Tuesday, 10 July 2018

TARIHIN KARAYE

TARIHIN KARAYE

Daga Sadiq Tukur Gwarzo
  08060869978

Littafin 'Ƙaraye Maƙarar Maganar Kano' da Alh Shehu Garba Ƙaraye da kuma Umar Ƙaraye suka wallafa ya kawo manyan muhimman batutuwa na tarihi da suka faru a Ƙaraye.
   Daga ciki, sunyi maganar Wanzuwar garin ƙaraye tun kafin soma sarautar Bagauda a Kano, a shekara ta 999 miladiyya.
   Littafin ya tafi akan cewa tun da jimawa, akwai maguzawa da suke zaune a garin ƙaraye, waɗanda suke bautawa bishiyoyin kukoki da kuma na Rimaye.
  Daga Rimayen da aka samu ana yiwa bauta don samun tagomashi akwai Rimin yaki-yaki, Rimin Kwatankwaro, Rimin tagwaye, da Rimin kofar Zango. Sai dai littafin bai faɗi asalin daga inda waɗannan mutane maguzawa suka zo ba.
   Dangane da sunan wannan gari na Ƙaraye kuwa, a wani wuri littafin ya faɗi cewa Sunan shugaban Maguzawan farko a garin shine Ƙaraye, don haka ake kiran garin da sunansa.
Amma kuma a wani wuri na daban, littafin ya sake kawo cewar sunan ƙaraye ya zone daga yawaitar Ƙaro dake wata bishiya a tsakiyar garin.
     Garin ya soma kafuwa ne a arewa da inda yake a yanzu, kuma anan ya wanzu tsawon lokaci har bayan jihadin fulani, sannan ya dawo inda yake da zama yanzu. Koda yake, har yanzu ana kiran wancan gari da suna tsohuwar ƙaraye, domin akwai mutane zaune acikinsa. Kuma akwai alamu masu nuni da tsufan gari da kai tsaye akan iya lura da zarar an shiga cikinsa.
   Ana ganin Ƙaraye ta girmama, kuma ta shahara a zamanin baya, ta yadda faɗaɗar ta ya tuƙe da ƙasashen Katsina, Zaria da kuma kano, kafin daga bisani a kacaccala ta.
Haka kuma tayi tashen sadaukantaka da ƙarfi wurin yaƙi, tayadda tun sa'ar da ta ƙulla alaƙar zumunta da kano, ba'a taɓa samun wata rundunar mayaƙa data shigo Kano daga yamma don kawo hari ba, domin tun kafin isowarta Ƙaraye zata tarbeta tare da tabbatar da cewar tayi nasara akanta. Wannan shine asalin kiran ƙaraye da suna 'ƙyauren yamma da birni'.
   Tsoffin garuruwan yammacin kano da sukayi tarayya da ƙaraye a tsawon zamunna da suka shuɗe sune Baɗari, Goɗiya, Yalwan ɗan ziyal da kuma shanono, sai kuma Getso, da Ƙwanyawa, da Gwarzo daga baya, da wasu makamantansu.
Waɗannan garuruwa na fsrko suna da tambura da ake ƙaɗawa sarakunansu, wanda ke nuna bunƙasar sarautarsu da kuma haɓakar garueuwan nasu.
   Garin Ƙwanyawa na can yamma da Ƙaraye, kuma ya haɓaka ta yadda har akwai ganuwa kewaye dashi . An samu cewa awancan zamanin, dukkan garuruwan dake kewayen, basu da wurin fakewa idan an kawo harin yaƙi sama da Ƙwanyawa ko Ƙaraye. Da zarar sun shige birni aka ɓame ƙofa tofa sunsha, sai dai kaga sadaukai na hawa saman ganuwa suna harbo kibbau ga abokan gaba.
   Wata rawa gagaruma da ƙaraye ta taka itace lokacin yaƙin Jihadin fulani don tsarkake addinin musulunci a kano. A wannan zamani, ƙaraye ta fafata da dakarun masu jihadi aƙalla sau uku, kuma ta samu nasara akansu sau biyu.
Kashi na farko shine a lokacin da masu jihadi suka yaƙi Goɗiya, sai suka gangaro yamma da nufin barin ƙasar kano izuwa ƙasar Ghana.
   Karo na biyu kuwa shine a lokacin da masu jihadi suka dawo kano, sai suka riski dakaru sun haɗu ana saurarensu a ƙaraye, suka fafata dasu amma basu samu nasara ba.
    Sai da taimakon Allah masu jihadi suka karya lagon ƙaraye gami da ƙwace garin a karo na ƙarshe da suka buga.
   Ance a zamanin Sarkin Kano Sulaimanu ne aka ɗaga darajar Shugabancin ƙaraye izuwa darajar Sarki, saboda kasancewar wanda aka naɗa ya shugabanceta mai suna Mallam Adamu Kwasanlo, bafulani ne basulluɓe, wanda ya taka rawa a yaƙin jihadi. Don haka akace masa darajar sarautarsa ta sarki ce, yadda a gaba ba zaizo ya shiga sahun masu neman sarautar kano ba.
A yanzu haka, karaye ƙaramar hukuma ce a jihar kano. Kuma har yau sarkin yanka gareta, amma dai yana a matsayin Hakimi ne na mai martaba Sarkin Kano.
(Kaɗan daga tarihin ƙaraye kenan. Mai son jin ƙsri sai ya nemi littafin 'Ƙaraye Maƙarar Maganar Kano').

