Sunday, 19 August 2018

KANO DAGA TSAUNIN DALA: WATA MAHANGA A TARIHIN HAUSA

KANO DAGA DUTSEN DALA: WATA MAHANGAR AKAN TARIHIN HAUSA DA HAUSAWA

DAGA SADIQ TUKUR GWARZO
  08060869978
Kano ta dabo tumbin giwa, mai Dala da Gwauron dutse.
  Wannan wani shahararren kirari ne da kowa ya sani ana yiwa Kano, ta yadda ake koɗa garin  tare da  jiɓantashi da manyan tsaunikan garin masu suna Dala da Gwauron dutse.
Akwai maganganun masana da dama game da tarihin waɗannan tsaunika, sai dai kuma wannan wani tarihi ne da muka samo daga bakunan mazauna yankin da waɗannan duwatsu suke a wata ziyara da mukayi zuwa yankin.
Mal Yahaya Madigawa, matashi mai bibiyar tarihi kuma marubuci, shine ya zagaya damu wuraren da muke da bukatar gani, ciki kuwa harda saman tsaunin Dala, inda tsawon lokuta ake bautar aljana tsumburbura akai.
  Da fari dai, wannan mahanga ta tafi akan cewa Dala, Gwauron dutse da kuma Fanisau kamar yadda aka sani ba duwatsu bane, tarin ƙasa ce da wata ƙabila ta taɓa tarawa tsawon shekaru da suka gabata.
Ance Marigayi Mal Mudi Speaking, da wasunsa na daga cikin masu irin wannan ra'ayin.
Ance sunan wannan ƙabila Dala, kuma dalilin tara ƙasar na da alaka da al'adarsu ta tulawa ƙabarin manyansu ƙasa kwatankwacin gine-ginen pyramid da aka samu a ƙasashen Misira da Sudan.
Don haka ake ganin sa'ar da shugaban ƙabilar Dala ya rasu sai aka binne shi a inda tsaunin Dala yake ayau, sannan mabiya ƙabilar suka bazama kurfa-kurfa tare da lalubo ƙasa suna tulawa a saman ƙabarin, shine kuma har saida wajen ya zama tsauni babba kamar dai yadda ake iya gani zuwa yanzu duk kuwa da kasancewar Ruwa ya zaizaye tsaunin sosai.
Shi kuma Gwauron dutse ance gawar matar Shugaban nasu ce, yayin da ake kallon tsaunin Fanisau a matsayin kushewar ɗansu.
Ance asalin waɗannan ƙabila mai suna Dala mazauna duwatsu ne, kuma a Magwan aka sansu da zama baki ɗayansu. Koda yake, wasu na hasashen daga habasha suka taso tun zamanin Nana Bilkisu da Annabi Sulaiman A.S, yayin da wasu ke kallon kasancewarsu a matsayin jikokin ƙabilun NOK da kimiyya ta tabbatar da fakuwar su a wuraren arewacin Nigeria shekaru kimanin dubu biyu da suka gabata.
Babban abu dai shine, lallai da akwai alamar alaƙa tsakanin waɗannan mutane da akace sun zauna a Magwan da kuma ƙabilun da suka zauna a Lupur, Sontolo, Kwatarkwashi da sauran tsoffin duwatsu dake wannan yanki waɗanda aka tabbatar da cewa mutanen baya sunyi rayuwa a samansu, musamman idan aka kalli yadda ɗaukacinsu suka rayu akan duwatsu.
