Thursday, 29 November 2018

TARIHIN DAMAGARAM (ZINDER)

Tarihin Damagaram.
Muƙala akan Damagaram.

Tsawon lokaci daya shuɗe, labarin baka ya faɗa mana tsawon lokaci daya gabata, wasu mafarauta guda biyu (daga yankin Kelle, cikin Kutus) a lokacin tafiyarsu suna neman wasa suka risƙi ƙasar dana ambata Damagaran.
  Watarana, sai kowannen su yayi shawarar farauta daban da ɗanuwansa. Don haka suka rabu, rabuwar kuma mai tsayi.
Rannan, sai ɗaya daga maharban ya tafi neman tsohon abokin sa,  daga ƙarshe ya same shi yana share ciyaye.
Bayan haɗuwarsu suka gaisa, sai fira ta shiga tsakanin su. Shine sai mafarucin yake tambayar abokin sa daya tarar cikin yaren Kanuri da cewa 'Daa maa grimi?' Ma'ana, 'shin nama kaci ne?'.
Sai kuwa aka sanyawa wannan ƙauye wannan suna, daga baya Hausawa suka tanƙwara sunan tare da soma kiran sa 'Damagaram'.
NB: Gundumar Damagaram jerin wasu ƙauyuka ne  dake ƙarƙashin shugabancin Maalam da magadansa kafin samar da daula a Zinder.
  Daga cikin ƙauyukan akwai: Damagaram, Gorgore, Dumummuge, Ciihanza, Gaafati, Magarya, Lautey, Albarkaaram, Kaasamma, Baadaraaaka, Ganesku, Kirshiyaa.
Maalam, shine wanda ya samar da daular Zinder bayan ya baro ƙasar sa Bornu, ya sauka a ƙauyen Damagaram. Kimanin mil dubu tamanin nesa danan, sai wani maharbin haifaffen Borno yabi da ambaton ƴan gargajiya, yazo domin ƙirƙirar ƙauyen Zinder wanda turawan mulkin Mallaka suka rinƙa kira da suna Zinder.

 Me yasa wannan suna?
 Barth, wanda ya rubuto sunan da 'scinder', ya ambaci sunan a matsayin birnin da Sarkin Damagaram ke da zama ne, kuma har yanzu kuwa anan yake da zama.
Bayan shi, sai Monteil, Foureau, da Lamy suka zaɓi kalmar Zinder domin sanyawa birnin Sarki, ko ace, sunan gari ɗaya daga maƙwabta ne har zuwa yau ya samar da suna Zinder.
 Haka abin yake ga Landeroin, wanda a farƙon ƙarni ya zauna a ƙasar, shi da Kanal Abadie da Serre na Reivers.
Don haka har zuwa lokacin da turawan mulkin mallaka na faranshi suka ƙwace Damagaram, tare da kafuwar Zinder a ƙasar, Mutanen Zongoo, waɗanda asalinsu daga sansanin Tuareg suke, sun zamo maƙwabta na mafi yawan baƙi, a wuraren da a baya can ba sa cikin birnin Zinder.
NB: Ana kiran Gundumar da Sarki ke zaune Birni, tunda Sarki  Tanimun ya gina ganuwa data zagaye birninsa.
Wannan GANUWA da hausa ita ake kira Birni, (ko Garu) daga baya aka faɗaɗa ta inda har kalmar Birni ke nufin gari.
A yanzu, karɓaɓɓen sunan Damagaram shine Zinder. Amma ƴan asalin garin suna cigaba da amfani da kalmar Damagaram wajen wakiltar Zinder. Domin rarrabewa tsakanin birnin Damagaram da kuma ƙasar Damagaram kuwa, sukan ambaci 'Kasal Damagaram' domin nuni da ƙasar Damagaram.
Yaya Garun yake?
A ranar 6 ga watan Nuwamba, birnin Zinder yake wakiltar manyan kusurwowi uku, da katangunsa a baubauɗe, da zagayayyun kusurwowi kimanin faɗin murabba'i 125 na hecta, a zagaye da katangun ƙasa masu tsayin mita 9 zuwa 10 gwargwadon tudun ƙasar wajen, sai kuma kimanin mita 12 zuwa 14 na kauri a kwance, amma suna siririntuwa a tsaye daga ƙasa zuwa sama inda yake komawa kusan santimeta 50 zuwa 60.
Wannan katanga kusan dukkanta an ƙawata ta da siffar haƙoran zarto daga sama, daga wajen katangun kuwa a kwance ya samu zagayawar magudanar ruwa ne wanda akan yi musu wajen zuba jefi jefi.
Daga ciki kusa da ƙofa kuwa, ƙasan katangar na da kauri, saboda dandazon ruɓaɓɓun ciyayi, sannan katangun sun sirance daga sama, kimanin mita 1 ko 2 zuwa wani faffaɗan wuri da akanyi kamar bencin zama don maharba kibbau da masu jefa masu .

