Friday, 20 April 2018

HIKAYAR WASU KWARTAYE

HIKAYAR WANI BAKO GA SARKI MAI SUNA 'DUNIYA'

Tare da SADIQ TUKUR GWARZO

Akwai wani Babban bafaden Sarki a wani garin Hausawa, yana da wata mata kyakkyawar gaske, wadda ake yawan sanar dashi cewa tana tara maza a gidansa, amma sam baya yadda.
Watarana sai wata Tsohuwa ta kirawo bafaden nan, tace masa "kullum idan ka tafi fada, matarka maza take tarawa. Amma idan kanason ka gane hakan, sai kace mata zakaje unguwa kauye, acan zaka kwana, inyaso sai ka dawo kafin lokacin don ka ganewa kanka abinda ke faruwa".
  Sai kuwa bafade yace da tsohuwa, "haka nan za'ayi". Daga nan ya tafi ya samu mai ɗakinsa ya sheda mata cewa zai tafi unguwa sarki ya aikeshi kauye, bazai dawo ba sai gobe.
Bafade yahau dokin sa, ya bar gida abinsa.
Matar gida kuwa ta samu abinda takeso.
 Mai gida ya tafi bazai dawo ba, don haka ta yanke shawarar aikewa masu nemanta cewa yau gida a buɗe yake.
Daga cikin waɗanda ta aikewa akwai Wazirin gari, da Galadiman gari, da kuma wani babban bako na Sarki mai suna Duniya, dukkansu suna nemanta.
Nan da nan waziri ya aiko da kaɓakai na nama da shinkafa, yace wa matar gida ta gyarasu yana nan tafe zuwa dare.
Dare nayi kuwa sai ga waziri fagan-fagan, ya karaso gidan bafade. Matar bafade ta taryeshi da abinci da nama wanda ya aiko dasu.
Ya zauna yana ci kenan, sai ya jiyo sawun takalma, nan fa hankalinsa ya tashi, tsammaninsa Maigida ne yake zuwa. Sai yayi wuf ya shige karkashin gado.
Ashe galadima ne ya samu karasowa.
  Nan ma sai matar gida ta tarbeshi da kissa, ta gabatar masa da abincin da waziri ya bari. Galadima ya zauna ya fara cin abinci ana fira, sai shima ya jiwo sawun takalma.
Hankalinsa ya tashi, tsammaninsa Maigida ne, ya tambayi matar gida ina mafita, ita kuma sai ta nuna masa karkashin gado, inda waziri yake, nan take kuwa yayi wuf ya auka. Ashe bakon sarki mai suna Duniya ne ya shigo.
 Koda Galadima ya shiga karkashin gado, sai ya fahimci akwai wani bayan shi aciki. Daya duba sosai sai ya gane ai waziri ne.
  Galadima yace Waziri me kakeyi anan? Waziri yace Kaga Galadima, abinda ya kawoka shi ya kawo ni, saboda haka mu rufawa kanmu asiri.
Galadima yace aikuwa haka nan ne.
Suna nan suka jiyo muryar Duniya da matar gida suna taɗi, shima an bashi abinci kamar yadda aka basu. Daga nan su waziri suka gane ashe ba Maigida bane, Duniya ne.
Ba'a jima ba sai suka jiwo karar kofatan dawaki, alamar Maigida ya dawo kenan. Nan da nan Duniya yayi wurgi da kwanon abinci, ya tashi tsaye yana dube-duben mafita, can ya hango karkashin gado, sai kuwa yayi wuf ya auka.
Da shigar sa shima sai yayi arba da mutane biyu a ciki. Ya kalle su a tsanaki ya ganesu, yace Waziri!! Galadima!! Me ya kawo ku nan? Sukace muna gama ka da Allah mu rufawa juna asiri. Duniya yace to shikenan. Sai kowa cikin su yayi tsit kamar ruwa yaci su.
Maigida ya sauko daga kan dokinsa sannan ya daure shi, yace mai ɗakinsa ta bashi ruwa ya wanke jikinsa, da ta kawo masa ya gama kimtsawa, suka suka shiga cikin ɗakin tare, ya zauna a gefen gado.
Maigida yana cike da mamakin Kazafin da ake yiwa matarsa, tunda ance idan yayi haka zai kama matarsa da maza, gashi kuma yayi bai kama ta ɗin ba. Shine yake fadin "duniya.. duniya,, duniya"
Matar gida tace "Maigida me ya faru ne kake kiran duniya?"
Maigida yaci gaba da cewa "Duniya, duniya, duniya ba gaskiya"
Shikuma Duniya dake karkashin gado sai hankalin sa ya tashi, abinka da bako, tsammanin sa Maigida sunan sa yake kira. Sai yayi wuf ya ce "Haba maigida, yanzu sunana kaɗai kake kira alhali ga Waziri ga kuma Galadima?"
 Maigida ya tashi zumbur, yana fafutikar neman madoki, kafin kace haka tuni galadima da waziri da Duniya sun fara kacaniyar fitowa daga karkashin gado domin arcewa a na kare...