Wani Masanin kimiyyar tantance adadin shekarun kayan tarihi mai suna Mallam Habib ya faɗa cewar sunbi diddigin tarin wannan ƙasar dake tsube a tsaunin Dala a wani ɗan ƙwarya-ƙwaryar bincike da suka gudanar, har kuma sun samu cewa tsaunin na ɗauke ne da tarin ƙasa mabanbanciya da aka ɗebo daga wasu sassan kano. Har yake ganin an ɗebo ƙasar ne a wasu yankunan da suke tsakanin birnin kano zuwa Gwarzo.
Sai mahangar tace gushewar wannan ƙabila data auku tsawon lokaci ne ya kawo zamanin ƙabilar Barbushe, waɗanda suka gaji tsaunin har kuma suka rinƙa bautar aljanna tsumburbura a saman sa.
Dangane da shaharar wannan tsauni a zamanin da, har zuwa yanzu mun lura akwai wasu mutane daga mazauna yankin tsaunin Dala masu iƙirarin cewa asalin tushen su ba anan yake ba, kawai dai farauta ce tayi silar  zuwan kakannin su gefen tsaunin a tsawon zamani daya gabata, har kuma daga baya mutanen suka yanke shawarar zama a wurin.
Asalin wajen ance daji ne mai ɗauke da albarkatu, amma daga baya sai aka soma  haƙar tama a jikin tsaunin, kasancewar an ɗebo ƙasashe masu ɗauke da ita tamar tsawon zamani daya gabata, sai kuma ta kasance tana girma kamar yadda marmara keyi.
 Haƙo tama ɗin ne kuma ya sake janyo hankulan mutane suka rinƙa zama a yankunan, suna sarrafa ta wajen yin ƙarafa, sannu a hankali wajen ya zama gari mai haɓaka.
A irin haka ne akace wani shehin malami ya ƙaraso wurin daga ƙasar Libya mai suna Fatahullahi, wanda akewa laƙabi da Abul Raas, amma hausawa ke kiransa da suna 'Bunsurun Dala' wai saboda tulin gemanyar dake fuskarsa wanda yasha ban-ban da al'adarsu ta wancan lokacin.
Shehi Fatahullah ya riska a lokacin ana musulunci a kano, amma kuma hawa tsaunin Dala don neman biyan buƙatu bai saki kanawa daga abinda suka gada na maguzanci ba, wanda hakan yasa ya ƙirƙiro da wata al'ada data ɗoru akan musulunci bisa burin sauya akalar mutanen daga maguzanci zuwa ɗorar da wani abu na addini, wanda yayi hasashen idan addini yayi ƙarfi za'a tureshi baki ɗaya a ɗora mutane akan addini zuryan. Wasu na ganin tun daga can aka sauya dalilin hawa tsaunin da wani abu makamancin bikin takutaha.
Ance marigayi Fatahullah ya riski Kano a lokacin tana ƙarƙashin daular Borno ne, shine yasa wasu ke ƙaryata zamansa a Kano dube da rubututtukan da almajiransa sukayi suna masu ambatar sunan Borno a matsayin inda ya koma da zama, don haka tana iya yiwuwa a zamanin sarkin Borno Mai Idris Alooma ne wanda ya rayu tsakanin ƙarni na goma sha uku zuwa na sha biyar.
Har yanzu kuma kabarinsa yana gefen tsaunin dala, zagaye acikin wani masallaci kawwamamme.
Game da asalin Hausawa, mun samu cewar akwai daga mazauna yankin da suke cewar Hausawa na asali wata ƙabila ce mai suna 'MANGU', kafin daga baya a rinƙa kiransu da suna 'Maguzawa', waɗanda akace sun taso ne daga wani yanki na Jos. Kuma akace har yanzu akwai ɓurɓushin su dake zaune acan....