An yanki wani tsagi daga Masarautar Zinder ta André Salifou

Sunday, 11 November 2018

TARIHIN IMAM MALIK BN ANAS

TARIHIN IMAMU MALIK BN ANAS

SADIQ TUKUR GWARZO

  Cikakken sunan sa shine Abu 'Abdullah Malik ibn 'Anas ibn Malik ibn Amr al-Asbahi an haifeshi a birnin Musulunci Madina a shekara ta 93 bayan Hijirar Manzon Allah Annabi Muhammad S.a.w, dai-dai da shekara ta 714 miladiyya.
  Ance asali, tsatson sa daga ƙasar Yemen ne, daga ƙabilar al-Asbahi, amma sai kakansa Abu Amir ya dawo Madina da zama bayan ya karɓi musulunci. Mahaifinsa Anas ya ɗauki ilimi a wajen Halifa Umar bn Khattab R.A, kuma dashi akayi aikin tattarawa gami da rubuta littafin Alqurani maigirma a zamanin Halifancin Usman bn Affan R.A. A haka kuma har Allah ya ƙadarta haihuwarsa a birnin na Madina.
   A Littafin Muwaɗɗa nashi Imam Malik ɗin, an faɗi siffar Imam Malik a matsayin dogo kakkaura, mai cikakken farin gemanya da korayen idanuwa.
   Imam Malik ya zamo babban masani a Madina, ko ace a duk duniyar musulunci ma baki ɗaya. Anan madina yayi karatunsa, ya kuma karɓi ilimin sa ne daga hannun Sahabbai da kuma Tabi'ai na Manzon Allah  Annabi Muhammad (s.a.w).
  Kasancewar Mahaifan Imam Malik na da rufin asiri, ya sanya shi mai da hankali kacokan kan meman ilimi daga manyan malumman Madina, musamman ilimin Fiqhu, watau na sanin addinin musulunci.
 Ance ya haddace Alqurani tun da ƙuruciyarsa,  ya koyi karatunsa daga   malamai irinsu Hisham ibn Urwah, Ibn Shihab al-Zuhri, da kuma Abu Hanifa, wanda ya samar da mazhabar Hanafiyya, har ma Imam Malik ya ɗauki darasi a gidan Imamun mabiya Shi'a ɗan uwa ga Annabi S.a.w watau Jafar al Sadiq.
  Ance tun a zamanin sa ake son haifar da Mazhabar sa ta Maliku amma yaƙi yadda, a lokacin Mazhabobin Sunnah uku ne Kacal, watau Hanafiyya, Hambaliyya da Shafi'iyya. Har ma wata rana Halifa Al Mansur yace masa "Ina so na kaɗaitar da ilimi, don haka zan rubutawa kwamandojin yaƙi na da kuma Gwamnoni cewa su maida littafinka Muwaɗɗah doka da za'a rinƙa hukunci akansa, duk wanda yazo da wani abu makamacinsa a kashe shi".
   Da jin haka sai Maliku ya amsa da cewa "Ya kai Jagoran muminai, akwai wata hanyar saɓanin haka ai. Kayi sani Annabi ya rayu ne a wannan alƙarya, kuma ya rinƙa aikewa da dakaru ƙasashe domin yaƙi, kuma bai kame ƙasashe da yawa ba har Ubangiji ya karɓi ransa, daga nan Abu Bakr ya zama Halifa, shima bai kame ƙasashe masu yawa ba. Daga nan sai Umar, wanda ƙasashe da yawa suka samu a hannunsa.
    Don haka Umar ya rinƙa aikewa da sahabban manzon Allah s.a.w waɗannan ƙasashen domin su koyar da addini, kuma mutane basu tsagaita Wajen ɗaukar ilimi daga garesu ba har gushewarsu, inda manyan masana suka gajesu, bayan tafiyarsu waɗansu suka maye gurbinsu, har ya zuwa zamanin nan namu.