Thursday, 19 April 2018

TARIHIN BIRNIN LALLE DA SARKIN SU KUTTURU

Tarihin Birnin Lalle da sarkin mutum-mutumi, MAI SUNA Sarki Kututturu.

Sadiq tukur gwarzo, rn.
 
Daga abinda marubuci Dan Zubairu ya ruwaito, masarautar Birnin Lalle dake can a yankin Dakoro na Jahar Maraɗin Jamhuriyar Nijar, shahararra ce wadda ambatonta ba zai yanke ba.
  Kasancewar Birnin Lalle ɗaya ne daga tsoffin cibiyoyi ga Masarautar Gobir, ana ganin Gobirawa ne suka kafa garin. Amma kuma akwai alamu dake nuna cewar tun da jimawa Birnin Lalle ya kafu, kawai dai gobirawa  sun shigo cikinsa ne tare da kwace ikon sa.
   Birnin ya samo sunansa ne daga yawaitan bishiyoyin Lalle (wanda mata ke kunshi da kuma wanka dashi a baya) dake cikinsa.
   Birnin lalle shine birni na gaba da Gobirawa suka sauka tun bayan barowarsu daga Birnin Marandat da Birnin Toro. Da yake daman ance asalinsu daga Baghaza suke, suka shiga duniya, har kuma a hankali suka rinka sauka a garuruwa suna auratayya da yake-yake.. A haka har suka riski birnin Lalle.
   Masu cewa gobirawa ne suka kafa wannan birni na Lalle ɗaruruwan shekaru da suka gabata, sun faɗi cewar Gobirawa sun riski wajen ne yana fili sa'ar da suke neman gulbi ko tabki a wannan yanki domin su rinka gudanar da ayukkansu na noma, kasancewarsu daman bayan yake-yake, sukan jarraba noma tun tale-tale.
   Don haka ake ganin da isowar su bakin tabkin sai suka ga bishiyoyin Lalle burjik a zagaye dashi, shine sai suka baiwa wurin suna da cewa “Wannan wuri Birnin lalle kenan!”. Daga nan kuma suka yanke shawarar zama acikin sa.
    Amma dai wasu masanan tarihi sun tafi akan cewa Birnin lalle ya kafu ne tun kimanin shekaru 2000 da suka gabata. Sai dai kuma babu takamaimen sunan kabila ko mutanen da suka birnin.
   Haka kuma, ana ganin garin ya tumbatsa matuka a wani lokaci can a baya, amma ɓarkewar yunwa a wannan birni ce tayi sanadiyyar da Gobirawan suka tashi daga gareshi izuwa birnin Alkalawa dake tsohuwar masarautar Zamfara (wajajen karni na goma sha shidda).
   Sai dai duk da haka, ance garin ya sake haɓaka a wajajen karni na goma sha bakwai ta yadda fatake ke isa gareshi fatauci tun daga kano, lokacin ma garin maraɗi na karamin kauye, ko kuma ace sam bai kafu ba.
Ance Sarauniya Tahoua tayi mulkinta a birnin Lalle, ita kuwa itace sarauniya mace ta farko da aka yi a Gobir, kuma itace uwa ga waɗanda suka kafa Biranen konni dake cikin Jihar Tahoua a Jamhoriyar Nijar da kuma Argungu na jahar Kebbin Nijeriya.
   Sarki Kanni da Sarki Hammadin shine sunayen 'ya'yayen Sarauniya Tahwa, kuma sun tsira da rayukan sune bayan da suka gudu daga garin da dare, kamar yadda suka shawarta a tsakanin su.
  Dalilin hakan kuwa shine, an tilasta musu hawa kan gadon sarautar birnin ne alhali kuwa basu so.
   Kanni aka fara naɗawa sarki, dare nayi ya hau sirdi ya ɓace ba’a san inda ya dosa ba. Kashe gari aka naɗa kanin sa Hammadin, shima kuwa cikin dare ya bi ɗanuwan shi ya gudu.