Thursday, 9 August 2018

TARIHIN SARAKUNAN KANO A TAƘAICE

KASHI NA ƊAYA

DAGA SADIQ TUKUR GWARZO, RN.
         08060869978

Mazaunan Kano na Farko
Marigayi Alhaji Abubakar Dokaji ya faɗa a littafinsa mai suna 'Kano ta dabo cigari' cewar tun a ƙarni na tara waɗansu maharba da babu takamaimen inda suka fito suka zauna akan duwatsun dake sararin da ake kira Kano ayau, watau misalin dutsen Dala, Gwauron dutse, Magwan, da Fanisau.
  Sai dai, wasu na ganin faruwar hakan ya auku ne tun a wajajen ƙarni na bakwai
   Farauta shine mafi akasarin abinda waɗannan mutane suka fiyi, amma daga bisani suka soma taɓa noma.
Sarkin Kano na ɗaya: Bagauda.
Masu haɗa tarihin Kano dana Bayajidda, sunce yawaitar rashin zama lafiya daga mahara masu zuwa kamen bayi ne yasa mazauna kano suka rinƙa kai ƙorafi ga sarauniyar Daura Daurama. A lokacin Sarkin Daura Bawo kuwa sai ya turo ɗansa Bagauda Kano don yayi mulki.
  Akace Bagauda yayi zamani da wani bafaden Barbushe shugaban masu bautar tsunburbura mai suna Jankare, kuma daya ƙi bashi goyon baya sai yasa aka kama shi aka yanka.
  Bagauda ya iske alƙaryun Gazargawa, Zadawa, Fangon, Zaura, Dundunzuru, Shiriya, Sheme, Gande, Tokarawa, da wasunsu waɗanda ke zazzaune a sassan ƙasar kano irinsu Wasai, Sontolo, Barkum Watari, Jakara,  Shike, karmami, Ringim da wasunsu.
Bagauda ya sauka a Dinari ya shekara biyu, sannan ya koma Barka ya gina Talotawa, sannan ya koma Sheme inda ya tarar da waɗansu manyan matsafa waɗanda ya mallake su, misalin Galosami, Barmi, Gazawari, Dabgege, Fasataro da Bakin Bunu.
   Ance sa'ar da Bagauda zai baro Daura ya taho ne da mutanensa irinsu Kududdufi, Buram, Isa, Baba, Akasan, Darman, da Goriba.
  Sai dai, Maje Ahmad Gwangwazo ya ruwaito shigen haka a littafinsa 'Tarihin Kano kafin Jihaɗi littafi' na ɗaya, amma akwai saɓani a wasu wuraren, musamman dalilin zuwan Bagauda daga Daura da kuma hawan Sarautarsa.
   A nashi ɓangaren, yace Bagauda ɗan Bawo tun yana yaro yake jin labarin yadda yankin Kano ke haɓaka daga mahaifiyarsa Sarauniya, don haka daya girma sai ya kwashi abokansa ya sulale zuwa kano. Kuma sai daya shafe shekaru biyu yana koyon yaren Hausa, domin shi Bamange ne. Sannan yace mutanen kano da kansu suka ga dacewar ayi masa sarauta saboda halayensa na kirki wajen yiwa jama'a Hukunci da kuma jarumtakarsa.