   Saboda haka idan ka takura akan sauya mutane daga abinda suka sani izuwa abinda basu sani ba sai su kafirta. A maimakon haka, ka tabbatar da hukuncin da kowaɗanne mutane ke aiwatarwa a ƙasashensu, in yaso sai kai ka ɗauki sanin daga garesu".
  Wata ruwayar kuma akan haka cewa tayi bayan Halifa al Mansur ta saurari yadda Maliku ke bada fatawowi, sai yace "Na ƙuduri aniyar bada umarnin kwafen rubututtukan ka tare da watsa su ga duk inda wani musulmi yake a duniya ta yadda musulmai zasu rinƙa aiki da koyarwar cikinsa, su bar sauran da ba nasa ba".
  Sai Maliku yace "Ya Jagoran Muminai, kada kayi haka. Domin tuni mutane sun ji ruwayoyi daban-daban na Hadisai. Kuma kowanne rukuni mutane sun ɗoru da ayyukansu bisa abinda suka ji. Don haka kawar dasu daga abinda suke kai zai haifar da annoba a musulunci. A maimakon haka ka ƙyale mutane akan duk abinda suke kai da kuma duk abinda suka zaɓawa kansu".
Ance Imam Malik bai taɓa karanta Hadisin Annabi s.a.w ba batare da alwala ba, har ɗan uwansa Ismail bn Abi Uways ya faɗa cewar "na taɓa tambayar Kawuna Maliku a game da wani abu na ilimi, sai ya umarceni nayi alwala, sannan na zauna a gabansa, sannan nace , 'la hawla wala quwata illa billah'.. Bai taɓa bada wata fatawa ba tare da ambaton wannan kalma ba".
 Imam Maliku Yana da tsantseni da maida lamura ga Allah, kuma baya bada fatawa akan abinda bashi da cikakken sani akai.
   Imam Al-Haytham yace "na taɓa zama tare da Maliku a wata rana, inda aka tambaye shi wasu mas'aloli kimanin 40, ya amsa guda 8, amma sauran duk yana bada amsar su da faɗin Ban sani ba".
  An samu Imamu Maliku yana cewa "Kariyar Masani shine 'Ban sani ba'. Idan har ya guje ta, to kuwa zai rabauta da azabar mutuwa".
   A wani wajen kuma, Khālid ibn Khidāsh ya ruwaito cewa "Nayi doguwar tafiya daga Iraqi domin naga Imam Malik na tambayeshi wasu tambayoyi guda arbain. Amma dana haɗu dashi, guda biyar kaɗai ya amsa mini, sauran sai yace mini bai sani ba. Sannan sai yace 'Ibn Ijlan yana cewa idan malami ya tsallake kalmar ban sani ba, zai haɗu da azabar mutuwa'.
  Ibn Wahb ya ruwaito cewa naji Abdullah ibn Yazid ibn Hurmuz yana cewa dole ne malamai su naƙaltawa masu zama a tare dasu kalmar ban sani ba har sai ta zama ginshiƙinsu kuma garkuwa daga halaka.
  Imam Shafi'i ya faɗa akan Maliku cewa idan aka ambaci sunayen Malamai, sunan Maliku yana zamowa tamkar tauraro acikinsu.
  Imamu Maliku ya faɗa cewa bai soma zama domin bayar da fatawa ba a birnin Madina sai da malaman Madina 70 sukayi shaidar dacewar sa akan hakan.
   Shine marubucin hamshaƙin littafin nan
