Sunday, 17 January 2021

TARIHIN DORAYI

 TARIHIN ƊORAYI

Sadiq Tukur Gwarzo

Marubuci Alhaji Ahmad Bahago ya ruwaito a littafin sa KANO TA DABO TUMBIN GIWA: Tarihin Unguwannin kano da Mazaunanta da Ganuwa da Kofofin Gari, cewa;- A da duk filin wannan unguwa ta Ɗorayi itatuwan ɗorawa ne. Shi ne dalilin da ya sa ake cewa da wannan waje Ɗorayi.

Yace kuma "an kafa unguwar tun zamanin sarkin kano Abdullahi Maje karofi. Asalin mazauna unguwar bayin sarki ne, kuma akwai gidajen ƴaƴan sarki a wajen. Sarkin Haɗeja da na Kazaure a unguwar suka zauna suka yi karatu".

  Sai dai kuma littafin Tarihin Kano 'KANO CHRONICLE' ya kawo zance mai saɓawa wannan, sannan ya sanya kafuwar Ɗorayi nesa sosai da abinda Alh Ahmad Bahago ya ruwaito.

  Duk da yake littafin Kano chronicle bai kawo zance game da asalin inda kalmar 'Ɗorayi' ta samo asali ba, amma an jiwo sunan wani bamaguje mai suna 'Ɗoriyi (ko Ɗorayi) ɗan Bugazau' ɗaya daga waɗanda suka so yiwa sarautar kano zagon ƙasa a zamanin sarkin kano na shidda Naguji ɗan Ɗariki, lokacin da alaƙa ta soma tsami kenan tsakanin masu riƙe da sarautar kano jikokin Bagauda da kuma masu bautar tsumburbura.

   Ga abinda yazo a kano chronicle game da unguwar Ɗorayi:-

 A cikin zamanin Sarki na goma sha biyar Dawuda Baƙin-damisa, wani sarki mai suna Dagaci ya zo daga Barno tare da jama'a masu yawa da malamai. Shi ne yazo da bayanin bangar doki da pampami da tuta da bindiga.

  Yayin da ya iso Bampai, sai sarkin Kano ta fita zuwa gareshi. Sa'ad da ya sadu dashi, sai ya ganshi sarki ne mai-girma, ya bar shi ya komo gida, ya yi shawara da jama'arsa yace "wannan mutum ina zai zauna?" 

   Sai Galdaima Babba ya ce masa "Idan ka bar shi ya zauna a cikin wannan alƙarya wallahi zai mallaki wurin da ya zauna duka". 

Sarki yace "A ina zai zauna acikin wannan alƙarya tare da rundunar sa, Ganuwa ta kuntata da mutane, sai ko a ƙara ta?"

  Sa'annan sai Sarki ya aiki Galadima Babba wurin sa ya zo da shi, aka gina masa gida a Ɗorayi, da jama'ar sa duka. 


No comments:

Post a Comment