 Waƙar Bagauda kuwa da Mal. Abdullahi Kabuga ya rera mai bayar da tarihin Kano, ta nuna cewar Kafin Bagauda yazo kano, anyi wata gagarumar yunwa a wannan yanki daya zama ƙasar Hausa ayau, don haka mutane suka rinƙa barin  garuruwansu suna tafiya neman abinci. A haka Bagauda yazo kano ya sauka a Maɗatai, kuma ya soma taɓa noma tare da ganin albarkarsa. Daga nan ya aika gida iyalansa, ƴanuwansa da abokansa suka taho gare shi. Daga cikinsu akwai irinsu Shehe, Gwale,
A wata mahangar kuma musamman wadda ta fito daga wasu Maguzawan Kano, sun faɗa cewar Bagauda Bamaguje ne Bahaushe, wanda ya riski Kano daga yamma. Kuma asali ya baro gida ne da ɗan Uwansa mai suna Bugau. Bagauda ya rabu da yayansa Bugau a garin Baɗari yazo wurin wani ɗan kabilarsa mai suna Goɗiya ya zauna, daga bisani ya wuce zuwa kano.
  Bagauda dai yayi shekaru 66 a mafi inganci yana mulkin kano, kuma a zamaninsa ance an samu matuƙar tsaro da zaman lafiya a kano, duk da wasu na ganin har ya mutu akwai ɓurɓushin mabiya Barbushe da basa yi masa biyayya.
Sarkin Kano na biyu: Warisi
Ance shi ɗa ne ga Bagauda, sunan Mahaifiyarsa Saju. Alhaji Ahmad Bahago ya kawo waɗannan sunaye a matsayin manyan fadawan Warisi a littafinsa Kano ta Dabo Tumbin Giwa: Galadima Mele, Barwa,Buram, Sarkin Gija Koramayi, Maidalla Zakar, Makama Gargi, Jarmai Goshin wuta, Jarmai Baƙoshi da waɗansu.
Ance ya shekara 33 kan karagar kano, a zamaninsa aka soma naɗa sarautar gado a kano, watsu ƴaƴayen abokan mahaifinsa suka rinƙa samun sarautar iyayensu bayan rasuwarsu kamsr yadda ta auku gareshi. Kuma an samu zaman lafiya a mulkinsa, saidai ba kamar zamanin Bagauda ba.
Sarkin Kano na uku: Gijimasu
Ance shi ɗane ga Warisi, sunan mahaifiyarsa Yanusa, ya zauna a Garazawa da mulki tsawon lokaci, sannan shine ya soma bada shawarar yiwa kano ganuwa don kangeta daga mahara.
   A zamanin nasa ne kuwa aka soma ginin ganuwa, ya haɗa kusan kafatanin mazauna kano aka soma aikin ginin ganuwa. Bayan an gama, sai akayi mata kofofi takwas. Ance shanu ɗari sarki ya yankawa ma'aikata a ranar farko ta soma wannan aiki. Wasu sunce ya kasance mai yawan kyauta don haka ya samu nasarar haɗa kan jama'ar Kano a zamanin sa.
 Akwai masu cewa ya gina fadarsa ne a Madabo, amma wasu sunce a Gwammaja yayi ta.
Sarakunan kano na huɗu: Nawata da Gawata
Ance su tagwaye ne sunyi mulki tsawon shekara ɗaya kuma a tare, idan yau ɗaya na bisa mulki, ɗayan zai kasance a gida sai kashegari yazo yahau karagar mulki.
  Kuma tagwayen masu da ake gani har yanzu a hannun Sarkin Kano nasu ne aka haɗe wuri ɗaya tsawon lokaci.

