Tarihin Birnin Lalle da sarkin mutum-mutumi, MAI SUNA Sarki Kututturu.
Sadiq tukur gwarzo, rn.
Daga abinda marubuci Dan Zubairu ya ruwaito, masarautar Birnin Lalle dake can a yankin Dakoro na Jahar Maraɗin Jamhuriyar Nijar, shahararra ce wadda ambatonta ba zai yanke ba.
Kasancewar Birnin Lalle ɗaya ne daga tsoffin cibiyoyi ga Masarautar Gobir, ana ganin Gobirawa ne suka kafa garin. Amma kuma akwai alamu dake nuna cewar tun da jimawa Birnin Lalle ya kafu, kawai dai gobirawa sun shigo cikinsa ne tare da kwace ikon sa.
Birnin ya samo sunansa ne daga yawaitan bishiyoyin Lalle (wanda mata ke kunshi da kuma wanka dashi a baya) dake cikinsa.
Birnin lalle shine birni na gaba da Gobirawa suka sauka tun bayan barowarsu daga Birnin Marandat da Birnin Toro. Da yake daman ance asalinsu daga Baghaza suke, suka shiga duniya, har kuma a hankali suka rinka sauka a garuruwa suna auratayya da yake-yake.. A haka har suka riski birnin Lalle.
Masu cewa gobirawa ne suka kafa wannan birni na Lalle ɗaruruwan shekaru da suka gabata, sun faɗi cewar Gobirawa sun riski wajen ne yana fili sa'ar da suke neman gulbi ko tabki a wannan yanki domin su rinka gudanar da ayukkansu na noma, kasancewarsu daman bayan yake-yake, sukan jarraba noma tun tale-tale.
Don haka ake ganin da isowar su bakin tabkin sai suka ga bishiyoyin Lalle burjik a zagaye dashi, shine sai suka baiwa wurin suna da cewa “Wannan wuri Birnin lalle kenan!”. Daga nan kuma suka yanke shawarar zama acikin sa.
Amma dai wasu masanan tarihi sun tafi akan cewa Birnin lalle ya kafu ne tun kimanin shekaru 2000 da suka gabata. Sai dai kuma babu takamaimen sunan kabila ko mutanen da suka birnin.
Haka kuma, ana ganin garin ya tumbatsa matuka a wani lokaci can a baya, amma ɓarkewar yunwa a wannan birni ce tayi sanadiyyar da Gobirawan suka tashi daga gareshi izuwa birnin Alkalawa dake tsohuwar masarautar Zamfara (wajajen karni na goma sha shidda).
Sai dai duk da haka, ance garin ya sake haɓaka a wajajen karni na goma sha bakwai ta yadda fatake ke isa gareshi fatauci tun daga kano, lokacin ma garin maraɗi na karamin kauye, ko kuma ace sam bai kafu ba.
Ance Sarauniya Tahoua tayi mulkinta a birnin Lalle, ita kuwa itace sarauniya mace ta farko da aka yi a Gobir, kuma itace uwa ga waɗanda suka kafa Biranen konni dake cikin Jihar Tahoua a Jamhoriyar Nijar da kuma Argungu na jahar Kebbin Nijeriya.
Sarki Kanni da Sarki Hammadin shine sunayen 'ya'yayen Sarauniya Tahwa, kuma sun tsira da rayukan sune bayan da suka gudu daga garin da dare, kamar yadda suka shawarta a tsakanin su.
Dalilin hakan kuwa shine, an tilasta musu hawa kan gadon sarautar birnin ne alhali kuwa basu so.
Kanni aka fara naɗawa sarki, dare nayi ya hau sirdi ya ɓace ba’a san inda ya dosa ba. Kashe gari aka naɗa kanin sa Hammadin, shima kuwa cikin dare ya bi ɗanuwan shi ya gudu.
Ance Hammadin ya ɗan zauna tare da ɗan uwan shi Kanni a birnin Konni tsawon shekaru, daga bisani ya tashi bai sauka ba sai a Argungu.
Mawakin gargajiya kuma masanin tarihi, Marigayi Alhaji Maidaji Sabon Birni ya faɗa a wani baiti cewar duk sa'ar da mahaifiyar Kanni da Hammadin watau Sarauniya Tahwa ta tuno yadda ta rasa 'ya'ayenta, sai ta dugunzuma cikin ɓacin rai, tace “Gobirawa haka kuka kai ni, bani ga Kanni, bani ga Hammadin?”
Amma daga baya ance ta samu haɗuwa dasu bayan an gano mata inda suke. Shine ma akace an kaiwa Sarki Kanni matar shi mai ciki wadda ya gudu ya barta a Birnin Lalle, wasu masoyan sa kuma sukayi dandazo suka tafi gareshi domin zama tare dashi.
Ance Sarki Kanni da kanin sa Sarki Hammadi suna da tsagen Gobirawa guda shidda (6) a kuncinsu na tsagin hagu, da kuma guda bakwai (7) a tsagin dama, amma da suka haihu sai suka yanke shawarar yiwa kowane ɗa tsagu goma (10) a hagu da goma sha-biyu (12) a dama domin bambamta su daga sauran 'yanuwansu Gobirawa.
Game da Sarkin birnin Lalle Kutturu, wanda akan kira shi da suna Sarki Dalla Gungume, ya samu shiga cikin jerin sunayen da suka mulki wannan birni duk da kasancewar sa gungumen itace, watau sahun sarakuna irinsu Sarki Barankame, Sarki Kanni, Sarki Bartakeskes, Sarki Hammadin, Sarki Bartuwatuwa da wasunsu kimanin ɗari uku da tamanin (380).
Asalin naɗa shi shine, ance akwai wani lokaci a baya, da husumar hawa mulkin Birnin Lalle tayi tsamari a tsakanin Gobirawa dake da iko da garin, ya zamana duk wanda aka ɗora sarki sai masu adawa dashi sunbi dare sun halaka shi komai tsarin sa, don haka sai dabarar sassaka gungumen itace a matsayin mutum-mutumi tare da sanya shi cikin ado gami da ɗora shi akan karagar mulki ya faɗo a zukatan manyan fadawan wannan masarauta.
Bayan an yi bikin naɗin Sarki kututturu bisa karagar mulki, rannan sai waɗanda basu so suka sake yin yunkurin kawarda sarkin, kamar yadda suka saba yi ga duk wanda aka naɗa bisa wannan karaga, suka biyo dare ɗauke da makamai, amman sai suka tarar da Sarkin ɗangalgal bisa karagar shi.
Da yake basu san shirin da akayi ba, sai kurum tunanin su ya basu cewa lallai wannan sarki hatsabibi ne, domin basu san adadin layu ko kahunan da ya tanada ba ta yadda ko gezau bai yiba a lokacin da suke fuskantar sa don su halaka shi, sai kurum suka rantaya da gudu.
Tun daga nan kuma aka samu sauki, har kuma aka cigaba da naɗa mutane bisa mulkin Birnin Lalle.
A ɗan lokacin da Sarki Kututturu yayi bisa mulki, waɗanda suka naɗa shine ke gudanar da harkokin mulki gami da zartar da duk wasu lamurori. Har ma an samu cewa idan mutane sunzo yin gaisuwar fada, sai fadawan su amsa da cewa “Sarki ya gaisheka”, don haka ake ganin watakila wannan ne mafarin irin wannan amshin gaisuwa a tsarin Shugabancin Hausawa.

No comments:
Post a Comment