BONONO
SADIQ TUKUR GWARZO
Kamal Iyantama ne ya ja hankali na a wani rubutunsa mai nuni da yadda wata Marubuciya ta halarci wani taro sanye da tufafi mai nuna tsiraicin jikinta.
Don haka sa'ar da na halarci taron Marubuta, tunda ina da wancan ilimin a ƙwaƙwalwata, na zuba ido naga wacce zata kwata irin wancan abin da ya faru. Kwatsam sai kuwa na hango ta.
Shahararriyar marubuciya ce fa, ina girmama ta, tana shiga sha'aninmu sosai. Tufafin da ta sa ƙasaitacce ne. Irin wanda ake cewa ɗan ubansu! Daga kallonsa na san mai tsada ne wanda sai hamshaƙan mata ke ɗaurawa.. aibunsa kaɗai shine rashin rufe tsiraici. Wannan ne yasa na tuno da wata shahararriyar Hikayar Amurka mai suna 'The Emperor has No Clothes'. Bari na sanar daku wannan hikaya a taƙaice.
Wani Sarki aka taɓa yi mai son ƙawa a ƙasar Turai. Sai rannan wani maɗinki yace masa zai ɗinka masa tufafin da babu tamkarsa da wani zare na musamman. Sarki ya ɗauki tarin dukiya ya bashi.
Tun Kafin Maɗinkin ya gama aiki har Sarki ya sa anyi shela cewa za a ɗinka masa tufafin da babu tamkarsa, don haka yana son jama'ar gari suzo kallo a ranar da zai sanya shi.
Da Maɗinki ya kawo tufafi, sai Sarki baiga komai ba. Maɗinki ya gamsar da Sarki cewa zaren da aka ɗinka kayan idanuwa basa iya ganinsa. Don haka akayi dabaru, aka sanyawa Sarki wannan tufafi. Sarki ya fito gaban jama'a yana ƙwambo a matsayin wanda ya sanya mafi ƙawan tufafi na zamani.
Ko da fitowar Sarki, sai jama'a duk suka razana, domin a zahirance Sarkin tsirara yake, to amma tun kafin fitowarsa an sanar dasu cewa zaren tufafin sarki ba kowanne ido ke iya kallo ba. Don haka ba tsiraicin suke kallo ba, tufafin suke kokarin ganowa.
A haka, sai wani yaro ya kasa dannewa, ya ɗaga murya yana mai cewa "The emperor has no clothes". Watau, Sarki fa a tsirara yake! Daga nan kuwa sai hankalin jama'a ya dawo jikinsu cewa wannan fa rainin hankali ne, Sarki tsirara yake babu komai a jikinsa! Daga nan mutane suka watse cikin takaici. Sarki kuwa yayi turus, kunya duk ta lulluɓe shi.. ƙarshen mulkinsa kenan!
A irin rayuwar da muke ciki fa kenan (Fake life), mun fi yin abu don burga da burge mutane sama da cimma buƙatu na zahiri. Abinda ke faruwa a zahirin rayuwa daban, abinda muke kallo daban, sannan abinda muke muradi ma daban.. Wohoho!
Don haka, manufar tufafi ga ɗan adam shine rufe tsiraici.
Ko nawa ka kashe wajen siyen tufa, matsawar bata rufe tsiraici ba to anyi abinda ake kira BONONO.
Yin Bononon tsiraici kuwa, yana jan hankalin shaiɗanu ga mata, sannan ga uwa uba tsinuwar mala'iku.
Fatana, Allah ya sa ƴanuwana mata su faɗaka!