Tuesday, 7 August 2018

TARIHIN FANISAU

TARIHIN DAKE YANKIN 'TSAUNIN FANISAU'

Sadiq Tukur Gwarzo, RN.

Tarihin garin Fanisau na komawa ne shekaru sama da dubu kwatankwacin shekarun kafuwar Kano.
   Wani tsoho mai suna Usman Abdul'aziz Jikan wakilin Shawara, ya sanar mana da cewa tarihin Fanisau da  tarihin Kano abubuwa biyu ne da suke a matsayin ɗaya.
    Babu wanda ya san ainihin lokacin da mutane suka soma zama a gefan wannan tsauni na Fanisau tun kafin ma wurin ya zama gari kenan amma dai an gamsu da cewa kusan duk shigen al'adun da suka wakana akan dutsen Dala an samu kwatankwacinsu akan tsaunin Fanisau.
    Wani Bamaguje da ake kira Gwambari Jade ne ya fara dawowa saman tsaunin Fanisau da zama daga kano sama da shekaru dubu ɗaya da suka gabata, shikuwa ya kasance Waziri ne ga Barbushe a wajen bautar gunkin Tsumburbura dake saman dutsen Dala tun a zamanin Maguzanci.
     Ance da mazauna Dala, da Magwan, da Gwauron Dutse gami da Fanisau duk maguzawa ne masu ƙabila iri ɗaya. Sai dai sanin tushen su gami da yarensu zuwa yanzu yana da matuƙar wahala.
   Irin waɗancan mutane ne suka soma zama a kewayen tsaunin Fanisau tun wurin yana ƙurgurmin daji.
 Tana iya yiwuwa albarkar namun daji dake wurin da kuma neman tallafin Aljanar dake saman dutsen ce ta sanya mutane suka rinƙa komawa yankin da zama, sannu a hankali har ya zama gari.
   Tabbas, akwai wata aljana dake saman wannan tsauni na Fanisau wadda ake kira da suna 'Aljanar Kan Dutse', wadda akace ita ƙawa ce ga Aljanna Tsumburbura. Wadda kuma aka samu cewa asalin maguzawan da suka soma zama a wurin suna mu'amala da ita na tsawon lokaci.
Ance tun a wancan zamani, takan taimaki garin wajen samun nasarar duk wani yaƙi daya taso. Sannan da zarar an tura mayaƙan Fanisau yaƙi zuwa wani yanki, har kuma sukaci nasara, sai aji garin fanisau ya kaure da guɗa. Don haka tanan mutanen garin kan gane nasarar yaƙin mayaƙansu tun gabanin su komo gida.
 Sannan duk tawagar data nufo garin Fanisau da yaƙi zata ganshi yayi duhu, hayaƙi na tashi daga gare shi.
   Wata majiya tace wani bamaguje mai suna Nisau shi ne uban Gumbarjado mai gida bisa saunin fanisau. Daga sunan ne aka samo fanisau.
A tsawon zamani, garin Fanisau ya kasance kamar wata unguwa ce dake nesa da birnin kano wanda sai an shige wani surƙuƙin daji ake kaiwa gareshi. Ance sai a zamanin Sarkin Kano Muhammadu Rumfa yasa aka zagaye garin da ganuwa, sannan aka fitar masa da kofofin shiga ta yadda da zarar yaƙi ya matso, sai mutanen dake zaune a kewayen garin su rugo su shige don meman mafaka.
Ance Sheikh Abdulƙadir Al Magili daya  riski Kano a wuraren ƙarni na goma sha biyar zamanin Mulkin Sarkin Kano Muhammadu Rumfa ya sauka ne a Fanisau, sarki yana aika masa da abinci gami da sauran ababen buƙata. Amma daga baya aka tasoshi ya dawo Zauren Tudu, dake Ƙofar Wambai ta birnin Kano.
Asalin sunan Fanisau ya fito ne daga wani shahararren malami daya soma zama a garin bayan gushewar mulkin Maguzanci, ana kiransa da suna Mallam Nisau.
Shaharar Mallam Nisau ta sanya har daga wurare ake zuwa ɗaukar darasu wurinsa. Don haka mutane kan ce 'Na tafi Fan Nisau'. Har daga bisani ake kiran garin baki ɗaya da suna Fanisau.
Garin Fanisau na cike da Mayaƙa waɗanda suka taka matuƙar rawar gani wajen kare martabar Kano. Shiyasa ake ganin akwai kyakkyawar alaƙa mai tsawo tsakanin mazauna Fanisau da kuma mutanen birnin Kano, saboda tun tale-tale, duk yaƙin da Kano zata buga sai ta tafi da mayaƙan Fanisau.
Amma sai a zamanin mulkin Fulani aka soma yunƙurin ginawa garin babban Masallaci tare da gidan Sarki. Kuma ana ganin koda sheik Abdullahi Gwandu, ƙani ga Mujaddadi Usmanu ɗan Fodio yazo kano, sai daya riski Fanisau.
An sanar mana cewa Sarki Ibrahim Dabo ne ya soma wannan aiki na gina masallaci, sai kuma babban ɗansa daya gajeshi watau Sarki Usmanu ya Kammala.
Daga nan kuma aka soma yin hawan Fanisau, inda Sarki ke ware rana dashi da tawagarsa su tafi Fanisau, ya zauna a gidansa tsawon yini ɗaya sannan ya komo birni, al'adar da har zuwa yau ba'a daina yinta ba.
Akwai labarun fitattun mayaƙa da yawa da aka taɓa samu a garin Fanisau, misalin su Samagi, Sha'aike, Ɗan Toro, Bashar, da wani mai suna Sa'adu Kuzo ku duka..
Sa'adu kuzo ku duka shine wanda akace a zamaninsa saboda tsabar jarumtaka, duk yawan dakaru zai afka musu har kuma yayi galaba akansu. Don haka jama'a ke matuƙar tsoronsa har takai ko Dagacin garin baya iya shigewa ta gabansa face ya cire takalmi.
Sannan ance ko ɓarawo aka kamo daga wani gari za'a kai shi Kano don yin hukunci, sai an kawo ɓarawon gabansa ya buge shi sannan ayi gaba..
 

