Sunday, 31 July 2022

HANYAR KANO: TARIHIN DA KE GURIN GAWA

 HANYAR KANO: TARIHIN DA KE GURIN GAWA


SADIQ TUKUR GWARZO

Kamar yadda marubutan littafin 'Urban Society ' Gist da Halbert suka faɗa, kuma kamar yadda yake game da asalin ita kanta Wayewar, tushen kowanne birni kusan ya samo asali ne daga hijirar mutanen ƙauyuka.

Birane sune cibiyar hadar-hadar kasuwanci, tsaro, al'adu, ilimi da bincike. Don haka ya sanya mutanen karkara na kusa da na nesa, da ma wasu mutanen da ke wasu biranen da dama kan ziyarci birane domin samun mafakar tsaro, ko kasuwanci, ko samun ilimi ko cimma wani dalili na al'ada da ma sauran muradai walau ziyarar ta kasance ta wucin gadi ko kuma ta-din-din-din. 

  Akwai ilimin tarihi mai yawa da mukan rasa yayin kawar da kawunan mu ga tafarkan da suke sadar da mutane zuwa waɗancan birane. Wannan kuwa ya haɗar da tarihin wasu muhimman abubuwa da aka taɓa yi ko kuma muhimman wurare masu dangantaka da biranen kansu.

Sau tari a ƙasar Hausa mutane kan niƙi gari domin ziyartar wani birni amma sai su shantake a wasu wurare na kusa ko na nesa da biranen bisa wasu dalilai. Haka kuma a wasu lokutan, sauyawar yanayai kan tursasa mutanen cikin birane komawa makusanta ko manesantan garuruwa ko birane da zama.

 Garin Gurin Gawa na ɗaya daga cikin ƙauyukan da suka kafu a turbar kano. Hasashe ya nuna cewar mabanbantan mutane da akasarin su ƴan tafarki ne suka kafa garin tsawon lokaci da ya shuɗe. Garin yana kudu da garin kano, akan turbar da zata shigar da mutum birnin kano ta ƙofar Ɗan Agundi (wadda aka sara a wajajen shekarar 1499AD). Don haka duk mutanen da suke son shiga kano daga yankunan Rano, Jos, sassan ƙasar Bauchi da makamantan su sai sun bi ta wannan turba.

ASALIN SUNAN GURIN GAWA

Akwai mabanbantan zantuka game da asalin sunan Gurin Gawa.

1. Na ɗaya: Gurin Gawa daga Gurin Gawarwaki. Ance an samo sunan ne daga kasancewar wurin filin daga. Watau a zamanin yaƙi, da zarar kano ta samu labarin an tunkaro ta da yaƙi ta wannan shiyya, sai ta turo dakarunta ta jibge su a wannan wuri. Don haka anan za a fafata yaƙi, anan kuma za a samu tulin gawarwaki bayan ƙarewar yaƙi. 

2. Na biyu: Gurin Gawa daga 'Gurin-Ge'

Wannan ra'ayin yana cewa an samu sunan ne daga wani Bafillatani mai suna Gurin-ge, wanda kiwo ya biyo dashi ta wajen har kuma dabbobin sa suka gano masa wani kwarmin ruwa, don haka ya mayar da wajen mazaunin sa, daga bisani ƴanuwansa fulani suka riƙa riskar sa da zama.

3. Na uku: Gurin gawa daga Gurin da aka samu  gawar Kuyangar Sarkin Rano

Ance akwai wani rafi tsakanin Medile da Gurin Gawa wanda ake kira 'Ci-kuyangi', saboda yadda yayi silar mutuwar kuyangi da dama a ciki har da wata amintacciyar kuyangar Sarkin Rano wadda ta rasu a wurin akan hanyarta ta shiga Kano, ance daga nan aka samo sunan na Gurin Gawa.

  Zuwa yanzu, garin ya kasu kashi biyu, akwai Ruga inda fulani masu sarautar garin suke, da kuma ɓangaren Hausawa inda ake kira Dausayi. Anan ne mahaifiyar shahararren masani marigayi Sheikh Nasir Kabara ta ke.

TASIRIN SHAHARAR KANO GA SAURAN MAKUSANTAN GARURUWA

 Kasancewar birnin Kano birnin kasuwanci ne ba birnin Siyasa ba, ya samu ɗaukaka tsawon lokaci saboda yadda fatake ke tururuwar zuwa gare shi bisa dalilan kasuwanci. Wannan ya taimakawa birnin wajen zamowa shahararre, shahararsa kuwa ta yi tasiri ga makusantan ƙauyuka wajen karɓar baƙi a ko-da-yaushe, da kuma hada-hadar kasuwanci.

Kamar yadda aka sani, a baya babu tsarikan otal ko masaukai a ƙasar Hausa, sannan akan rufe ƙofofin shiga birane  idan dare yayi. Saboda haka, matafiya a zamanin baya sukan samu waje da suka aminta da amincin sa su yada zango idan dare yayi kafin su ƙarasa cikin birni. Don haka kafuwar ƙauyuka a kusa da birane kan zamo masaukai ga baƙin da suke haramar shiga kano yayin da dare yayi musu.