 Al-Muwatta' watau 'Karɓaɓɓe' ko 'Tabbatacce', wanda ke ƙunshe da ingantattun hadisan Annabi s.a.w da zantukan sahabbansa masu girma, ta waɗanda suka zo bayan su, da waɗanda suka biyo bayansu.
  Iman Malik ya faɗa akan littafinsa Muwattah cewar sai daya gabatar dashi ga Malaman Madina guda 70, kowannen su yana mai inganta shi (kulluhum wata ani alayh), don haka ya sanya masa suna 'Muwattah'.
  Imam Al-Bukhari ya faɗa cewar Mafi inganci bisa kowanne Silsilar hadisi itace wadda akace ta fito daga  "Malik, daga Nafi, daga Ibn 'Umar." Ance masanan hadisi suna kiran wannan salsala da suna 'zinariyar salsala' saboda darajar ta.
   Imam Malik ya shirya littafin al-Muwatta' acikin shekaru 40, inda da fari ya tsara littafin da hadisai dubu 10, kafin daga bisani ya ƙunƙunce shi zuwa hadisai dubu 2.
   Kamar dai sauran malaman Islam, Imam Malik mutum ne mai tausayi da tausasawa. Gashi da gaskiya gami da tsayawa don tabbatar da ita.
   Don haka a lokacin da Gwamnan Madina ya nemi tursasa mutane yin mubaya'a ga Halifan musulunci daga zuriyar Umayyawa Al Mansur, sai Imam Malik ya bada fatawa cewa wannan ɗaukar alƙawari yasasshe ne domin anyi shine bisa tursasa wa.
  Ya bada fatawar ne dogaron sa ga hadisin sakin aure, wanda Annabi yace duk wanda aka tursasa masa sakin matarsa to bata saku ba.
  Wannan ne sanadin da mafi yawan mutane suka samu ƙwarin guiwar bayyana matsayar su na ƙin goyon bayan Halifa Al Mansur, daga bisani mahukunta suka kama Imam Maliku tare da zartar masa da hukuncin bulala a bainar jama'a.
Allahu Akbar!.
   Mabiya Maliku ne suka samar da tafarkin Mazhabar Imamu Malik wadda ake hukunci da bada fatawowi bisa koyarwarsa, kuma wannan mazhaba ta watsu a ƙasashen Afirka, Andalus, Yemen, Sudan, Iraq, Khorasan da wasunsu.
  Imam Tirmizi ya ruwaito wani Hadisi da Manzon Allah s.a.w yake cewa a nan gaba kaɗan, mutane zasu rinƙa hawan bayan raƙuma suna bazama neman ilimi, kuma ba zasu samu wani masani ba sama da masanin Madina.
  Imam Qadi Ayyad, Imam Al-Zhahabi da wasu irinsu Sufyan ibn `Uyaynah, ‘Abd ar-Razzaq as-San'ani, Ibn Mahdi, Yahya ibn Ma'in, Zhu’ayb ibn `Imama, Ibn al-Madini,  da wasun su sun tafi akan cewar hadisin bushara ne da zuwan Imam Maliku.
  Ance Halifa Al Mansur ya taɓa tambayar Maliku 'shin ina yafi kamantuwa na fuskanta don yin addu'a tsakanin kabarin Annabi mai girma da alƙibla?'.
  Sai Maliku ya amsa masa da cewa "Me zaisa ba zaka fuskance shi ba (s.a.w) alhali shine mai sadar dakai ga Allah da kai da baban ka Adamu a ranar alƙiyama?"
   Imam Malik ya rasu a shekarar 796 miladiyya, hijirar ma'aiki 179 a birnin Madina, kuma an binne shi a maƙabartar Baƙi' a mai daraja
 