TARIHIN BIRNIN RANO

 TARIHIN BIRNIN RANO

Daga Sadiq Tukur Gwarzo
08060869978

Saɓanin abinda Marigayi Maje Ahmad Gwangwazo ya kawo a littafinsa 'Tarihin Kano kafin Jihadi' cewa asalin garin Rano daga wani mai suna Ranau ne da yazo ƙasar Hausa daga ƙasar Habasha tare da ƴanuwansa Maguzawa masu suna Gayya da Dala tun kafin haihuwar Annabi Isa A.S, bayani daga Rano ya kawo wata mahangar wadda ta saɓawa haka.
        A littafin da Maigirma Barayan Kano Hakimin Bunkure Tafida Abubakar Ila ya wallafa mai suna Tarihin Rano, ya kawo cewa ƙabilar Kwararrafawa da suka zo daga Kwararrafa ta cikin ƙasar Riruwai sune asalin kafa Rano.
   A cewarsa waɗannan ƙabila mafarauta ne, kuma wasu daga cikinsu ne suka baro garinsu tare da riskar yankin da Rano take ayau, suka ganshi cike da albarkatu da tsaunika, don haka sai suka yanke shawarar zama akan duwatsun suna noma da kiwo.
     Basaraken ya faɗa cewar Asalin sunan Rano yazo ne daga wani sarkin Rano mai suna Ranau, wanda wata rana aka kawo yaƙi ƙasar sa har kuma aka hallaka shi a wajen yaƙi, aka binne shi a gefen wani dutse mai suna Tajika.
   Yace kasancewar akwai ƙorama da mutane ke zuwa domin samo ruwan sha, sai mutane ke cewa mun tafi gurin Rauno ɗebo ruwa, daga baya aka koma kiran yankin da suna Rano.
     Waɗannan Kwararrafawa sun jima suna mulkin Rano a tsakaninsu, sun zauna da fadojinsu akan waɗannan manyan tsaunika na Rano misalin Dutsen Damishi, dutsen Kurgun da dutsen Mairama, kuma har yanzu akwai sawun wanzuwarsu a wurare mabanbanta, misalin wasu mashigai da sawun gine-ginen duwatsu da koguna masu duhu da aka samu wsɗanda akace mutanen sukan ɓoye acikinsu idan an kawo musu hari, waɗanda kuna zuwa yanzu sai jarumin gaske ne kaɗai zai iya cusa kansa ciki, daga baya sai Hausawan Haɓe suka zo suka ƙwace mulkin yankin baki ɗaya.
Dangane da sarkin farko a zuriyar Haɓe daya fara mulkin Rano, kusan dukkanin maruwaita sun haɗu akan cewa Autan Bawo, ƙani ga Sarkin Kano Bagauda, kuma jikan Bayajidda shine ya soma mulkin Rano. Sai dai akwai saɓani akan ainihin sunansa da kuma dalilin zuwansa Rano.
Barayan Kano ya faɗa a littafinsa cewar Zamna Kogo shine sunan Sarkin Rano na farko da Haɓe suka ɗora. Kuma ya nuna kamar yaƙi ne Haɓe suka kawo Rano har suka cita da yaƙi gami da ɗora nasu a mulki a wajajen shekara ta 1082 miladiyya.
 Amma Maje Ahmad Gwangwazo ya tafi akan cewa Hamza Zimango ne sunan wannan sarki, kuma shi ƙani ne ga Bagauda sarkin Kano na farko.
 A cewarsa Zimango yazo ne daga Daura da iyalansa, ya sauka a wurin yayansa Bagauda, har kuma yayan nasa ya labarta masa dabarun da yabi ya zamo sarkin Kano, watau ta hanyar Jarumtarsa da kuma alƙalanci na adalci daya rinƙa yi tsakanin mutanen Kano, sai shima Zimango ya tashi daga Kano yayi kudu, har ya riski Rano, anan ya zauna tare da maguzawan yankin, har kuma daga baya suka naɗa shi sarkin su.
Don haka, Rano ta shahara da mayaƙa gami da ɗaukaka gagaruma a zamanin baya, kuma ko a lokacin Jihadi, itace ƙasa ta ƙarshe da Fulani suka ci da yaƙi a zamanin Sarkin Kano Sulaimanu, lokacin da Sarki Alwali ya gudu daga Kano sai ya zauna a Rano sannan ya tafi Zariya, bayan shekara ɗaya ya baro Zariya ya sauka a Rano, ya wuce burum burum, kafin daga bisani rundunar mayaƙan fulani ta kawo musu yaƙi wanda yayi sanadiyyar mutuwar shi kansa Sarki Alwalin da kuma Sarkin Rano Jatau na lokacin. Suka naɗa sarki Dikko bafulani na farko a tarihi..

