Assalamu Alaikum
Tarihin shafin facebook
wani matashi wanda har yanzu shekarun sa
basu wuce ashirin da bakwai ba, wanda kuma ya
samu damar shiga sahun attajiran duniya, mack
zuckerberg ne ya qirqiro wannan shafin yayin
karatunsa a jami,ar Harvard dake qasar Amurka.
A ranar 4 ga watan fabrairun shekara ta 2004 ya
samu nasarar liqa shafin sadarwar mai suna The
facebook da yanar gizo bayan ya dauki dawainiyar
tsara shafin daga na'urarsa mai kwakwalwa, a
lokacin ne ABOKANAN karatunsa suka fara yin
rijista da shafin saboda tsarin shafin anyi shine
domin sauqaqewa daga wani littafin da yan
MAKARANTAR keyi wanda yake dauke da sunan
dalibi da adireshinsa da wasu bayanai, sunan
littafin Exeter, kwatankwacin photo album da
wasu daliban makarantu keyi a yanzu.
A cikin sati biyu da liqa shafin na The
facebook, sai da aka samu kimanin rabin daliban
wannan jami,a ta Harvard sunyi rijista, daga nan
sai makwabtan jami'o'i suka nemi izinin fara
amfani da shafin, kafin a dauki tsawon lokaci sai
shafin ya bunqasa da dalibai daga jami'o'i daban-
daban, wannan ne yasa shi mai shafin Mark
komawa da baya ya bunqasa shafin, saboda
yanayin yadda ya qera shafin baiyi hasashen
samun mutanen daya samu ba, wannan ne yasa
yayi tunanin buda shafin yadda kowa da kowa zai
iya amfani dashi.
Daga nan sai ya nemo abokanansa domin su
tayashi wannan aiki, ya dauko su a matsayin haya
zai rinqa biyan su, wani mai suna Dustin Moskorits
ne ya zama mai jagarantar fagen sarrafawar
shafin (programming), Eduard saverin ya zama
mai jagorancin harkar siye da siyarwa na shafin,
chris Hughes ne ya jagoranci harkar ciyar da
shafin gaba da da bunqasa shi, sai kuma Andrew
Mccollum wanda ya dauki dawainiyar qawata
shafin da zane_zane irin na yanar gizo (web
designing). Ba'a jima dayin haka ba sai suka
yanke shawarar bude cibiyar kamfanin nasu, inda
suka amshi hayar wani qaramin gida a Palo Alto,
cikin jihar california, a wannan lokacin ne kuma
suka ci nasarar siyan haqqin mallaka na sunan
kamfanin a yanar gizo, daga nan sunan ya koma
kamar yadda yake a yanzu "faceboo.com".
Amfanin Shafin Facebook
A yanzu dai wannan shafin sadarwa ba baqo bane
har a cikin mu hausawa, domin ya zamo wani
dandali na yan mata da samari, yayin da wasu
malaman addinai da yan siyasa tare da kamfanoni
da qungiyoyi ke amfani da shafin don cimma
burikansu. Mutum yana iya neman wasu
abokanan sa da sukayi makaranta ko wata
huddar arziqi a wannan shafin na facebook, haka
kuma yana iya wanzuwa domin sadar da
zumuncin dake tsakanin su ta hanyar gaisuwa da
fatan alheri a garesu a kullum ko kuma jefi-jefi,
sannan akwai damarmaki na haduwa da sabbin
abokanai a wannan shafin.
Sai dai amfanin nasa bai tsaya anan ba, domin
a yanzu akawai dumbin mutanen da suka maida
shafin wajen cin abincin su, inda a duk wata suke
samun maquden kudaden shiga a shafin, kuma
kamar yadda kowa ya sani, inda mutane suke
anan ake zuwa yin talla, don haka shafin facebook
ya zamo wata kasuwa mai dauke da dumbin
mutane, akwai kimanin mutanen Najeriya miliyan
biyar da sukayi rijista da shafin, yayin da a duniya
kuma akwai kimanin mutane miliyan dari biyu
duk da sukayi rijista da shafin.