  Ance Hammadin ya ɗan zauna tare da ɗan uwan shi Kanni a birnin Konni tsawon shekaru, daga bisani ya tashi bai sauka ba sai a Argungu.
  Mawakin gargajiya kuma masanin tarihi, Marigayi Alhaji Maidaji Sabon Birni ya faɗa a wani baiti cewar duk sa'ar da mahaifiyar Kanni da Hammadin watau Sarauniya Tahwa ta tuno yadda ta rasa 'ya'ayenta, sai ta dugunzuma cikin ɓacin rai, tace “Gobirawa haka kuka kai ni, bani ga Kanni, bani ga Hammadin?”
 Amma daga baya ance ta samu haɗuwa dasu bayan an gano mata inda suke. Shine ma akace an kaiwa Sarki Kanni matar shi mai ciki wadda ya gudu ya barta a Birnin Lalle, wasu masoyan sa kuma sukayi dandazo suka tafi gareshi domin zama tare dashi.
  Ance  Sarki Kanni da kanin sa Sarki Hammadi suna da tsagen Gobirawa guda shidda (6) a kuncinsu na tsagin hagu, da kuma guda bakwai (7) a tsagin dama,  amma da suka haihu sai suka yanke shawarar yiwa kowane ɗa  tsagu goma (10) a hagu da goma sha-biyu (12) a dama domin  bambamta su daga sauran 'yanuwansu Gobirawa.
      Game da Sarkin birnin Lalle Kutturu, wanda akan kira shi da suna Sarki Dalla Gungume, ya samu shiga cikin jerin sunayen da suka mulki wannan birni duk da kasancewar sa gungumen itace, watau sahun sarakuna irinsu Sarki Barankame, Sarki Kanni, Sarki Bartakeskes, Sarki Hammadin, Sarki Bartuwatuwa da wasunsu kimanin ɗari uku da tamanin (380).
  Asalin naɗa shi shine, ance akwai wani lokaci a baya, da husumar hawa mulkin Birnin Lalle tayi tsamari a tsakanin Gobirawa dake da iko da garin, ya zamana duk wanda aka ɗora sarki sai masu adawa dashi sunbi dare sun halaka shi komai tsarin sa, don haka sai dabarar sassaka gungumen itace a matsayin mutum-mutumi tare da sanya shi cikin ado gami da ɗora shi akan karagar mulki ya faɗo a zukatan manyan fadawan wannan masarauta.
 Bayan an yi bikin naɗin Sarki kututturu bisa karagar mulki, rannan sai waɗanda basu so suka sake yin yunkurin kawarda sarkin, kamar yadda suka saba yi ga duk wanda aka naɗa bisa wannan karaga, suka biyo dare ɗauke da makamai, amman sai suka tarar da Sarkin ɗangalgal bisa karagar shi.
    Da yake basu san shirin da akayi ba, sai kurum tunanin su ya basu cewa lallai wannan sarki hatsabibi ne, domin basu san adadin layu ko kahunan da ya tanada ba ta yadda ko gezau bai yiba a lokacin da suke fuskantar sa don su halaka shi, sai kurum suka rantaya da gudu.
  Tun daga nan kuma aka samu sauki, har kuma aka cigaba da naɗa mutane bisa mulkin Birnin Lalle.
   A ɗan lokacin da Sarki Kututturu yayi bisa mulki, waɗanda suka naɗa shine ke gudanar da harkokin mulki gami da zartar da duk wasu lamurori. Har ma an samu cewa idan mutane sunzo yin gaisuwar fada, sai fadawan su amsa da cewa “Sarki ya gaisheka”, don haka ake ganin watakila wannan ne mafarin irin wannan amshin gaisuwa a tsarin Shugabancin Hausawa.



