labarin ku ruwaito shi gare ni, ko da dinare dubu ya nema a gareku ku bashi, ina son kuzo mini dashi.

  Wanda duk a cikin ku yazo mini da wannan labarin a cikin ku, na ƴanta shi, zan bashi komai na duniya guda dubu, kuma zai zama shine wakilin gidana duka".

   Daga nan bayi suka ɗauki guzurin tarin dukiya sannan suka bazama cikin duniya suna masu neman hamshaƙin labarin Saiful Muluki da Aljanna Badi'atul Jamali. 

Ɗaya daga cikin su ya nufi Hindu da Sindu, na biyun su ya nufi ƙasar Ajami da Sinu, na ukun su ya nufi ƙasar Yamma, na huɗun su ya nufi ƙasar Sham, sai na biyar ɗinsu ya nufi ƙasar Masar. ..

TARIHIN GARIN KURA

 

Sunday, 17 January 2021

TARIHIN DORAYI

 TARIHIN ƊORAYI

Sadiq Tukur Gwarzo

Marubuci Alhaji Ahmad Bahago ya ruwaito a littafin sa KANO TA DABO TUMBIN GIWA: Tarihin Unguwannin kano da Mazaunanta da Ganuwa da Kofofin Gari, cewa;- A da duk filin wannan unguwa ta Ɗorayi itatuwan ɗorawa ne. Shi ne dalilin da ya sa ake cewa da wannan waje Ɗorayi.

Yace kuma "an kafa unguwar tun zamanin sarkin kano Abdullahi Maje karofi. Asalin mazauna unguwar bayin sarki ne, kuma akwai gidajen ƴaƴan sarki a wajen. Sarkin Haɗeja da na Kazaure a unguwar suka zauna suka yi karatu".

  Sai dai kuma littafin Tarihin Kano 'KANO CHRONICLE' ya kawo zance mai saɓawa wannan, sannan ya sanya kafuwar Ɗorayi nesa sosai da abinda Alh Ahmad Bahago ya ruwaito.

  Duk da yake littafin Kano chronicle bai kawo zance game da asalin inda kalmar 'Ɗorayi' ta samo asali ba, amma an jiwo sunan wani bamaguje mai suna 'Ɗoriyi (ko Ɗorayi) ɗan Bugazau' ɗaya daga waɗanda suka so yiwa sarautar kano zagon ƙasa a zamanin sarkin kano na shidda Naguji ɗan Ɗariki, lokacin da alaƙa ta soma tsami kenan tsakanin masu riƙe da sarautar kano jikokin Bagauda da kuma masu bautar tsumburbura.

   Ga abinda yazo a kano chronicle game da unguwar Ɗorayi:-

 A cikin zamanin Sarki na goma sha biyar Dawuda Baƙin-damisa, wani sarki mai suna Dagaci ya zo daga Barno tare da jama'a masu yawa da malamai. Shi ne yazo da bayanin bangar doki da pampami da tuta da bindiga.

  Yayin da ya iso Bampai, sai sarkin Kano ta fita zuwa gareshi. Sa'ad da ya sadu dashi, sai ya ganshi sarki ne mai-girma, ya bar shi ya komo gida, ya yi shawara da jama'arsa yace "wannan mutum ina zai zauna?" 

   Sai Galdaima Babba ya ce masa "Idan ka bar shi ya zauna a cikin wannan alƙarya wallahi zai mallaki wurin da ya zauna duka". 

Sarki yace "A ina zai zauna acikin wannan alƙarya tare da rundunar sa, Ganuwa ta kuntata da mutane, sai ko a ƙara ta?"

  Sa'annan sai Sarki ya aiki Galadima Babba wurin sa ya zo da shi, aka gina masa gida a Ɗorayi, da jama'ar sa duka. 


Saturday, 2 January 2021

1. TAKOBI A HANNUN MATA: TARIHIN FITATTUN MATA DA SUKA YI IKO DA KANO

 TAKOBI A HANNUN MATA: TARIHIN FITATTUN MATA DA SUKA YI IKO DA KANO


Sadiq Tukur Gwarzo


1.0 GABATARWA

Ɗumbin Tarihi, ƙasaitacciyar masarauta, dogon zamani, sharafi, nasibi, iko da nufi, tumbatsa da nasara, duk sun tabbata ga kano. Mutane da dama sun yiwa kano kirari mai nuna kwarzantakar ta gami da ɗaukaka a tsawon zamunna, amma watakila mafi daɗaɗa rai shine wanda Farfesa Sani Zahraddin, babban limamin kano ya kawo yayin ta'aliƙin sa ga littafin Tarihin Kasuwanci da ƴan kasuwar kano wanda marigayi marubuci Maje Ahmad Gwangwazo ya wallafa, yana mai cewa: ana yiwa kano kirari da:- '

Ka misulu alfin, 

Jalla babbar Hausa, 

Gari ba kano ba dajin Allah, 

ko dame kazo an fika'.