Thursday, 5 July 2018

TARIHIN TSOHON BIRNI AUYO

Tarihin Tsohon birni 'auyo'.
                                       Daga
Sadiq Tukur Gwarzo
Da
 Gaddafi Hussain Auyo



  Garin Auyo tsohon gari ne, domin kuwa tarihi ya bayyana mana  cewa Auyo na ɗaya daga cikin tsoffin birane kuma mashahurai a wannan kasa waɗanda sukayi sharafi har kuma ya zamo suna cin gashin kansu tun tsawon zamani daya gabata.
  Haka Kuma birnin Auyo ya jima yana ɗauke da tsarin masarauta wadda sarakuna ke tafiyarwa cikin ka'idoji gami da lura.
    Dangane da daɗewar Auyo, tarihi ya bayyana mana cewa ko lokacin da fir'auna Remesis II na zamanin Annabi Musa (A.S) yayi yekuwa tare da gangami daga manyan birane yana mai neman waɗanda suka kware akan sihiri da surkulle, a wannan karawar da tarihi ya ruwaito Firaunan yayi da Annabi Musa A.S, an samu cewa tabbas akwai matune a Auyo, har kuma wasu shahararru akan sihiri daga kasar Auyo sun halarci wancan taron tare  kuma da jarraba tsibbace-tsibbacen su a wurin, amma daga bisani da Annabin Allah Musa yayi galaba akan ɗaukacin Masihirtan, ance suna cikin waɗanda suka gaskata Annabi Musa (A.S) kuma sukayi masa mubayi'a.
    Har ila yau, akwai zance na gaskiya mai nuna cewar lokacin da tawagar wakilai daga  kasar Borno a zamanin wani Sarkinsu da ake kira 'Maidinama' suka tafi birnin Madina  domin su karɓo addinin musulunci a wajen Shugaba, Manzon Allah (s.a.w) har kuma suka tarar Manzon Allah yayi wafati sai Sayyadina Abubakar R.A ne ke Halifanci, har da mutanen Auyo acikin tawagar.
  A wancan lokacin ance shima Sayyidina Abubakar ɗin yana fama da yakuna, don haka yace su zauna kafin a samu natsuwa, har kuma Allah ya karɓi rayuwar sa. Amma da fara Halifancin Sayyidina Umar R.A sai ya taso da maganar, ya haɗo rundunar sahabbai da littattafai suka taho Borno..
 Kasar Auyo ta kasance mai  daɗaɗɗen tarihi, domin kuwa anyi imanin cewa duk wasu garuruwa da ake alakantawa da hausa bakwai ko banza bakwai, to kuwa Auyo ta girme su.. A ciki harda Daura, domin dai abisa kiyasi na bincike an gano cewa Auyo tafi shekara dubu biyar da kafuwa.
   Ance wani mutum mai suna 'Auya' shine ya kafa garin na Auyo, don haka daga sunan sane aka samo kalmar 'Auyo', kuma shi ɗan kabilar 'Bagirmine' waɗanda akace tun da jimawa suna zaune a arewaccin kasar Sudan.
       Kasar Auyo tana da mashahuran malamai masanan addinin musulunci. Tarihi ya bayyana mana cewa daga cikin malaman da sukayi fice a kasar kano akwai da yawansu waɗanda asalinsu Auyakawane.
  Garin Auyo yana ɗaya daga cikin garuruwan da anan baya-baya aka haɗe aka samar da masarautar Hadejia. Amma wannan gari sam ba koma baya bane acikin tarihin kasar Hadejia, kasancewarsa tsohon gari wanda ya daɗe da wanzuwa zamuna masu tsawo da suka shuɗe, gashi kuma sanan-nan gari daya tattara mutane masu baiwa iri daban-daban kama daga dakaru da baraden yaki zuwa uwa uba  malamai mahardata alqur'ani mai girma.
   Auyo ta jima ɗauke da masana masu ilimin taurari dana bugun kasa da masu lakkuna da sauran iliman asararu na tsaron kai da tsaron kasa, haka ma suna da mutane wadanda suka shahara  wajen sihiri da surkulle irin na wancan lokacin. Don haka muna iya cewa ita tunjimin gari ne wanda kome mutum yaje nema yana iya samu..
   