Sunday, 15 April 2018

TARIHIN DAULAR KATSINA

TARIHIN DAULAR KATSINA

DAGA SADIQ TUKUR GWARZO

Maruwaitan tarihi sunyi ruwaya mabanbanta dangane da tarihin Katsina.
   Daya daga ciki itace mai cewa an kafa Daular Katsina ne a wajajen karni na goma sha uku, kuma wata zuria mai suna Ambutai ne suka fara mulkin birnin katsina a inda yake a yanzu,
  Wata ruwayar kuma tace Sunan sarkin Katsina na farko shine Kumayau, kuma shi jikan Bayajidda ne, ance shine wanda  ya kwace ikon masarautar Durɓi, daga nan ya haɗe masarautar tare da kafa cibiyar mulki a birnin Katsina.
  Wata ruwayar kuma ta tafi akan cewa Katsina ta kafu ne tun a shekarar 950 miladiyya, daga kabilar Nufawa wangarawa.
   Sai dai, watakila zance mafi inganci shine wanda maigirma Walin Katsina ya faɗa cewar asalin birnin Katsina karamin kauye ne, sai wata gimbiyar tsohon birnin Durɓi ta kusheyi mai suna Katsi ta gudo daga garin izuwa nan saboda wani dalili. Aka shiga nema ba'a gantaba, sai daga baya aka same ta a wannan ɗan kauye. Shine ake cewa Katsi-na-nan.. Daga nan sunan 'Katsina' ya samo asali har kuma a hankali cibiyar masarauta ta baro Durɓi izuwa nan, wanda yayi sanadin bunkasar garin.
  Dangane da tarihin asalin mutanen Durɓi, wasu sun tafi akan cewa asalinsu mutanen Mali ne masu fatauci suka kafa garin, yayin da wasu ke ganin dube da aiyukan maguzanci da suka auku a Durɓi, da bautar Magiro a Kwatarkwashi, sai ake ganin mutanen garin sunfi kamantuwa da zamowa jikoki ga mutanen tsohuwar daular 'Katsina Ala' data taɓa wanzuwa a ɗaukacin yankin.
   Kusan dukkan masu ruwaito tarihi sun yadda da cewa Kumayau shine wanda ya kafa Katsina tun farko, shine kuma shugabanta na farko, sai dai kuma akwai saɓani dangane da yadda tarihi ya nuna cewar a zamanin da ana zaɓen sarki a wannan masarauta.
  Wasu sun tafi akan cewar ta hanyar jifan mashi ake zama sarkin Katsina, watau duk wanda jifansa ya kerewa saura shine zai zama sarki.
  Yayin da wasu ke ganin ta hanyar kokawa ake zama sarkin Katsina, watau wanda ya kayar da wani shine sarki.
    Ance anyi sarakuna masu suna Ramba, Taryau, da Jatinnati a iya tsawon shekaru kimanin ɗari bayan kafuwar Katsina,  sannan Muhammadu Korau yazo daga wani gari mai suna 'Yandoto yaci nasara a gasar zamowa sarki.
  Wasu sunyi maganganu akan cewar sai da Korau ya haɗa kai da matar sarki Sanau tare da karya asirin sa sannan yaci galaba a gasar da aka shirya musu ta kokawa don zamowa sarki. Daga baya ya samu nasarar kayar da Sarki Sanau tare da  yanka shi da wata wuka mai suna 'Gajere', sannan kuma ya halaka matar tasa.
Wasu kuma na ganin sa'a kurum ya samu akansa.
   Ana ganin Sarki Muhammadu Korau yayi mulki ne a wajajen shekara ta 1445 miladiyya zuwa 1495, amma dai ana ganin shine sarki Musulmi na farko a daular Katsina, sannan shine sarkin daya mayar da cibiyarsa izuwa birnin katsina na yanzu da zama, haka kuma a zamanin mulkin sane shahararren malamin addinin musulunci mai suna Muhammad Abdulkarim al-maghili yazo birnin katsina tare da soma  karantaswa. A lokacin ne kuma aka gina tsangayu da masallatai manya, ciki kuwa harda hasumiyar Gobarau wadda har yau tananan cikin birnin katsina.