  Manufar wannan rubutu shine zaƙulo wasu fitattun mata waɗanda suka taka rawar gani wajen iko da kano, ko ace waɗanda suka samu gagarumar nasarar aiwatar da muradun zukatun su sabili da nasabar su da masu zartar da iko a kano. Wannan birni na kano mai tsohon tarihi bai taɓa samun jagora mace ba a iya abinda muka riska, amma kwatan-kwacin mulkin da turawan mulkin mallaka suka aiwatar a ƙasar hausa (in-direct rule) ta hanyar sarakunan gargajiyar lokacin su, akan iya cewa an samu zamunnan da mata ke irin wancan mulki a sakaye. Don haka wannan rubutu zai bi diddigin irin waɗannan mata ne tun daga zuwan Bagauda kano har zamanin da muke ciki (2021) da yardar Allah.

 2.0 KAƊAN DAGA TARIHIN KAFUWAR KANO DA SOMA IKO DA ITA

Akwai mabanbantan zantuka game da tarihin kano.

Amma dai ama iya cewa shekaru sama da dubu biyu da suka gabata, sun tabbatar da cewa akwai mutane masu rayuwa a Afirka ta yamma. Waɗannan mutane basu da wata sana'a sama da farauta. A wancan lokacin sana'ar noma bata shahara ba a duniya, don haka mutane suka fi dogaro da farautar namun daji a matsayin aikin yi. Lokaci yana tafiya, har labarin wani babban dutse ya fara zama shahararre a kunnuwan mafarauta. Dalili shine, akwai namun daji masu yawa a yankin da dutsen yake. Sannan ana iya haƙo Tama sinadarin haɗa ƙarfe a wurin. Waɗannan abubuwan suna daga mafi daraja a wancan lokaci. Domin akasarin kayayyakin farautar waɗannan mutane da duwatsu aka sassaƙa su, don haka suke da matuƙar buƙatar kayayyakin ƙarfe masu daraja da sauƙi wajen sarrafawa. Sunan wannan dutse DALA.

    A bisa wata mahangar ta masana, wasu na ganin yankin Dala a matsayin wuri ne wanda k'abilu daban-daban (kazo-na-zo) ke taruwa domin shiga dajin dake kusa dashi don yin farauta. Shine har wasu ke ganin babu takamai_miyar ƙabilar da ta fara zama a yankin. 

  Haka kuma babu takamaiman wanda ya fara zuwa bakin wannan dutsen, wasu sunce mambobin wata ƙabila da suka taso daga wani birni mai suna Dahlak dake Habasha (daga baya sunan ya koma Dala) ce ta fara zama a wurin, daga nan aka sanyawa dutsen suna Dala, wasu kuma suka ce sunan wanda ya fara gina gida akan dutsen tare da fara rayuwa akai shine Dala. Don haka ake yiwa dutsen kachokan laƙabi da sunan sa.

   Daga bisani dai, sai mutane suka fara zama kadan-kadan a gefen dutsen domin neman arziki. Maƙera na zuwa don haƙo tama da ƙarfe tare da sarrafawa, mafarauta kuma na zuwa don siyen ƙarafa tare da shiga farauta a dajin dake bayan dutsen Dala, kamar dai yadda yake a tarihi, za'a ga cewa mutanen da suka gabacemu sunfi rayuwa a wuri mafi daraja. Watau sa'ar da ruwa yake da tsada a wuri, sai kaga mutanen sun gina gari a wurin da ruwa yake, kamar yadda ya faru a garuruwan Makkah da wasun su.

  Waɗanda suka ce Dala ne ya fara zama akan dutsen, sun cigaba da cewa ya rayu tsawon shekaru masu yawa akan wannan dutse, tare dashi akwai matarsa da 'ya'yansu bakwai, huɗu maza uku mata. Wani mai suna Garegaji aka bayyana a matsayin babban ɗansa, shine kuma akace uban wani ƙaƙƙarfa mai suna Nuzamu, Nuzamu kuwa ance shine ya haifi Barbushe. Barbushe mutum ne ƙaƙƙarfan gaske, wanda akace yakan iya kashe giwa ya saɓota a kafaɗa duk girmanta.

 Littafin Tarihin Kano 'Kano chronicle' ya faro tarihin kano ne daga lokacin Barbushe. Shine ma har wata masaniyar tarihin Nigeria mai suna Elizabeth Isichei tayi hasashen cewa Barbushe ɗan k'abilar Sao ne saboda yadda akace girmansa da ƙarfin sa yake yafi kamanceceniya da ƙabilar ta sao. Ƙabilar sao kuwa itace tsohuwar ƙabilar da tarihi ya nuna cewa al'ummar kanembou (Kanem) sun samo tsatso daga garesu.