HIKAYAR WANI SARKIN HINDU DA ƊIYARSA HARIBAI

HIKAYAR ƊIYAR SARKIN DAULAR PITUGAR DAKE HINDU
SADIQ TUKUR GWARZO
A wani lokaci mai tsayi daya gabata a Hindu, anyi wani sarki a daular Pitugar mai jiji-da-kai. Sunansa Dheema.
  Sarkin yana da ƴaƴaye ƴammata guda biyu, dukkansu kyawawa ne. Ɗaya ta faye yawan surutu, gata da halin ko-in-kula, sunanta Kalimbai. Ɗayar kuwa sunan ta Haribai, kuma ita mai shiru-shiru ce da natsuwa.
   Da lokacin aurensu yayi, sai wani hamshaƙin attajiri ya fito neman auren babbar cikinsu watau Kalimbai, ai kuwa sarki ya bashi aurenta. Akayi gagarumin biki na ƙawa, duk gari kowa sai labari yake saboda kece raini da akayi a wannan biki.
  Bayan biki ya ƙare, sai Sarki Dheema ya lura da kaɗaicin da ɗiyarsa Haribai take fama dashi tun bayan auren yayarta Kalimbai, don haka sai yakan ware lokaci yana zuwa ɗakinta suna firar duniya da ita.
   Rannan sarki ya shiga ɗakin Haribai suna taɗi kamar yadda suka saba, sai idanuwansa yakai ga wani fai-fai a ɗakin mai ɗauke da rubutu kamar haka: "Duk gidan da mace mai hikima take a cikinsa, a koda yaushe zai rinƙa bunƙasa"
"Wanene ya sanar dake wannan zance?" Sarki Dheema ya faɗa yana mai nuni da rubutun dake jikin fai-fan.
 "Babu wanda ya sanar dani, amma da kaina nayi imani da hakan" Haribai ta bashi amsa.
 Sarki Dheema yayi murmushin yaƙe saboda yadda zuciyarsa ta sosu daga wannan magana.
Yace "kinga, ni Sarki ne, kuma kasancewata a gidan nan shine yasa komai da komai yake bunƙasa acikinsa. Don me zakice sai gida na ɗauke da mace mai hikima zai bunƙasa?"
  Haribai tace "Baba, magana ta fa haka take. Bunƙasar gidan nan ta dogara ne ga Hikimar mahaifiyar mu"
  Sarki ya fusata, ya daka mata tsawa yana muzurai, yace sam ba haka wannan zance yake ba. Amma Haribai ta dage kai-da-fata cewar hikimar mahaifiyarsu a wannan gida ne sanadin haɓaka da albarkar gidan baki ɗaya.
  A ƙarshe Sarki ya tashi ya fice daga ɗakin, yana tunanin hanyar da zai ladabtar da wannan ɗiya tasa, har ta gane cewa tayi laifi babba.
  Akan haka ya ƙudurce cewa shine zai lalubo mata ƙasƙantaccen mutum ya haɗata aure dashi.
  Cikin wannan mako Sarki Dheema ya lalubo wani mutum mai sana'ar saran itatuwa da faskarawa mai suna Nandu, yace masa "Kai Nandu! Zan aura maka ɗiyata Haribai"
  Nandu yace "Ranka ya daɗe ni talaka ne, sam-sam ba zan iya ɗaukar ɗawainiyar rayuwar jindaɗin da ɗiyarka zata iya buƙata daga gareni ba. Don haka bani iyawa".
  Sarki Dheema yace "aikuwa zaɓi biyu gareka, kodai ka auri Haribai ko kuma nasa a datse min kanka"
  Ba shiri Nandu yace ya yarda da wannan aure.
  Duk da irin dagewar da waziran Sarki gami da iyalansa sukayi akan hana wannan aure, amma ya kafe sai da akayi.
 Haribai kuwa bata taɓa ɗaga kanta akan lamarin ba.
 Akayi biki babu armashi, ta tafi tarewa a wani ruɓaɓɓen gida da mijinta Nandu ke rayuwa aciki nesa da gari.