  Ance sarki Maje shine ya ɗora akan inda sarki Korau ya tsaya ta fannin yiwa addinin musulunci hidima. Ya wanzar da shari'ar musulunci, ya zama mai umarni da yin sallah akan kari, tare da tursasawa tuzurai yin aure.
 A shekarar 1513 akace Sarkin Songhai Muhammadu Askiya ya aiko dakaru kasar Hausa, har suka karɓe ikon Katsina.
   Ance a wajajen shekarar 1554 Katsinawa suka 'yantar da kansu daga masarautar Songhai, sannan a wajajen shekara ta 1570, suka samu nasarar yaki akan masarautar Kano, wadda take hamayya dasu a wancan lokaci. Amma babu jimawa sai akace daular Borno ta samu iko da ita na tsawon wani lokaci.
    Zuwa karshen karni na goma sha shidda birnin katsina ya zama cibiyar karantarwar addinin musulunci kwatankwacin Timbuktu, musamman saboda cikar garin da manyan malumma masu karantarwa.
 Daga cikin malaman akwai Muhammed Bin Masani al Barwani al Katsinawi (Dan Masani) wanda akace asalinsa daga Borno yake. Da kuma  Muhammad al-Katsinawi Ibn Sabbag (Dan Marina). Sai kuma Muhammad al-Fulani al Katsinawi.
  Shi Muhammad al Fulani shashararre ne a fagen ilimai na addini dana kimiyya dana falsafanci.  Ance bayan ya koyi karatu a katsina sai ya ɗauki haramar tafiya Makkah don yin aikin Hajji. Akan hanyarsa ta komowa ya sauka a Cairo yana karantarwa, har kuma ajali ya riskeshi a shekarar 1734. Amma an samu cewar yayi wallafe-wallafe na ilimi da dama, aciki har da wani littafi mai suna ‘al-Durr al-Manzum wa Khulasat al Sirr al Maktum fi Ilmi al-talasim wal Nujum’.
  Zuwa karshen karni na goma sha takwas aka samu cewar adawa gagaruma ta shiga tsakanin daular katsina da masarautar Gobir. Ance rigimar ta samo asali ne a lokacin da dakarun Gobir suka karɓe iko da birnin Maraɗi, daga nan suka fara turawa izuwa  Birnin Katsina.
  Sarkin Katsina na lokacin mai suna Agwaragi (1778-1799) ya tara rundunar mayaka domin yakar Gobirawa, amma cikin rashin nasara Gobirawa suka yiwa dakarunsa sukuwar sallah tare da tarwatsa su.
  Tun daga nan sai rikici ya cigaba tsakanin masarautun biyu, ya zamana ana gwabzawa lokaci bayan lokaci, har izuwa zamanin Sarkin Gobir Yakubu (1788 – 1795) wanda akace ya halaka wani shahararren makeri Bakatsine tare da kai farmaki garin Ruma wanda yake cikin kasar Katsina.
Daga karshe dai katsinawa suka gwabza da Gobirawa tare da halaka sarkin su Yakubu, suka sare wuyansa, suka tafi da kansa birnin katsina.
 Ance tun daga nan yaki ya kare tsakanin su.
  Haka nan masarautar Katsina ta rinka faɗaɗa a hankali, inda ta zamo giwa mai makwabtaka da masarautar kano a Gabas, Zaria a kudu, Zamfara a yamma, Daura da Damagaran a ɓangaren arewa maso gabashi.
  Manyan biranen tsohuwar masarautar katsina sune:- ‘Yandoto, Gozaki, Maska, Tasawa, Gazawa, Ingawa, Matazu, Ruma, Kwatarkwashi, Birnin Bakane, Karofi, Maraɗi, Gwiwa, Kanen Bakashe, da suransu.