Sunday, 10 December 2017

LABARIN BAWA DORUGU 9

LABARIN DORUGU, BAHAUSHEN DAYA FARA ZAGAYA TURAI
Kashi na Tara
Daga Sadiq Tukur Gwarzo
Dorugu yaci gaba da cewa "Ina tsammanin birnin kano
nada kofofi sha hudu. Bayan birnin akwai gonaki da
koramu, ginin birnin yana da tsawo. An ginashi da
yimbu. Daga ciki suna da wani dutse sunan sa Dala.
Idan ka zauna kusa dashi kayanka suna yin Ja kamar
goro idan farare ne kayan naka. Naji a gurin kanawa
wai wani mutumin Inliz ya taba cewa zai fitar da zinare
acikin dutsen amma kuma yunwa zata fada ga gari.
Shikuma sarki yace indai yunwa zata fada a gari to a
barshi.
A wajajen Dala, babu gida sai fili mai ciyawa inda
dabbobi ke kiwo. Bayi suna zuwa yanko ciyawa sukai
gida. Akwai ruwa a wajennan. Kasuwar birnin kano
kuwa tana da girma. Akwai takalma, tandun kwalli,
barkono, gishiri, nama, itace, riga, zane, alharini,
matsokaci ko madubi, silin alharini, takobi, alewa,
shanu, rakuma, 'ya'yan itace, hatsi, giddan allura,
duwatsun kwalliya da takanda.
Makafi da masu gani duka a garwaye suke. Kasuwa ta
cika. Kusa da kasuwar akwai babbar fadama, ko idon
ruwa dake tsakanin gari. Wani lokacin yakan cika
kamar zashi shiga ga kasuwa. Sai sukan tare ruwan da
tasar karfe. Haka nan naga saman ruwan duk kainuwa.
Idan ka zaga marinan kano, kana ganin mutane da
yawa, wadansu suna rina alharini, wadansu suna rina
riga, wadansu kuma na dinki. Anan ake aikin fata mai
kyan gani. Idan zasu rina riga, suna gina rami gaba
hudu ko biyar, watakila yafi nan, su gyarta cikinta da
yimbu, idan ta kekashe sai su Tsira Baba su cikata da
ruwa, kana susa Baba bisa gareta har ya kusa ga
shashinta, du dauki sanduna masu tsawo guda hudu su
fara daka Baba har ya fara jini, su barta ta kwana, su
rufeta kwanaki hudu ko biyar, su budeta, su wanke
zane fari, in daudarsa ta fita sai susa ga cikin marina.
Mutumin da yake rinin hannunsa yana yin baki kamar
aduwa. Gurin da Baba yake girma shine ga gari, ko a
daji. Garin kano cike yake da Baba, da auduga, da
barkono, da taba.
Akwai mutane daban-daban a cikin birnin kano.
Larabawa, abzinawa, bare-bari, nufawa, fulani,
yarubawa, wadawa, adamawa da sauransu. Mutane da
bayi masu magana daban-daban. In ka shiga ga birnin
kano sai kayi hankali da kayanka, don sun sace tasar
mu sunsa ga karkashin babbar rigarsu. Suna da kwarya,
duk da ita muke shan ruwa. Ita kuwa a gona take
girma.
MUN DAUKI HANYAR TURAI
Da muka tashi daga nan, munyi tafiyar wata daya ko
fiye muka isa Kukawa. Mutane sukayi ta murna, suka
ce mana munji kuna Timbuktu an kashe ku. Mukace
bamu mutu ba, amma munsha wahala acikin Timbuktu.
Muka zauna kadan, sannan muka bar borno amma bada
son mutane ba. Mukayi tafiya ta kusan kwana shida
kana muka iske wani gari. Anan ne ake siyan dabino da
shinkafa da Gari, saboda idan kayi gaba zaka dade
kafin kaje wani gari, har muka hadu da wani mutum
mai bayi kamar ishirin ya shigo cikinmu don tafiya.
Daga nan muka shiga cikin rairayi (sahara), munyi
tafiya sosai, ga gajiya, nima tilas na sauka bisa rakumi
saboda suma sun gaji, ga rashin ruwa, har muka tarar
da wata rijiya rairayi ya cikata, tilas muka gina wata.
Muka cigaba da tafiya a rairayi inda babu ciyawa ko
kadan, duk inda ka duba sai kaga gawarwakin dabbobi
ko na mutane, kishirwa ta kashesu. Mukayi ta tafiya
har muka hango wani gari, daga nan muka fara murna
har da harba bindiga, anan garin muka rabu da abokin
tafiyarmu Tubo mai bayi ashirin, ya wuce garinsu.
Da yake garin akwai dabino da yawa, sai muka diba,
sannan muka shiga wani daji kuma. A wannan karon
bamu da Jagaba wanda yasan hanya, amma dajin babu
rairayi da yawa. Mukayi ta tafiya har muka zaga wani
gari kusa da Murzuk, bamu dade ba muna tafiya muka
isa Murzuk din. Sai muka sauka a gidan Gunsul.
Muka kwana kamar shidda, gunsul yayi mana rakiya.
Muka hadu da wasu mutane wadanda muka isa ga
wani gari mai suna Sokuna dasu. Sokuna gari ne
karami, amma yana da mutane larabawa da yawa.
Bamu shiga cikin garin ba, garin yana da zafin rana,
rakumi da jaki suna wahala, domin sune ke debo ruwa
daga rijiya. Rijiyoyin su kuwa kana samunta gaba ishirin
ko talatin kafin su tarar da ruwa. Idan sun sanya guga
a cikin rijiya, sai su daure igiyar a jikin rakumi ko Jaki,
sai a korashi yayi tafiya mai nisa har sai gugan ya futo
da ruwan..."

No comments:

Post a Comment