Tuesday, 1 May 2018

TARIHIN KABILAR BABUR DAYADDA DABIUNSU NA AURE SUKE

BABUR MARRIAGE CULTURE AND RITUALS

TARIHIN KABILAR BABUR DA AL'ADUNTA NA AURATAYYA

DAGA SADIQ TUKUR GWARZO, RN

Kabilar Babur tana danganta asalinta ne da Mutanen Yamen, don haka aka ruwaito cewa rundunar wasu mutane ne sukaƴi hijira daga Yemen a wajajen shekara ta 600 miladiyya suka riski Kasar Sudan, sannan suka shigo cikin sahara tare da sauka a yankin da Kabilar Babur ke rayuwa a yanzu cikin kasar Borno.
   Ba iya kabilar Babur ba, har kabilun Kanuri da Luguda da wasunsu dake rayuwa a wannan yankin suna ikirarin asalin kakanninsu daga Yemen suke. Gusawar zamani ne kurum ya sanya takamaimen tarihinsu ya sauya.
   Zuwa yanzu dai, ana samun kabilar Babur ne a Jihohin Borno da Adamawa.
  A jihar Borno, akwai kabilar Babur a garuruwan Biu, Hawul, Kwaya kusar, Shani, Kwajaffa, Sakwa, Marama, Shaffa, Wandali, Kida, Miringa, Buratai, Zuwa, Yimirshika ,Hyera ,Dayar, Fumwa, Azare, Gwaski, Diragina, Yimana, Gwallam, Tiraku, Shindiffu, Goski, Pela Birni, Wangdang, Bula tawewe, Kogu Tashan Alade, Kida, da hang shang  da kuma Bayo, amma a jihar Adamawa kabilar Babur sunfi yawa a garin Garkida cikin karamar hukumar Gombi.
  Dukkan waɗannan garuruwa da Kabilar Babur ke zaune ciki nada nasu tarihin.
  Misali, ance jarumin daya kafa daular mulki ta Biyu mai suna Yamta, ɗane ga wata mace 'yar kabilar Mandara.
  Wai Tun tana da cikinsa aka ɗauke ta zuwa gidan Sarkin Borno, don haka acan aka haifeshi kuma acan ya taso da tarbiyar kanuri.
  Amma da Yamta ya girma, sai ya tumbatsa wajen jarumta. Shine fa harbya karɓe ikon yankin da Biu take ayau tare da kafa masarauta.
   Ana ganin ya fara kafa mazaunin masarautar sane a wani wuri mai suna 'Limbur' tsakanin chikorkur da Mandagarau. Har zuwa yanzu kuma ance kabarinsa yana nan a Limbur ɗin.
  Kabilar Babur, sune keda rinjaye a garin Biu da wasu garuruwan makwabta, amma akwai kuma kabilar Bura wadda ke zaune a makwabciyar kasar Babur ɗin, mai suna 'Babur Bura'. Dukkansu kusan da yare ɗaya suke amfani, kuma yaren yana da kamanceceniya dana garuruwan Chibok, Marghi, Higgi , Kilba and Bazza.
 Anfi samun kabilar 'Babur Bura' a jihohin gabashin Nigeria, watau Borno, Adamawa, Gombe da Yobe.
  AL'ADUN AURE
Mafi yawan kabilun Borno musamman Kanuri, Shuwa Arab da Babur nada kamanceceniya wajen al'adun auratayya. Watakila hakan ya faru ne saboda jimawar kabilun wajen zaman tare ko kuma ana iya cewa kakanninsu ne ɗaya, don haka daga garesu sukayo gadon ɗabi'un.
  Bisa al'ada ta Kabilar Babir, Idan namiji yaga mace yana so, to bazai sanar mata ba, sai dai ya nemeta da abota.
  A wannan abotar ne zai rinka bincikar halayyarta dana magabatanta, ba tare da ta sani ba, daga bisani kuma sai ya samu wani dattijo a danginsa ya ɗora masa alhakin kammala masa bincike akan yarinyar da zuriyarta duka.
  Daga wannan matakin kuma sai mai neman auren ya zaɓi maza uku da mata biyu akalla, daga danginsa su rakashi gidan su yarinya.
   Anan ne zasu haɗu da iyayenta ko 'yanuwanta, har kuma a tambayeta abinda ke tsakaninsu da wannan mai neman auren nata, da kuma muradinta akansa da sauransu.
  Idan an aminta a kulla auratayya, to daga nan ne za'a sanya ranar yin Baye, suna kiranta 'Yuyma'.
  Idan ranar tazo, dangi zasu haɗu daga ɓangaren namiji da mace maza da mata a gabatar da kayan ci dana sha, sanna a sanya ranar aure, watau “Mbwa Nyika”.
  Dangane da batun kuɗin aure ko sadaki, namiji na iya bayar da dukkan abinda ya samu gareshi ga iyayen wadda yake so ya aura, sukuma zasu ciri wani abu kaɗan su mayar masa da ragowar, (wasu ma ance basa cirar kome), to amma za'a gabatar masa da sunayen wasu abubuwa da akeso ya siya mata.
  A hakan ma, ba dole bane ya siyi dukkan komai ba, kawai dai yana iya zaɓar abinda yake da iko ne ya siya.
  Idan namiji ya haɗa kayan, sai ya tashi yan uwansa su tafi sukai gidan su yarinya. Daga nan kuma za'a saurarar ranar ɗaura aure.
  Daura aure kuwa ya danganta da addinin da mutum yakebi, kasancewar addini yayi tasiri cikin kabilar Babur, don haka kiristocin cikinsu sukanje chochi ne domin ɗaura aure, yayin da musulman cikinsu kan ɗaura aure a Masallatai ko gidaje, tare da aiwatar da al'adun aure kalar wanda musulunci ya halatta

No comments:

Post a Comment