shafin facebook yazo da salo na sauqaqawa
wanda yasa ya zarce sa'a ga sauran shafuka irin
sa kamar squido.com, xanga.com,
classmates.com, youTube.com har ma da
shahararren shafin nan na Myspace, mai iya
gogaiya da shafin facebook shine shafin
Twitter.comidan aka dauke shafin
google.comwanda ya zarce sa'a. Daga cikin
abubuwan sauqaqawa da facebook ya kawo shine
damar qirqirar shafi naka nakanka a kyauta. Duk
wanda yake son qirqirar shafinsa idan ba'a
facebook bane sai ya rinqa biyan kudi duk
shekara bayan ya sayi sunan shafin (domain
name), amma sai gashi facebook ya bada dama,
ka qirqiri shafi akan duk abinda kakeso indai bai
danganci cin mutumci ba, sannan bayan ka
qirqiri shafin, kana da damar aikawa da katin
gaiyata ga mutane kyauta, kana da damar tallata
hajar ka idan kai dan kasuwane a shafin naka,
kana da damar sayar da littattafai idan kai
marubuci ne, kana da damar sayar da abubuwan
wasa da sauran masarrafan kwamfuta a shafin
idan
kai programmer ne, kana da damar taimawa da
bada ilimi ga dalibai ko sauran mutane idan kai
malami ne,kana da damar neman shawarwari da
jin ra'ayin jama'a idan kai dan siyasa ne. a taqaice
dai damarmakin suna da yawa ga wanda yasan
yadda zaiyi amfani dasu, kawai dai abinda yake
aakwai shine shafin na facebook.comzai ciri wata
yar la'ada aduk sanda ka kasa wata haja taka aka
siya kuma.
Baya da wannan kuma sai wana damar ta
kyauta, inda ko ayanzu na sani akwai kungiyoyi
da kamfanoni da suke cin gajiyarta, damar itace
ta qirqirar dandali(group) a kyauta don tattauna
muhimman abubuwa. Qungiyar yaqi da cin hanci
da mai fafutukar yancin talaka duk suna da
wannan dandali, mawaqa da masu wasan
kwaikwayo suma suna da wannan dandali. Haka
nan ana samun dalibai daga wasu makarantun da
suke bude irin wannan dandali domin tattunawa
a tsakaninsu, likitoci, yan jaridu da sauran
rukuno ...
nin al'umma duk sun bude irin wannan dandali a
shafin yanar gizo na facebook.com. Na qarshe
kuma shine mutum yana iya amfani da
masarrafan shafin facebook da wasanni na games
a kyauta a shafin, har ma ya jawo hankulan
mutane don suyi mu'amala dashi a shafin daya
bude ko kuma dandalin daya bude. abubuwan
sun hada da cookbook, zoho office 2004, Task
master da sauransu.
Yadda ake rijista a shafin facebook.comDomin
yin rijista a wannan shafin, sai a ziyarci
wannanadireshin http://www.facebook.com,idan
shafin yabude sai aje a latsa inda aka rubuta ''sign
up'' a , daga nan shafin zai bude su bada fom da
za'a cike. Akasari suna tamyar cikakken suna,
kwanan wayar haihuwa, lambobin sirri, sai lambar
waya ko adireshin email. Ko dai mutum ya bude a
wayarsa ta sadarwa ko kuma ya bude a na'urar
kwamfuta. Ga wanda zai bude da wayar sadarwa
yana buqatar layin sadarwa, inda acikin fam din
dazai cike na shafin zai rubuta lambar layin
sadarwar, idan kuma a na'urar kwamfuta ne,
mutum yana buqatar ya mallaki adireshin email
wanda zai cike a fom din. Domin mallakar
adireshin email, sai a ziyarci daya daga wadannan
adiresoshi masu bada damar bude email a
kyauta.: http://www.yahoomail.com,http://
www.gmai.com,http://www.live.comko kuma
http://www.altavista.com,idan an bude shafukan,
sai a latsa madannin 'sign up' ko kuma inda aka
rubuta 'create gmail account'. Mutum
zai cike fom din.
Yadda ake bude shafi ko dandali
Idan har mutum ya gama yin rijista da shafin na
facebook.com, yayi 'sign in', gidansa ya bude
(Home page) daga gefe zai ga inda aka rubuta
'create Grouf' zai kuma ga inda aka rubuta 'create
page', don haka sai ya latsa wanda yafi sha'awa
daga ciki, sannan yabi a hankali ya cike fom din
da zasu bashi, ya zabawa shafin nasa ko dandalin
nasa suna mai qayatarwa wanda zai ja hankalin
mutane, sannan ya daure ya qayata shafin da
hotuna masu ma'ana, da kuma rubutu akan abin
da ya gina shafin. ya danganta dai da abinda
kake so ka cimma wajen gina shafin naka,
kasuwanci ne, wa'azi ne, koyarwa ce da sauransu.
Daga Sadiq Tukur Gwarzo
08060869978
No comments:
Post a Comment