  A kullum da garin Allah ya waye, Nandu zai ɗauki gatarinsa ya tafi daji sana'arsa ta saran itace. Acan ne zai wuni aiki, sai da marece  zai siyo kayan abinci da ɗan abinda ya samo, sannan ya kaɗo kansa gida abinsa, ita kuwa matarsa ta sarrafa abinda ya kawo ɗin zuwa abinci.
 Sai Haribai ta lura da cewa tana wuni bata aikin komai a gida har sai mijinta ya kawo kayan abinci da yamma take aiki. Don haka rannan sai ta shaida masa cewar "ina ganin, daga yau, ka rinƙa raba ƙuɗin da kake samowa zuwa gida uku, kashi biyu ka siyo mana abinci wanda zamuci sau biyu a rana, kashi ɗayan kuwa mu rinƙa tara shi, idan yayi yawa sai mu ƙaro sabon gatari.. Inaso na rinƙa binka daji aiki."
 Abinda ya faru kenan, babu jimawa kuɗin siyan gatari ya taru. Suka siya suna zuwa daji saro itace tare. Ya zamana ƙuɗin da suke samu a wannan aiki da wanda suke ajiyewa tari duk sun ƙaru.
 Jimawa kaɗan kuma sai Harimbai ta sake samun wata dabarar. Ta sanar da mijinta cewar ta lura da cewar maƙwabciyarsu nada dutsen tishi da ake niƙa alkama izuwa fulawa, don haka tana ganin ya kamata su siyo shi domin ƙara haɓaka hanyar samar da kuɗinsu.
 Nandu yayi murna matuka da haka, yace "duk yadda kikace haka za'ayi". Ya ɗauki kuɗin da suka tara ya nufi kasuwa. Bai dawo ba sai da ƙaramin dutsen tishi na dai-dai kuɗinsu.
  Sannu a hankali ya zamana suna iya samar da kuɗin da zasu iya warware matsalolin gabansu.
 Ita Haribai a iya niƙan data keyi tana samar da abinda zasuci a kullum. Don haka duk kuɗin da Nandu zai kawo gida ajiyewa kurum akeyi.
Daga baya sai Nandu ya ware fili a gidan, ya zamana a kullum itacen yake kawowa ya ajiye ba tare daya siyar ba.
 Rannan akayi sa'a, lokacin ana fama da muku-mukun sanyi, sai wani Sarki yazo shigewa ta wannan ƙasa da jama'ar sa.
Ya sauka a wani daji nesa da gari, sannan ya umarci barorinsa su bazama nemo itacen da za'a hura wuta don jin ɗumi.
 Koda isowar barorin cikin gari, sai sukayi kiciɓus da gidan Nandu mai ɗauke da tarin itace. Sai kuwa suka nuna buƙatuwarsu ga wannan itace. Nandu ya siyar dashi baki ɗaya garesu. Ai kuwa ya samu riba mai yawa daga wannan ciniki.
A wannan lokaci, Kar kaso kaga murna wurin Harimbai da Nandu.
Rannan kuma, Nandu yana saran itace, sai yazo kan wata bishiya mai kyau. Ganyayenta yala-yala, itacen jikinta kuwa sala-sala ne.
Daya komo gida sai yake nunawa matarsa kalar itacen daya samo a wannan ranar. Sai ta cika da murna, tace "Maigida, wannan ai itacen Sandal ne mai daraja. Aikuwa ya kamata ka ƙoƙarta samo irinsu da yawa ka girke a gidan nan".
Kasancewar Haribai daga gidan sarauta take, ta san darajar wannan itace. Domin sarakuna sunfi son ayi amfani dashi wajen ƙone gawarsu idan sun mutu ko kuma wajen shagalin bukuwan Havan da Pujan.
  Kashe gari Nandu ya tafi daji, ya lalubi wannan itaciya ta sandal tare da soma saran ressan ta a hankali ta yadda zata ƙara tohowa. Haka ya rinkayi a kullum, daga wannan zuwa waccan, har sai daya tara wannan itace da yawan gaske.
Akwai wata alƙarya a kusa da birnin Pitugar wadda aka wayi gari Sarkinta ya rasu. Kafin rasuwarsa kuwa attajirin gaske ne. Har kuma yayi wasicci da a ƙone gawarsa da itacen Sandal bayan rasuwarsa.