  Tarihi dai ya nuna cewa a lokacin Barbushe shine sarkin mutanen dake zaune a zagayen dutsen Dala. Kuma suna da al'adar bautawa wani gunki mai suna 'Tsumburbura' wanda yake can kan saman dutsen dala, akan wata bishiya wadda take zagaye da katangu mai suna Shamus. Ance babu mai shiga wurin dodon tsafi tsumburbura sai barbushe. Duk kuwa wanda ya shiga sai ya mutu. Barbushe kuwa ance a saman dutsen yake rayuwa abinsa. Yana saukowa ga mutanen sa sau biyu a shekara domin gudanar da bikin bauta na al'ada. A lokacin mutane ke taruwa sosai a bakin dutsen na Dala suna jiran saukowar sarkinsu barbushe. Wanda yake saukowa gabanin faduwar rana. Yana mai buga ganguna. Sai yayi kirari da yabo ga tsumburbura, mutane suna tayashi. Daga nan akace sai yahau sama mutanen na biye dashi a baya har izuwa saman dutsen na dala. Wanda akace daf da isarsu saman dutsen sai mutanen su yanka hadayar da suka kawowa tsumburar, abinda sukan yanka kuwa shine ; bakin kare, bak'ar kaza, ko bak'ar akuya. Idan suka isa bakin d'akin bauta kuwa, sai kowa ya tsaya. Barbushe ne kadai ke shiga. Kafin shigarsa ance sai yayi kirari da kuwwa. Yana cewa "Sai ni magajin dala. Mutane dole su bini, ko sunƙi ko sun so". Daga bisani idan ya fito, sai ya jagoranci yin bautar tsumburbura, wadda ake zagaya dakin bauta ana rawa da kiɗa tsirara.

  Idan an kammala kuma sai aci asha a wurin. Sannan sai barbushe ya fadi saƙon da tsumburbura ya bashi. Saƙon da a mafi akasari akace labari ne na abubuwan da zasu faru a shekara mai zuwa. 

Duk waɗannan abubuwa ana hasashen sun faru ne a shekaru ƙasa da shekara ta 900AD (miladiyya) bayan wafatin Annabi Isah AS. Koda yake Marubucin littafin Kitab Al-buldan mai suna Al'yaqubi bayan yawace-yawacen sa da yayi a yammacin Afirka, ya ruwaito a shekarar 872-873 cewa "akwai wata masarauta awani wuri dake tsakanin masarautar kanem da tafkin kwara (dai-dai da ko kuma kusa da inda kano take a yanzu), mai suna 'HBSH'. Sunan mai mulkinta 'MRH' sunan birnin ta 'ThBYR'. Rashin wasulla a waɗannan kalmomi yasa shakku da jayayya a tsakanin masana tarihi. Domin wasu na hasashen sunan masarautar shine Hausa, (domin kuwa sunce HBshH na nufin Habasha ne), sunan da ake tsammanin daga cikinsa aka samo sunan Hausa. Wasu kuma na hasashen cewa masarautar ta auku ne a kusa da kano, amma daga baya kafuwa da ƙarfin da kano tayi ya rusa ta, ya kuma yi sanadiyyar komawar mutanen ta zuwa kanon.

   Koma ya abin yake, daga baya littattafan tarihi na kano misalin 'Kano chronicle' (har yanzu ana taba-bar wanda ya rubuta shi),  sun ruwaito cewa wani mai suna Bagauda ne ya zama sarkin kano na farko a tarihi a shekarar 999AD. Shi kuwa Bagauda wasu na cewa jikan Bayajidda na Daura ne, kuma daga garin Gaya suka taso shi da al'ummar sa, wai sunan su shine 'Abagayawa' (waɗanda suka zo daga gaya) ko ɗaya daga Gaudawa, shiyasa kuma ake kiransa da 'Bagauda', ma'ana, mutumin- Gaudawa, kamar yadda mallam bahaushe ya fitar da Bakibɗe daga Kibɗawa. 

   Wasu kuma  suka ce sam, Bagauda ba jikan Bayajidda bane, yazo yankin Dala ne tare da wata runduna mai yawa kamar yadda Barbushe ya taɓa bada labarin zuwan su, kuma ainihin sunan sa shine kano, don haka daga sunan sa kano ta samo asalin sunan ta. Amma kuma wasu sun tafi akan cewa Kano, sumam waninshahararren mautum ne mainsana'ar ƙira wanda yayi sharafi a gefen tsaunin Dala, wanda har ɗaukakar sa ta sanya ake kiran gurin baki ɗaya da sunan sa. Don haka a mahangar su Bagauda daban, Kano daban.

  3.0 FITATTUN MATA DA SUKA YI IKO DA KANO..