Kafin rasuwar Imam Maliku ya wallafa littafinsa 'Al Muwattah', wanda har Imam Shafi'i yake cewa shine littafi mafi inganci bayan Alƙurani mai girma.
  Sai kuma littafin 'Al-Mudawwana al-Kubra' wanda Mallam Suhnun ibn Sa'id ibn Habib at-Tanukhi ya tattara bayan rasuwar Malikun.
   Da fatan Allah ya gafarta masa, yayi masa rahama amin.


  Da fatan Allah ya jiƙansa amin

Sunday, 4 November 2018

TARIHI: ASALIN BAKIN MUTUM DA MAZAUNIN SA 8

TARIHI: ASALIN BAKIN MUTUM DA     MUHALLIN SA
   (fitowa ta takwas)

Daga SADIQ TUKUR GWARZO

Sai dai kuma, menene magana mafi inganci dangane da ainihin kabilun dake zaune a wannan yanki na Afirka?
   Hujjojin da aka samu a yanzu haka, sunfi karkata akan cewa duk wadansu kabilu da yaruka sun samo usuli ne daga manyan kabilu hudu da suka fara zama anan afirka.
   Yankin Libya dai, tun da jimawa akwai mutane a cikinsa. Jimawar na nufin shekaru dubu biyar kafin zuwan Annabi Isa A.S, kwatankwacin lokacin da Egypt ta soma samun mafarauta a dandamarin kasar ta.
   Lokacin da muke hasashen anyi ruwan d'ufana kenan an dauke, tunda abaya mun kawo yadda masani Robert Ballard yayi hasashen aukuwar ruwan dufana da cewar ya auku shekaru dubu bakwai da dari biyar da suka gabata.
   An bayyana kabilar Berber a matsayin kabilar data dade a wancan tsohon yanki na libiya. Amma kuma kabilu irinsu Nasamones, Aushiase, Asbytaeas, Garamantis, Macae, Gindanes, Lotuphagia, Machles da Auses duk sun auku a wancan yanki daga baya.
  Daga bayan ne kuma, kabilar Toureg, da wasu kabilu tsatson kabilun fulani suka samu wanzuwa daga can K'asa da kasar ta Libya. Yankin kasashen Morocco, Tunisia, Algeria da Mauritania kenan.
   Wad'annan mutanen duk fararen fata ne, asalin su daga tsohuwar kabilar Libya suka samu rassa.
  A baya-bayan nan kuma, ga tarihin kafuwar Daular Awkar (Ghana empire) a garin 'Koumbi Saleh' yankin kasar Mouritania tare da yadda ta taimaka wajen kafuwar garuruwan Tiraqqa, Tadmakka da Timbuktu dake yankin kasar Mali na bakaken fata.
   Sannan ga gusawar zuriyar tushen fulani daga kasar ta Mauritania izuwa 'Futa Toro dake Senegal da kuma 'Futa Djallon' dake yankin kasar Guinea gami da yadda suka kewayo yankin Gobir tare da mamaye kasar Hausa, duk kansu abin kulawa ne.
  Wadannan fa, duk sun isa 'yar manuniya akan yadda mutane ke matsawa daga nan zuwa can, da kuma yadda jinsi da al'ada ke rikedewa daga wannan zuwa wancan. Watakila, kimiyyar had'aka ce zata bamu amsar silar wannan haduwa. (Watau dai, duk inda aka ce abu kaza ya hadu da abu kaza, abu kaza yake bayar wa).
   Masanin tarihi Herodotus ya riski Egypt a wajajen shekara ta 460 kafin zuwan Annabi Isa A.S. Ga kuma abinda ya ruwaito a littafi na daya a game da kabilun dake afirka.
   "Da akwai kimanin garuruwa dubu ashirin masu dauke da mutane a yankin egypt... Al'ummar afirka ta kunshi kabilu biyu ne mazauna, watau Libiyawa da kuma Bakaken fata (Ethiopiyawa), da kuma Kabilu biyu bak'i, sune Girkawa da Sumeriyawa (Phoenicians)".
Ashe kenan, daga kafuwar egypt a wajajen shekara ta dubu biyar kafin aiko Annabi Isa A.S, izuwa shekara ta dari hudu da sittin kafin Aiko Annabi Isa A.S (shekaru dubu hudu da dari biyar da arba'in kenan), har garuruwa dubu ashirin sun kafu. Dai-dai kenan da muce duk bayan kimanin kwanaki 81, ko watanni uku, gari daya na samuwa a yankin.
  Sai dai gashi, bamu da alkaluman da zasu nuna mana adadin garuruwan da suka kafu a kasar bakin mutum ta ainihi, balle mu lissafa wanda yafi wani habaka a tsakani. Amma dai, hakan na nuna mana cewa kamar yadda dubunnan garuruwa suka wanzu a wancan gari da egypt bai kai tsufan sa ba, haka ma wasu garuruwan sun kafu a daular bakin mutum ta asali.
  Halayyar mutumin-da kuma ta matsawa daga nan zuwa can don kafa neman abin bukata tare da kafa gari ke tabbatar mana da kafuwar garuruwa mabambanta.
  Tunda ana maganar garin Mazaber ne dake yankin Erithrea asalin gari. A hankali tarihi ya nuna yadda aka rinka fadada izuwa kasar Ethiopia, Somalia har akazo Sudan. ( Kasar da kasar Chadi ce kadai ta raba Nigeria da ita).
   Kuma gashi acan ma, daga Libya aka soma, amma sai da farin mutum ya fantsama kasashen Arewacin afirka kamar yadda muka fada a sama.   Tabbas, alamomi sun tabbata cewar bakin mutum ya gangaro ne daga ainihin mazaunin sa izuwa makotan ainihin cibiyar sa misalin kasashen afirka ta yamma, kamar yadda itama wayewa, al'adu da salon sarrafa harshe suka gangaro gareshi sannu-a-hankali...