 Sai dai kuma akaf garin, an rasa wanda keda wadataccen itacen sandal da zai isa shagalin wannan biki. Akan haka ɗan sarki mai mutuwa ya bada cigiya zuwa maƙwabtan birane, har kuma akazo masa da labarin cewa akwai wani mai suna Nandu yana dashi.
  Sai yace aje wajensa a siyo masa itacen akan ko nawa ya yanka.
Barorin ɗan sarkin sukayi murna da suka tarar da cewa Nandu nada kalar itacen da uban gidansu keso kamar yadda labari yaje gareshi. Suka siyi itacensa da darajar gaske.
Daga nan fa Nandu da mai ɗakinsa suka fita daga kangin talauci. Tunda sun samu tarin dukiya.
 Nandu yasa aka gina musu ƙatan gida na sarauta mai cike da manyan zauruka, kai kace gidan sarkin garin ne.
Bayan tsawon lokaci da auren Nandu da Haribai, sai mahaifinta Sarki Dheema ya cika da tausayin ƴartasa, har ya soma da-na-sanin hukuncin daya ɗauka akanta.
Rannan sai ya yanke shawarar ya kai ziyara a garesu duka domin ganin halin da suke ciki.
Bayan ya gama shirya kyaututtukan dazai kai musu, sai ya tashi tare da da barorinsa, kai tsaye ya nufi gidan babbar ɗiyarsa Kalimbai. Yana ɗokin ganinta, a zuciyarsa yana rayawa cewar tabbas tana cikin farin ciki.
 "Ɗiya ta Kamli, yaya kike?" Sarki Dheema ya faɗa yayin haɗuwar su da Kalimbai.
Kalimbai ta rugo da murna, ta gaishe da mahaifinta. Sannan ta gabatar masa da ƴaƴayenta waɗanda tace ƙiriniya tayi musu yawa, ko makaranta ma basa zuwa.
Sarki Dheema ya kaɗu da yadda yaga wannan gida duk a hargitse. Ga yara duk babu natsuwa. Sannan Barori biyu ne kaɗai suka rage a gidan, yayin da a farkon aurensu gidan cike yake da masu hidimta musu. Tabbas da alamu karayar arziƙi ta gitta a wannan gida.
Ai kuwa da Sarki ya zanta da ɗiyar tasa sai ya gane cewar itace silar durƙushewar maigidan nata, domin kullum cikin buƙatar kashe kuɗaɗe take, ta gaza sauya rayuwa daga wadda ta saba a gidan sarauta zuwa gidan aure data samu kanta.
Ran Sarki Dheema a ɓace ya fito gidan, yace gida zai koma domin shawarta abinyi.
Yana isa kuma sai akazo masa da katin gayyata, akace masa wani attajiri ne yayi sabon gida yake gayyatarsa bikin tarewa domin neman albarkarsa.
Da sarki ya isa gidan, sai yake ta mamakin girma da kasaitar sa. Mai gidan ya fito ya tarbeshi. Sarki yayi mamakin yadda wannan baƙon attajiri yazo garinsa ya bunƙasa ba tare da saninsa ba.
Ana haka sai ga ƴarsa Hambai ta fito cikin kayan ƙawa, tana ɗauke da murmushi a fuskarta, tana mai marhaba lale ga mahaifinta.
  "Sannu da zuwa mai martaba mahaifina".
Sarki Dheema ya cika da mamaki, "ɗiya ta, gidan kine wannan!!!?"
Ta amsa masa da cewa "kwarrai kuwa"
"Tayaya haka ta faru?" inji Sarki Dheema.
 Hambai tace "Ranka ya daɗe, ka tuna da abinda ka taɓa karantawa a ɗaki na?.." Daga nan cikin ladabi ta zayyana masa duk hanyoyin da suka bi har rayuwarsu ta zamo haka.
Sarki Dheema ya gyaɗa kansa sama cikin mamaki. Ya raya a zuciyarsa cewa hakika ƴarsa tayi gaskiya.. Duk gidan dake ɗauke da Mace mai hikima, wannan gida sai ya bunƙasa.."