KANO DAGA DUTSEN DALA: WATA MAHANGAR AKAN TARIHIN HAUSA DA HAUSAWA
DAGA SADIQ TUKUR GWARZO
08060869978
Kano ta dabo tumbin giwa, mai Dala da Gwauron dutse.
Wannan wani shahararren kirari ne da kowa ya sani ana yiwa Kano, ta yadda ake koɗa garin tare da jiɓantashi da manyan tsaunikan garin masu suna Dala da Gwauron dutse.
Akwai maganganun masana da dama game da tarihin waɗannan tsaunika, sai dai kuma wannan wani tarihi ne da muka samo daga bakunan mazauna yankin da waɗannan duwatsu suke a wata ziyara da mukayi zuwa yankin.
Mal Yahaya Madigawa, matashi mai bibiyar tarihi kuma marubuci, shine ya zagaya damu wuraren da muke da bukatar gani, ciki kuwa harda saman tsaunin Dala, inda tsawon lokuta ake bautar aljana tsumburbura akai.
Da fari dai, wannan mahanga ta tafi akan cewa Dala, Gwauron dutse da kuma Fanisau kamar yadda aka sani ba duwatsu bane, tarin ƙasa ce da wata ƙabila ta taɓa tarawa tsawon shekaru da suka gabata.
Ance Marigayi Mal Mudi Speaking, da wasunsa na daga cikin masu irin wannan ra'ayin.
Ance sunan wannan ƙabila Dala, kuma dalilin tara ƙasar na da alaka da al'adarsu ta tulawa ƙabarin manyansu ƙasa kwatankwacin gine-ginen pyramid da aka samu a ƙasashen Misira da Sudan.
Don haka ake ganin sa'ar da shugaban ƙabilar Dala ya rasu sai aka binne shi a inda tsaunin Dala yake ayau, sannan mabiya ƙabilar suka bazama kurfa-kurfa tare da lalubo ƙasa suna tulawa a saman ƙabarin, shine kuma har saida wajen ya zama tsauni babba kamar dai yadda ake iya gani zuwa yanzu duk kuwa da kasancewar Ruwa ya zaizaye tsaunin sosai.
Shi kuma Gwauron dutse ance gawar matar Shugaban nasu ce, yayin da ake kallon tsaunin Fanisau a matsayin kushewar ɗansu.
Ance asalin waɗannan ƙabila mai suna Dala mazauna duwatsu ne, kuma a Magwan aka sansu da zama baki ɗayansu. Koda yake, wasu na hasashen daga habasha suka taso tun zamanin Nana Bilkisu da Annabi Sulaiman A.S, yayin da wasu ke kallon kasancewarsu a matsayin jikokin ƙabilun NOK da kimiyya ta tabbatar da fakuwar su a wuraren arewacin Nigeria shekaru kimanin dubu biyu da suka gabata.
Babban abu dai shine, lallai da akwai alamar alaƙa tsakanin waɗannan mutane da akace sun zauna a Magwan da kuma ƙabilun da suka zauna a Lupur, Sontolo, Kwatarkwashi da sauran tsoffin duwatsu dake wannan yanki waɗanda aka tabbatar da cewa mutanen baya sunyi rayuwa a samansu, musamman idan aka kalli yadda ɗaukacinsu suka rayu akan duwatsu.
Wani Masanin kimiyyar tantance adadin shekarun kayan tarihi mai suna Mallam Habib ya faɗa cewar sunbi diddigin tarin wannan ƙasar dake tsube a tsaunin Dala a wani ɗan ƙwarya-ƙwaryar bincike da suka gudanar, har kuma sun samu cewa tsaunin na ɗauke ne da tarin ƙasa mabanbanciya da aka ɗebo daga wasu sassan kano. Har yake ganin an ɗebo ƙasar ne a wasu yankunan da suke tsakanin birnin kano zuwa Gwarzo.
Sai mahangar tace gushewar wannan ƙabila data auku tsawon lokaci ne ya kawo zamanin ƙabilar Barbushe, waɗanda suka gaji tsaunin har kuma suka rinƙa bautar aljanna tsumburbura a saman sa.
Dangane da shaharar wannan tsauni a zamanin da, har zuwa yanzu mun lura akwai wasu mutane daga mazauna yankin tsaunin Dala masu iƙirarin cewa asalin tushen su ba anan yake ba, kawai dai farauta ce tayi silar zuwan kakannin su gefen tsaunin a tsawon zamani daya gabata, har kuma daga baya mutanen suka yanke shawarar zama a wurin.
Asalin wajen ance daji ne mai ɗauke da albarkatu, amma daga baya sai aka soma haƙar tama a jikin tsaunin, kasancewar an ɗebo ƙasashe masu ɗauke da ita tamar tsawon zamani daya gabata, sai kuma ta kasance tana girma kamar yadda marmara keyi.
Haƙo tama ɗin ne kuma ya sake janyo hankulan mutane suka rinƙa zama a yankunan, suna sarrafa ta wajen yin ƙarafa, sannu a hankali wajen ya zama gari mai haɓaka.
A irin haka ne akace wani shehin malami ya ƙaraso wurin daga ƙasar Libya mai suna Fatahullahi, wanda akewa laƙabi da Abul Raas, amma hausawa ke kiransa da suna 'Bunsurun Dala' wai saboda tulin gemanyar dake fuskarsa wanda yasha ban-ban da al'adarsu ta wancan lokacin.
Shehi Fatahullah ya riska a lokacin ana musulunci a kano, amma kuma hawa tsaunin Dala don neman biyan buƙatu bai saki kanawa daga abinda suka gada na maguzanci ba, wanda hakan yasa ya ƙirƙiro da wata al'ada data ɗoru akan musulunci bisa burin sauya akalar mutanen daga maguzanci zuwa ɗorar da wani abu na addini, wanda yayi hasashen idan addini yayi ƙarfi za'a tureshi baki ɗaya a ɗora mutane akan addini zuryan. Wasu na ganin tun daga can aka sauya dalilin hawa tsaunin da wani abu makamancin bikin takutaha.
Ance marigayi Fatahullah ya riski Kano a lokacin tana ƙarƙashin daular Borno ne, shine yasa wasu ke ƙaryata zamansa a Kano dube da rubututtukan da almajiransa sukayi suna masu ambatar sunan Borno a matsayin inda ya koma da zama, don haka tana iya yiwuwa a zamanin sarkin Borno Mai Idris Alooma ne wanda ya rayu tsakanin ƙarni na goma sha uku zuwa na sha biyar.
Har yanzu kuma kabarinsa yana gefen tsaunin dala, zagaye acikin wani masallaci kawwamamme.
Game da asalin Hausawa, mun samu cewar akwai daga mazauna yankin da suke cewar Hausawa na asali wata ƙabila ce mai suna 'MANGU', kafin daga baya a rinƙa kiransu da suna 'Maguzawa', waɗanda akace sun taso ne daga wani yanki na Jos. Kuma akace har yanzu akwai ɓurɓushin su dake zaune acan....

No comments:
Post a Comment