TARIHIN TSOHON BIRNI GANGARA DAKE KASAR KATSINA

TARIHIN TSOHON BIRNIN GANGARA DA YADDA GARIN MALUMFASHI YA FITO DAGA GARESHI.

SADIQ TUKUR GWARZO
 Kirarin Garin: Gangara Ta Naturɓe, idan kaji ina kwana bako ne.. Sai dai Nyalli Jam.
Wannan gari tsoho ne, jimawarsa kuma har takai wasu na ganin ya girmewa tsoffin birane misalin Malumfashi, Getso, Baɗari da birnin Kano.
   Fulani kabilar Natirawa ne akace suka kafa garin lokaci mai tsawo daya shuɗe, sannan labari na gaskiya ya dusashe dangane da tsohon birnin, ko kuma lokacin kafuwarsa, wanda a yanzu ya zama kufai, amma dai zuwa yanzu an iya gane sashen ganuwar tsohon birnin. Haka kuma marinar garin da tsoffin kukoki nanan a inda tsohuwar rayuwar Natirawan ta auku shekaru ɗaruruwa da suka gabata.
  Babban limamin Garin mai suna Mallam Adamu, ya bayyana mana cewar an samo sunan garin 'Gangara' ne daga kalmar 'Gagara', ko kuma ace garin daya Gagara acishi da yaki, domin tunda wannan birni yake babu wani sarki daya taɓa cinsa da yaki.
  An samu cewa garin Gangara na usuli shahararre ne, mai zagaye da ganuwa, mai ɗauke da tarin mutane kuma. Mutane na zuwa fatauci daga sassa daban daban na kasar hausa. Har ma ance akwai zamanin da saida gidaje suka cika birnin, har ma wasun suka rinka yin gidaje a bayan ganuwa.
  Sannan kasancewar garin na fulani ne, akwai tsohuwar al'adar nan ta sharo da kuma wankan amarya da aka ruwaito tana wakana tsakankanin mazauna birnin, amma dai ance musulunci ya samu karɓuwa tun kafin zuwan Mujaddadi Usmanu ɗan fodio, don haka abubuwa irin na maguzanci basu yawaitaba.
  A batun yake-yake, garin Gangara yayi zarra, tunda ance akwai wani K'aton kada mai suna 'Nabogaji' wanda yake cikin wani tafki dake kusa da garin, wanda kuma yake rura kuka yayin da wani bala'i ya tunkaro garin domin sanar da mazauna birnin suyi shiri.
  Dukkan maruwaitan tarihin garin Gangara sun haɗu akan cewa babu wanda ya taɓa cinye garin da yaki. Wasu sunce da zarar Nabogaji yayi ruri, sai idanuwan mahara ya rufe, ya zamo basa iya ganin birnin da abinda ke cikinsa. Yayinda wasu ke ganin tsabar jarumtar sadaukan birnin ke basu ikon mayar da keyar mahara baya.
  Ance Gangara ta taɓa kaiwa garin Getso hari, taci nasara akan garin, har saida ta kori maza da mata dake garin.
  Haka kuma gangara tayi yaki da garuruwan matazu, kurkujan na musawa, da malumfashi a baya-bayan nan, kuma duk ta samu nasara.
