Sunday, 26 September 2021

FALSAFAR MUTUWA

 MUTUWA


SADIQ TUKUR GWARZO


Ubangiji Ta'ala ya faɗa a littafin sa Alqur'ani mai girma cewa 

 كُلُّ نَفْسٍ ذَائِقَةُ الْمَوْتِ  

3:185

Ma'ana, dukkan rai sai ta ɗanɗana mutuwa.

   Tabbas, mutuwa aba ce wajiba ga dukkan wani rai da aka busa mata numfashi.

  Masana falsafa sun haɗu akan cewa mutuwa na nufin tafiyar ruhi zuwa barzahu; watau zuwa rayuwa bayan mutuwa. 

  Shikuwa mutum yana ɗauke ne da ruhi da kuma gangar jiki. Ruhi kuma shine kamar 'software' mai rayar da gangar jiki 'hardware' a ilimin na'ura mai ƙwaƙwalwa.

  Don haka mutuwa na nufin raba ruhi da gangar jiki. Kuma da zarar rabuwar ta kasance, sai ruhi ya soma tafiya zuwa sama.

Wannan kuwa wata tafiya ce da Allah ya ƙadartawa ruhi, wadda ta zarar an ɗauke shi daga nan duniya sai a tafi dashi zuwa wata duniyar wadda aka tanadarwa masu irin aiyukan da ya aikata alhali yana cikin gangar jiki a wannan duniyar tamu, walau ayyuka na alheri ko na akasin haka. 

Haka zai cigaba da rayuwa har kuma lokacin da Ubangiji zai hukunta sake tayar da rayayyu domin yin hisabi.

  Haka nan, wani lokacin Allah yana yiwa wasu daga bayin sa nuni da ƙaratowar ajalin su, ta yadda za a ga sun sabunta alaƙantuwar su ga Ubangiji maɗaukakin Sarki, tare da riƙo da wasu ayyuka masu kusantar da bayi ga Allah.

  Hakika mun ga irin haka ga rayuwar magabata musamman masana ilimin falsafanci irin su Imam Muhammad Ibn Sina, wanda duk da kasancewar sa likita kuma marubucin Qanun fiɗ ɗibb, amma yayi biris da yiwa kansa magani.. a lokacin mutuwa kawai yake hange, kuma ita yake marari..

  A wani ƙadamin kuma mutuwa ta kan zowa wasu bagatatan ba tare da aune ko ankararwa ba. An ga irin hakanga mutane da dama, waɗanda suka mutu alhalinsuna cikin wani sha'ani, kuma suna masu cike da burikan rayuwa.

  Hakika, ga wanda duk yasan ilimin mutuwa ya isheshi tsarkake buwayar Allah maɗaujakin sarki. 

A ƙarshe, yana da kyau mubsani, babu wata tabbatacciyar alama ga mutuwa. Ita tana iya zuwa da dalili, tana kuma iya zuwa babu gaira babu dalili.

  Domin shiryawa mutuwa, yana da kyau mutum ya kasance a kullum ayyukan sa na alheri sufi na akasin su yawa, domin haƙiƙa ayyukan mu na da tasiri ga halin da zamu tsincinkawunan mu bayan mutuwa.

  Dafatan Allah ya jiƙan mu amin

No comments:

Post a Comment