Monday, 27 September 2021

ASALIN KAFUWAR GAYA

 ASALIN GAYA


(Tsakure)



SADIQ TUKUR GWARZO



Marigayi Maje Ahmad Gwangwazo ya kawo a littafinsa 'Tarihin Kano kafin Jihadi' cewa asalin garuruwan Kano, Gaya da Rano ya samu ne daga wasu mutane uku waɗanda suka yiwo balaguro tare da ahalin su daga ƙasar Habasha tare da ƴanuwansu Maguzawa. 

Sunayen waɗannan mutane kuma jagororin tawagar sune Ranau, Gayya da Dala, kuma sun yiwo wannan balaguron ne tun kafin haihuwar Annabi Isa A.S. (shekaru sama da dubu biyu da suka gabata kenan).

  A cewar marubucin, Ranau ne ya soma zama a garin Rano, kuma daga gareshi aka samar da sunan Rano, Dala ne ya soma zama akan dutsen Dala na kano, kuma daga gareshi aka samar da sunan dutsen Dala, haka kuma Gayya ne ya soma zama a inda garin Gaya yake a yanzu kuma daga gareshi aka samar da sunan Garin Gaya.

Masana irin su marigayi Alh Maitama Sule Ɗanmasanin kano da wasun sa duk sun haɗu akan cewa tabbas asalin (Hausawa) mutanen Gaya daga Habasha suke, kuma shi kansa wani shahararren mutum wanda aka ce daga sunan sa aka samo sunan garin Kano mai suna 'Kano maƙeri', daga garin Gaya yake. Har ma sun ƙara da cewa Bagauda wanda tarihi ya kiyaye a matsayin sarkin Kano na farko shima ɗan garin Gaya ne.

Amma a wasu zantukan na tarihi musamman waɗanda suka fito daga garin Gaya, an samo wani abu mabanbanci da wannan game da asalin kafuwar Gaya.

  Tarihin ya tafi akan cewa zamani mai tsawo da ya gabata, inda garin Gaya yake a yanzu jeji ne mai cike da albarkatun namun daji.

  Akan haka wani mafarauci da ake kira da suna Bagauda tare da ɗanuwan sa mai suna Gayya, suka ruski wajen tare da zama a inda garin Gaya yake a yanzu. Bagauda ya kafa rumfar sa a wani waje da har zuwa yanzu ake kira da suna 'unguwar Bagauda'. Ya zama nan ne makwancin sa, a kullum ya kan shiga daji yayi farautar namun daji sannan ya dawo rumfar sa ya sarrafa.

   Sannu a hankali sai mutane musamman ƴanuwan sa mafarauta suka fara riskar wajen tare da kafa rumfunan su na kwana. Kwanci tashi albarka na ƙaruwa, mutane na ƙara kwarorowa, daga mafarauta zuwa manoma, zuwa maƙera, zuwa matafiya masu shigewa zuwa Borno, da dai sauran masu sana'o'i daban-daban. Wannan kuma shine asalin yadda aka kafa garin Gaya.

  Game da yadda aka samo wannan suna na Gaya, an samu zantuka guda biyu.

  Na farko an faɗa cewa jim kaɗan da soma kafuwar garin Gaya a wancan lokaci, sai Bagauda ya ɗaura niyya tare da barin garin. Daga nan yayi yamma yana tafiya cikin dazuka gaminda farautar namun daji a hanya. Akan haka ya je ya sari wani gari da ake kira ƴar Gaya, sannan kuma da ya ƙara tashi, bai sauka ba  sai a inda garin kano ya ke a yanzu. A wancan lokacin ne ya sari kano.

  Littafin tarihin kafuwar kano kuwa 'kano chronicle' ya sanya cewar Bagauda shine sarkin kano na farko, kuma ya soma mulki ne a shekara ta 999 A.D.

  Wanda Bagauda ya bari a Gaya shine ɗan uwansa Gayya wanda suka riski wajen tare, don haka shine ya zamo jagoran mutanen da suka cigaba da zama a wurin, kuma daga sunan sa 'Gaya' ta samo asali.