 A irin haka ne aka samu wani mutumi daga ƙasar Bade ta cikin jihar Yobe a yanzu haka ya yada zango a Gurin Gawa tare da soma sana'ar Kwarami (awo), inda ya samu shahara a wannan sana'ar, ya rinƙa sauƙaƙawa fatake masu zuwa kano da jakuna siyan hatsi da kuma masu fitowa daga kano neman haja ba tare da sunyi dogon zango ba. (Har yanzu ana yiwa mazaunin wancan babarbare laƙabi da suna 'Marken Bade').

  A ƙarshe, ina da ra'ayin cewar muhimmancin buƙatar bibiyar tarihin manyan tafarkan da suke sadarwa zuwa biranen mu tamkar na sanin tarihin biranen ne.

HANYAR KANO: TARIHIN RIMIN GADO

 HANYAR KANO: TARIHIN RIMIN GADO


SADIQ TUKUR GWARZO


Akan yiwa garin Rimin Gado kirari da cewa "Rimin Gado garin ƴan lalle", silar hakan kuwa shine, Allah ya baiwa garin yalwa ta bishiyoyin lalle, wanda a zamanin baya ya kasance itace mai daraja wanda mutane ke rububin neman sa domin yin amfani da shi a matsayin sinadarin tsaftace jiki da magani da sauran su.

 Wannan gari, a zamanin baya, ya zamo kasuwa matattarar fatake inda mutane ke niƙo gari daga mabanbantan sassa domin siyen lalle da sauran hajoji.

A binciken da Mallam Muhuyi Magaji Rimin Gado yayi, ya sanya kafuwar garin Rimin Gado da kimanin shekaru 300 da suka gabata. Kafin zamowar Rimin Gado gari, inda Rimin Gado yake a yanzu ya kasance (zango ne) wurin saukar matafiya ne masu kara-kaina tsakan-kanin birnin Kano da biranen da ke yamma da ita misalin Sokoto.

  KAFUWAR RIMIN GADO

Ance akwai wani mutum mai suna Magili, mabaraci ne, wanda ya taso daga Degel; wani ɗan ƙaramin gari dake jamhuriyar Nijar ayau zuwa inda garin Rimin Gado ya ke, don haka ana iya cewa shine asalin kafuwar wannan gari.

Bisa al'ada ta mabarata, sukan samu gefen turbar da mutane ke shigewa su fake suna addua ko zikirai ko waƙoƙin nasiha ga matafiya da makamantansu da nufin neman sadaka daga masu shigewa. Magili ya gina gadon ƙasa a inda garin Rimin Gado ya ke a yanzu, a gefen turbar da matafiya ke wucewa zuwa birnin Kano, akan wannan gado yake zama yana bara a ko-da yaushe.

ASALIN SUNAN RIMIN GADO

Ance Magili,  wanda yake zama akan gadon da ya gina na turɓaya yana bara da rana sai kuma ya kwanta bacci idan dare yayi, ya samo ƙwanson Rimi da ya tattara a matsayin matashin kai wanda yake ɗora kansa yayin bacci. A kwana a tashi sai ƴaƴan rimin da ke cikin ƙwanson ya rinƙa zuba daga gadon nasa zuwa ƙasa, har kuma aka yi sa a tsiron bishiyar rimi ya fito a wajen wanda daga bisani ya girma ya zama bishiya gagaruma wadda ake zama don hutawa ko don gudanar da cinikayya a ƙarƙashin ta. Daga nan ne fa aka samo sunan 'Rimin Gado' wajen nuni da bishiyar Rimin da ya girma a ƙarƙashin ko a kusa da gado. 

  Sannu a hankali wannan wuri ya haɓaka ainun tare da zamowa dandalin yada zangon fatake masu son shiga kano waɗanda akasarin su suke tafiya a ƙafa, ko a jakuna da sauran ababen hawan lokacin daga birane irin Alƙalawa, Sokoto da sauran su.

  TURBAR KANO TA SASHEN RIMIN GADO

  Wannan turba ta soma ne daga ƙofar Kabuga wadda take a yammacin kano, ta keta ta shacin Janguza, ta wuce ta Yalwan Ɗan ziyal har zuwa wannan gari na Rimin Gado. Daga nan kuma sai ta cigaba da nausawa sashen yamma har ta keta Gwarzo zuwa wasu sassan ƙasar Katsina. Kuma kamar yadda tarihi ya nuna, ta wannan turbar ne aka rinƙa samun sadarwa a tsakanin biranin Kano da biranen da suka kafu a zamanin baya waɗanda a yanzu suke cikin jihar kanon kanta, da Katsona da Zamfara daa Sokoto da Kebbi har zuwa sassan ƙashen Mali da  Nijar. Kuma haƙiƙa, ba iya Rimin Gado ba, akwai garuruwa da dama da kafuwar su ya samu ne daga albarkar wannan turba.