  Liman Mallam Adamu ya faɗa mana cewar asalin garin malumfashi Gangara ne. Domin kuwa zamani mai tsawo daya wuce, an taɓa yin wata annoba ta ciwon ciki wadda mutanen birnin Gangara suka rinka mutuwa.
  Don haka sai mutanen suka tashi izuwa gefensa suka kafa  sabon gari, yayinda waɗansu suka fantsama sassan duniya.
  To ance daga irin waɗannan mutanen ne wani banatire mai suna Dano (ko Dunu ) ya riski garin malumfashi a lokacin yana jeji. Sai ya sauka sannan ya sari gona domin yaɗan taɓa noma.
  Da amfanin gona yazo, sai ya zamana ya samu alheri, don haka ya shiga godiya ga mai sama yana faɗin "Yanzu Na-numfasa"
  Daga nan kuma sai labari ya iso garinsu Gangara, inda mutane suka rinka tafiya inda yake da zummar suje suyi noma su samu riba da kuɓuta daga waccan annoba. Don haka sai suma suka rinka cewa "zamu tafi inda Dano yake Munumfasa" watau mu huta daga wannan annobar. Daga baya aka maida sunan garin ya koma 'mulumfashi' ko 'Malumfashi'.
  A cewar Liman, babbar hujja akan haka shine unguwar Gangarawa dake garin malumfashi. Wadda babu wata tsohuwar unguwa data girme mata.
  Sunan sarautar garin Gangara shune 'ɗan-saka', ance ta samu ne daga wani sarkinta mai sakawa duk waɓda aka yiwa zalunci daga talakawansa. Hak kuma kasancewar sunayen tsoffin sarakunanta sun ɓata, amma dai an samu cewar a baya bayan nan sarakuna irinsu:-
Dan saka Atiku, Dan saka Babba, Dan saka Nani, Dan saka Isiye, Dan saka Bello zarɓe magajin tunkuɗa, ɗan saka sarki ya-musa, ɗan saka yuguda, da ɗan saka muhammadu magajin daɗi duk sun mulketa, sai kuma dagacin dake mulkinta ayau mai suna Magaji Alh Bala ɗan muhammadi majidaɗi.
   Koda yake, ance yanzu sarautar ɗansaka ta koma garin Gora bisa tashin tsohom ɗan saka Muhammadu majidaɗi daga Gangara zuwa garin na Gora saboda tsangwamar natirawa, don haka da aka turo ɗansa sai ake masa lakabi da Magaji. Saboda hak yanzu sunan sarautar garin 'Magaji'.
  Sannan kuma har gobe mutanen garin Gangara suna fahari da cewar Mujaddadi Shehu Usmanu ya sauka a garin akan hanyarsa ta zuwa kano daga sokoto, harma ya sahale aka soma sallar juma'a a garin, a lokacin da duk yamma da kano daga Rimin Gado, sai malumfashi ake zuwa yin sallar jumu'a...
   Zuwa yanzu dai, garin yana nan a kusa da garin Dayi, kuma yana karkashin karamar hukumar malumfashi ne ta jihar katsinan Nigeria.