TARIHI: ASALIN BAKIN MUTUM DA MUHALLIN SA
(fitowa ta takwas)
Daga SADIQ TUKUR GWARZO
Sai dai kuma, menene magana mafi inganci dangane da ainihin kabilun dake zaune a wannan yanki na Afirka?
Hujjojin da aka samu a yanzu haka, sunfi karkata akan cewa duk wadansu kabilu da yaruka sun samo usuli ne daga manyan kabilu hudu da suka fara zama anan afirka.
Yankin Libya dai, tun da jimawa akwai mutane a cikinsa. Jimawar na nufin shekaru dubu biyar kafin zuwan Annabi Isa A.S, kwatankwacin lokacin da Egypt ta soma samun mafarauta a dandamarin kasar ta.
Lokacin da muke hasashen anyi ruwan d'ufana kenan an dauke, tunda abaya mun kawo yadda masani Robert Ballard yayi hasashen aukuwar ruwan dufana da cewar ya auku shekaru dubu bakwai da dari biyar da suka gabata.
An bayyana kabilar Berber a matsayin kabilar data dade a wancan tsohon yanki na libiya. Amma kuma kabilu irinsu Nasamones, Aushiase, Asbytaeas, Garamantis, Macae, Gindanes, Lotuphagia, Machles da Auses duk sun auku a wancan yanki daga baya.
Daga bayan ne kuma, kabilar Toureg, da wasu kabilu tsatson kabilun fulani suka samu wanzuwa daga can K'asa da kasar ta Libya. Yankin kasashen Morocco, Tunisia, Algeria da Mauritania kenan.
Wad'annan mutanen duk fararen fata ne, asalin su daga tsohuwar kabilar Libya suka samu rassa.
A baya-bayan nan kuma, ga tarihin kafuwar Daular Awkar (Ghana empire) a garin 'Koumbi Saleh' yankin kasar Mouritania tare da yadda ta taimaka wajen kafuwar garuruwan Tiraqqa, Tadmakka da Timbuktu dake yankin kasar Mali na bakaken fata.
Sannan ga gusawar zuriyar tushen fulani daga kasar ta Mauritania izuwa 'Futa Toro dake Senegal da kuma 'Futa Djallon' dake yankin kasar Guinea gami da yadda suka kewayo yankin Gobir tare da mamaye kasar Hausa, duk kansu abin kulawa ne.
Wadannan fa, duk sun isa 'yar manuniya akan yadda mutane ke matsawa daga nan zuwa can, da kuma yadda jinsi da al'ada ke rikedewa daga wannan zuwa wancan. Watakila, kimiyyar had'aka ce zata bamu amsar silar wannan haduwa. (Watau dai, duk inda aka ce abu kaza ya hadu da abu kaza, abu kaza yake bayar wa).
Masanin tarihi Herodotus ya riski Egypt a wajajen shekara ta 460 kafin zuwan Annabi Isa A.S. Ga kuma abinda ya ruwaito a littafi na daya a game da kabilun dake afirka.
"Da akwai kimanin garuruwa dubu ashirin masu dauke da mutane a yankin egypt... Al'ummar afirka ta kunshi kabilu biyu ne mazauna, watau Libiyawa da kuma Bakaken fata (Ethiopiyawa), da kuma Kabilu biyu bak'i, sune Girkawa da Sumeriyawa (Phoenicians)".
Ashe kenan, daga kafuwar egypt a wajajen shekara ta dubu biyar kafin aiko Annabi Isa A.S, izuwa shekara ta dari hudu da sittin kafin Aiko Annabi Isa A.S (shekaru dubu hudu da dari biyar da arba'in kenan), har garuruwa dubu ashirin sun kafu. Dai-dai kenan da muce duk bayan kimanin kwanaki 81, ko watanni uku, gari daya na samuwa a yankin.
Sai dai gashi, bamu da alkaluman da zasu nuna mana adadin garuruwan da suka kafu a kasar bakin mutum ta ainihi, balle mu lissafa wanda yafi wani habaka a tsakani. Amma dai, hakan na nuna mana cewa kamar yadda dubunnan garuruwa suka wanzu a wancan gari da egypt bai kai tsufan sa ba, haka ma wasu garuruwan sun kafu a daular bakin mutum ta asali.
Halayyar mutumin-da kuma ta matsawa daga nan zuwa can don kafa neman abin bukata tare da kafa gari ke tabbatar mana da kafuwar garuruwa mabambanta.
Tunda ana maganar garin Mazaber ne dake yankin Erithrea asalin gari. A hankali tarihi ya nuna yadda aka rinka fadada izuwa kasar Ethiopia, Somalia har akazo Sudan. ( Kasar da kasar Chadi ce kadai ta raba Nigeria da ita).
Kuma gashi acan ma, daga Libya aka soma, amma sai da farin mutum ya fantsama kasashen Arewacin afirka kamar yadda muka fada a sama. Tabbas, alamomi sun tabbata cewar bakin mutum ya gangaro ne daga ainihin mazaunin sa izuwa makotan ainihin cibiyar sa misalin kasashen afirka ta yamma, kamar yadda itama wayewa, al'adu da salon sarrafa harshe suka gangaro gareshi sannu-a-hankali...

No comments:
Post a Comment