Zance na biyu kuwa ya tafi akan cewa sunan Gaya ya samo asali ne daga wani jagora da aka taɓa yi a farko-farkon garin (ko Gayya ko kuma sarki na farko mai suna Sarki Kwalo). 

Ance wannan jagora yana da kyauta da haba-haba da mutane. Ya kasance duk baƙon da ya isa gareshi sai ya samu wani abu na alheri yayi masa. 

Akan haka ya kasance idan wasu suka ziyarce shi alhali ya gama rabar da abubuwan da yake dasu ga masu ziyartar sa,  maimakon ya barsu haka nan ba tare da ya basu komai ba sai yace " sai hakuri, babu abinci, babu nono, sai dai gaya".

Sai ya ɗauko gayan ya bayar.

Don haka sai mutane ke kiran sa da suna 'mai gaya'. Kuma daga gare shi sunan Gaya ta samo asali...

Sunday, 26 September 2021

FALSAFAR MUTUWA

 MUTUWA


SADIQ TUKUR GWARZO


Ubangiji Ta'ala ya faɗa a littafin sa Alqur'ani mai girma cewa 

 كُلُّ نَفْسٍ ذَائِقَةُ الْمَوْتِ  

3:185

Ma'ana, dukkan rai sai ta ɗanɗana mutuwa.

   Tabbas, mutuwa aba ce wajiba ga dukkan wani rai da aka busa mata numfashi.

  Masana falsafa sun haɗu akan cewa mutuwa na nufin tafiyar ruhi zuwa barzahu; watau zuwa rayuwa bayan mutuwa. 

  Shikuwa mutum yana ɗauke ne da ruhi da kuma gangar jiki. Ruhi kuma shine kamar 'software' mai rayar da gangar jiki 'hardware' a ilimin na'ura mai ƙwaƙwalwa.

  Don haka mutuwa na nufin raba ruhi da gangar jiki. Kuma da zarar rabuwar ta kasance, sai ruhi ya soma tafiya zuwa sama.

Wannan kuwa wata tafiya ce da Allah ya ƙadartawa ruhi, wadda ta zarar an ɗauke shi daga nan duniya sai a tafi dashi zuwa wata duniyar wadda aka tanadarwa masu irin aiyukan da ya aikata alhali yana cikin gangar jiki a wannan duniyar tamu, walau ayyuka na alheri ko na akasin haka. 

Haka zai cigaba da rayuwa har kuma lokacin da Ubangiji zai hukunta sake tayar da rayayyu domin yin hisabi.

  Haka nan, wani lokacin Allah yana yiwa wasu daga bayin sa nuni da ƙaratowar ajalin su, ta yadda za a ga sun sabunta alaƙantuwar su ga Ubangiji maɗaukakin Sarki, tare da riƙo da wasu ayyuka masu kusantar da bayi ga Allah.

  Hakika mun ga irin haka ga rayuwar magabata musamman masana ilimin falsafanci irin su Imam Muhammad Ibn Sina, wanda duk da kasancewar sa likita kuma marubucin Qanun fiɗ ɗibb, amma yayi biris da yiwa kansa magani.. a lokacin mutuwa kawai yake hange, kuma ita yake marari..

  A wani ƙadamin kuma mutuwa ta kan zowa wasu bagatatan ba tare da aune ko ankararwa ba. An ga irin hakanga mutane da dama, waɗanda suka mutu alhalinsuna cikin wani sha'ani, kuma suna masu cike da burikan rayuwa.

  Hakika, ga wanda duk yasan ilimin mutuwa ya isheshi tsarkake buwayar Allah maɗaujakin sarki. 

A ƙarshe, yana da kyau mubsani, babu wata tabbatacciyar alama ga mutuwa. Ita tana iya zuwa da dalili, tana kuma iya zuwa babu gaira babu dalili.

  Domin shiryawa mutuwa, yana da kyau mutum ya kasance a kullum ayyukan sa na alheri sufi na akasin su yawa, domin haƙiƙa ayyukan mu na da tasiri ga halin da zamu tsincinkawunan mu bayan mutuwa.

  Dafatan Allah ya jiƙan mu amin