BINCIKE A LUPUR, TSOFFIN MAZAUNAN MAGUZAWA DAKE RANO

BINCIKE A LUPUR, YANKI MAI ƊAUKE DA TSOFFIN TSAUNIKAN DA MAGUZAWA SUKA TAƁA KAFA DAULA.
DAGA
 SADIQ TUKUR GWARZO, RN.
  08060869978

Lupur, wani ɗan ƙauye ne dake daura da sabon garin Rano, koda yake ana iya cewa manyan tsaunikan nan masu tarihi ne suka raba ƙauyen da garin na Rano, watau duwatsun Ƙurƙubu, Ƙurgum, Damusu, da Mairamu.
Manyan ababen  ƙayatarwa a ƙauyen sune duwatsun Jidal da kuma Tsiriri dake can ƙurya dashi, dukkaninsu kuwa suna da tsohon tarihi.
Don haka sai na yanke shawarar ziyartar gani da ido zuwa garin.
Kafin zuwana, na saurari labaru kala-kala game da waɗancan tsaunika. Daga ciki akwai masu cewa Fadar sarakunan farko na maguzawa na cikin tsaunikan Lupur ne, akwai koguna masu duhu da kuma ababen tsoratarwa aciki.
 Ibrahim Haladu, shine matashin daya amince yayi mini rakiya zuwa cikin surƙuƙin waɗannan duwatsu. Haka kuma mahaifinsa Mallam Haladu tsoho ne, masanin tarihin wannan yanki, wanda har Maimartaba Sarkin Rano kan aiko mutane gareshi domin jin abinda ya sani game da tarihin tsohuwar Rano.
 Bayan mun gusa nesa da gari, sai gamu daf da sashen ganuwa ginin dutse, wajen ya zama gomaki amma dai ana iya ganin ɓurɓushin duwatsu da akayi alamomi dasu tun abaya, muna tsallakata  kuwa sai yace mini yanzu mun shigo asalin garin daya fara kafuwa kafin komawa Rano.
Wurin kewaye yake da manyan tsaunikan can dana faɗa a sama, watau Ƙurƙubu, Mairamu, Ƙurgum, Damusu, da wasunsu, amma Jidal da Tsiriri na can ciki.
A saman waɗannan duwatsun na hango birrai farare suna ta kaikawo, shigen jikinsu yaso yayi kama dana kyanwa. Ɗan rakiya ta yace mini sun fito shan ɗorawa ne, kuma sun saba ganinsu suna fitowa gungu-gungu. Wani sa'ilin ma har ƙasa suke saukowa takalar faɗa.
 Ibrahim ya nuna mini gonakinsu a ƙasan waɗannan duwatsu, kuma ya sanar mini cewa birrai na zuwa suyi musu ɓarna lokaci zuwa lokaci.
Da muka yi gaba daga nan, akwai wani sashen gini da aka nuna mini na duwatsu. Wajen ance tsohuwar fada ce, mai ɗauke da zauruka da manyan ɗakuna, har ma da inda ake zama don yin fadanci.
Ban samu labarin sunayen sarakunan da sukayi mulki acikin wannan fada ba, amma dai ance mini wannan waje ya girmewa tsohon garin Rano dake can tsallaken duwatsun, inda shima ake iya ganin sashen gini na ƙasa da sarakunan zamanin suka rayu a ciki.
 Sai dai kuma ana tsammanin sai da wayewa ta zowa waɗannan maguzawa sannan suka sauko daga kan tsaunika tare da soma yin bukkoki a dandamarin ƙasa. A zamanin ance Sarki kaɗai ake ginawa gida da duwatsu.
Babu kuma takamaimen bayani game da hanyar zaɓen shugaba a wancan tsohon zamani, amma dai kamar yadda aka sani, bata wuce gado ko kuma fin ƙarfi.
Daga can ƙurya kuma akwai sashen ƙofofin shiga gari masu suna ƙofar Ƙahu da Ƙofar Bezo, ance mutanen da suka zauna a wurin sun samar dasu ne domin sanya ƙarin tsaro kafin a riski inda suke.
Baya da nan kuma sai wani babban dandali, inda aka asanar mini cewa ainihin wajen matattara ce, kasancewar akwai mutane zazzaune a kusan kafatanin tsaunikan, don haka suna samun lokacin da suke haɗuwa don yin bautar gumakansu misalin gunki Darmo, har ma da yin wasanni.
Daga wasannanin da akace suna yi baya da kaɗe-kaɗe da raye raye irin na maguzanci, akwai wasan Ƙwado da ayanzu akafi sanin mata dashi. Don haka har yanzu ana iya ganin wani dutse da suka ƙwaƙule, suka yi masa ramuka kamar tandarun waina, wanda suke wasan ƙwado a kanshi.
Ance wani sarkin Rano ya taɓa zuwa ya umarci a haƙe shi a mayar dashi inda masarautarsa take, amma duk tsawon haƙan da akayi sai dai aga dutsen na ƙara zurfi, daga ƙarshe sai aka haƙura ba tare da angano cibiyarsa ba.
A gefe ɗaya kuma akwai tsaunikan Tsiriri da Jidal waɗanda ana iya cewa sune sukayiwa wannan farfajiya ƙawanya.
Shi tsaunin Tsiriri anan ne kogo yake, watau inda Zamna Kogo ya samo asali, inda akace anan ainihin maguzawan suka rinƙa zama tare da iyalansu.
Na samu hawa saman tsaunin tare da shiga kogon, na ganshi da faɗi, da kuma duwatsun zama barbaje a ciki, harda wani faffaɗa da akace anan shugabansu yake. Sai kuma wasu lunguna da suke sadarwa izuwa gareshi..
Akwai kuma wata rijiya mai suna Kurfafiya a saman tsaunin wadda ruwa mai haske yake tsatsowa daga tsakankanin duwatsu, wadda kuma akace tarihi ya nuna cewar daga gareta mazauna duwatsun ke samun ruwansha, haka kuma bata taɓa ƙafewa ba.
Ance maguzawan da suka rayu a wajen basa sanya tufafi, sai dai su rufe tsiraicinsu da ganyaye.
Haka kuma farautar namun daji ce babbar sana'ar su, gasu karfafa, don haka suna yawan fita yaƙi ga maƙwabtan birane, suma kuma ana yawan kawo yaƙi izuwa garesu.
Kuna iya kallon videon wajen kai tsaye tanan:- https://youtu.be/laLgoxK1RCM