Assalamu alaikum.
Hanyoyin da ake samun kudi a yanar gizo;-
Article writer
A wannan fannin, mutum yana iya zama mai rubuce-rubuce ga jaridu, qasidu ko wasu gurare na dab`I na duniya, inda zasu nemi ka rinqa rubuta musu sharshi kan al`amuran yau da kullum da suka shafi siyasar duniya ko ta qasashe, ko kuma rubutu kan kasuwanci da yadda za`a habaka kasuwanci, ko rubutun daya kebanci soyayya, ma`aurata da yarda za`a zauna lafiya da juna, dama sauran dumbin fannoni wadanda mutane suke zumudin karantawa idan sun ganshi.
Mai sha`awar wannin fannin, babu wata wahala, kawai abinda zaiyi shine, yayi tunani a karan kansa wane fanni yake da gogewa, inda zai rinqa yin rubuce-rubuce mai qayatarwa da jan hankali, zai kuma tabbata zaiy iya kiyayewa da qa`idojin rubutu na harshen turanci, daga nan sai ya ziyarci search engine kamar google a adireshinsu www.google.com, idan shafin ya bude, sai ya binciko qasida, ko jaridar da suka kebanci irin abinda yake da kwarewa akansa. Idan yafi kwarancewa akan rubutun daya shafi siyasa, kai tsaye qasidun siyasa zai bincika.
Idan har kayi haka, zai samu shafuka masu tarin yawa na qasidu(magazines), da jaridu na dunya, daga nan sai ka zabi wadda ta kwanta masa, ka ziyarci shafin jaridar ta hanyar kilikin akan adireshinta, sai ka karanta irin abubuwan da jaridar ko qasidar suke bugawa wadanda mutane irinka ke turo musu, daga nan sai ka tuntubi editan jaridar ko qasidar. A wannan gabar ne editan zai so yasan wanene kai, yasan kwalin rubutun ka da kuma abinda kake ganin zaka iya yi musu rubutu akai tare da tura wani samfuri na rubutun da ka tabayi. Indai mutum yabi qa`idoji daki-daki, zai samu gurbin yin rubuce-rubuce, inda za`a rinqa biyansa a mako ko a sati ko kuma duk rubutun daya gudanar.
YADDA MUTUM ZAI IYA YIN RUBUTU GA SHAFUKAN YANAR GIZO A BIYA SHI
Kamar yadda nake tunanin wasu suna da masaniya, yanar gizo ba ma`asumiya bace wadda ake yi mata wahayi daga sama, duk tulin bayanan da muke gani yau da kullum da suka shafi fannoni da dama na rayuwa da har wasu ke ikirarin duk abin da ka nema a yanar gizo zaka samu, to mutane ne mahaluqai suka dauki gabarar rubutawa. Wasu sun rubuta ne a matsayin (blog) kuma a kyauta, wasu kuma sun rubuta an biyasu. Don haka kai ma kana iya yin irin wadannan rubuce-rubuce a shafukan yanar gizo a fannin da ka sani. Domin yin haka, zaka iya ziyartar:-
www.getafreelancer.com
www.freelancewriting.com
wadannan adireshoshi suna da ban mamaki, aikin su kamar yankan wuqa( ta bakin mata) haka yake. Kawai abin da zakayi shine, ka ziyarci daya daga adireshin sannan kayi sign up, zasu nemi ka fada musu fanning da kake rubutu akai tare da tura musu samfurin rubutun da ka taba yi.
www.debthelp.tu
wannan shafin yana da wuya kafin su amince zaka rinqa yi musu rubutu, amma da zarar sun amince da ingancin ka, zasu baka dama ka rinqa yi musu rubutu suna biyanka $20 dala ashirin a duk rubutu. Idan kullum zaka rinqa yi ba zasu damu ba wajen baka kudin ka a kullum.
www.epinions.com
wannan ma wani shafi ne mai ban mamaki, ana samun kudi matuqa ga masu wayo. Yuadda akeyi shine idan kayi rijista dasu, zaka rinqa rubuta musu ra`ayinka ne akan kayayyakin su (products), duk wanda yayi kilik akan wannan ra`ayin naka, zaka samu kudi. Don haka anan ana yin ramuwar kura, idan kayi wa wani kilik, shima sai yayi maka, amma idan kana tunanin zaka rinqa yiwa kanka kilik, tofa wayon su ya isa, duk kilik da kayiwa kanka da kanka sai sun zaftare maka kudin da ka samu. Adsence ma haka yake.
www.articlemarket.com
www.ehow.com
da sauransu.
YADDA MUTUM ZAI SAYAR DA HOTUNA A YANAR GIZO-GIZO
Wataqila wannan ya bawa wasu mamaki, amma a yanzu yanar gizo tayi bunqasar da kome kake dashi, kome ka sani kuma koda ilimin kora jaki ne, zaka iya samun kudi dashi domin wani yana can yana neman irin wannan abinda kai ka sani din. Don haka zaka iya zama mai daukar hoto na mutane, dabbobi, fulawowi da sauransu, ka sayar a yanar fizo.
Shafukan da ake sayan hoto ko a siyar sun hadar da:-
www.photoprofit.com
www.dreamtime.com
www.stockphoto.com
www.fotolia.com
www.freeimages.com
Idan kuma mutum yana sha`awar siye-siye ne a yanar gizo, indai ya mallaki daya daga cikin katuna masu kama da katin ATM, sai ya ziyarci daya daga cikin manyan shagunan yanar gizo, inda zai siyi kaya a kawo masa har gida cikin rahusa. Adireshin shagunan sune:-
www.amazon.com
www.ebay.com
Anan nake ganin zan jingine wannan fanning, amma cikin ikon Allah a gab azan tabo wasu bangarorin. Ina fata yan uwana zasuci moriyarsa.
Daga Sadiq Tukur Gwarzo.
08060869978
tnk amma inaso nasan yanda zanbude shafina a internet
ReplyDelete