Wednesday, 11 December 2019

TARIHIN GARIN WUDIL

TARIHIN GARIN WUDIL

Sadiq Tukur Gwarzo
Garin Wudil na ɗaya daga manyan garuruwa a jihar kano kuma gari ne mai ɗauke da tarihi, don haka muka ga dacewar taskance kaɗan daga ɗumbin tarihin wannan gari.
  Ance wani maharbi ne ya sari garin, shikuwa daga Katsina ya taso. Tana iya yiwuwa Muhammadu sunansa, ko kuma Daudu, amma dai an tabbatar shine na farko da yazo ya zauna a wannan wuri inda garin wudil yake a halin yanzu.
   Ko da yake, da fari ance acan tsallaken ruwa ya soma zama, amma sai yayi tunanin yin amfani da ruwa wajen kare kansa da garin da zai kafa daga mahara kasancewar wancan lokaci ana cike da yake-yake da kamen bayi, don haka ya tsallaka ruwa sannan ya kafa Bukkar sa yana mai cigaba da sana'ar sa ta farauta a dajin dake kewayen kogin wudil.
  Sannu a hankali mutane matafiya masu zuwa neman ruwa suka rinka sauka a kusa dashi. Tun wasu na sauka su ɗanyi kwanaki sannan su tashi izuwa inda suka dosa, har kuma aka samu waɗanda suka mayar da wajen kachokan wajen zama tamkar shi. Akan haka akace gungun wasu fulan Joɓawa suka riski wannan maharbin tare da zama kusa dashi. Daga baya kuma sai shugabancin garin ma ya koma hannun su.
Sunan wudil ya samo asali ne daga wata Aljanna da aka tabbatar tana zaune a gidanta dake cikin tsakiyar wannan ruwa na Wudil. Ana kiranta da suna 'Uwar Wudil'.
Babu tabbacin lokacin da aljannar ta soma zama acikin ruwan, amma dai an tabbatar da cewa har yanzu tana nan tare da ahalinta.
  Ance ita fara ce doguwa mai siffar balarabiya, gashinta har gadon baya yake, kuma bata cutar da mutane, domin abaya takan shiga cikin garin Wudil ta yadda har mutane kanci karo da ita ba tare da ta razanar dasu ba. Ansha kuma ganinta a sauran garuruwa dake jikin wannan kogi na wudil.
Aljannar Wudil tana da tsohuwar alaka da mutanen garin wudil. Domin an samu cewar tana taimakon garin wajen samun kariya daga dukkan sharri tare kuma da yin galaba a yakunan da duk garin zai tunkara. Ance abaya, manyan gari na zuwa bakin kogi su yanka shanu, raguna ko tumaki sannan su sanar mata da abinda ya tasowa garin misalin yaƙi sannan sai azo a tafi. Ita kuma aikinta ne tayi duk mai yiwuwa wajen ganin buƙata ta biya.
  Wannan abu yana daga abinda Mallam Bakatsine ya ƙyamata tare da riƙa a matsayin hujjar yin jihadi a  zamanin Shehu Usman Danfodio. Don haka ance da lokacin hijira yayi, sai mabiya Shehu Usmanu dake kano suka tafi wani waje da ake kira Kwazazzabon Ƴarkwando, amma shi Mallam Bakatsine sai ya fita kano ta gabas yaje garinsu Utai ya ɗauki iyalinsa sannan ya ƙarasa garin wudil, inda ya yada zango a wani wuri da ake kira Nagge, anan ya tara runduna tare da zuwa buga yaƙi da garin Gaya inda ya ƙwace iko dashi.
 Duk da kasancewar a lokacin Garin Wudil zagaye yake da ganuwa da kuma ɗumbin jarumai, kuma karkashi Sarkin Kano Alwali amma babu labari mai nuna cewa sarakunan wudil sun yaƙi Mallam Bakatsine, ance hakan baya rasa nasaba da kasancewar a zamanin Fulani ke mulkin garin kuma suna da alaƙa dashi, don haka suka mara masa baya har ya cimma burinsa.
  Ana kiran sarautar wudil da suna Ɗan Daudu, kuma garin yana can gabas da garin kano da misalin tazarar mil talatin. 

Wednesday, 9 October 2019

TARIHIN TSOHON BIRNIN HAUSAWA; KAFIN DABGA

TARIHIN TSOHON BIRNIN HAUSAWA; KAFIN DABGA

SADIQ TUKUR GWARZO, GGA

  Daga cikin tsoffin biranen da Maguzawa suka kafa waɗanda kuma suka shahara a ƙasar Kano tun kafin zuwan jihadin Fulani akwai wannan tsohon garin mai suna 'Kafin Dabga'.
   Wani mashahurin mayaƙi bamaguje mai Suna 'Dabga' ne ya sari garin, shine kuma yayi masa kafi gagarumi domin kuɓuta daga dukkan harin mayaƙan wancan zamani, don haka ake kiran garin da suna Kafin Dabga.
   Garin ya haɓaka, ya shahara, kuma ya samu ɗaukaka. A baya ance zagaye yake da ganuwa, wadda aka yiwa ƙofofi guda huɗu. A kowacce kofa mace da namiji ne suka tsaya aka yaɓe su da ransu saboda surkulle, sannan da wata ƙaya sarƙaƙiya ake rufe kofar shiga birnin ba da ƙofa ba. Don hakangarin ya kasanxe mai tsananin uytsaro.
Idan yaƙi yazo, daka ake sanyawa ayi da dare, sai mayaƙa su shirya da hanzari. Masu kwari da baka su hau saman ganuwa, masu masu da takubba su shige surƙuƙi suna sauraron ko-ta-kwana.
Daga cikin sarakunan da ake iya tuna sunayen su a wannan gari, ance sunan Sarkin Kafin Dabga na farko Dugaji, Bamaguje ne, yayi wannan sarauta kimanin shekaru 400 da suka gabata, ko da yake tsufan kukokin garin da marinar garin na iya kaiwa sama da waɗannan shekarun. Amma dai kwatancin shekarun da ake tsammanin an soma sarauta a garin kenan.
Bayan mutuwar sa sai shi Dabga yayi mulki, wanda asali ance ya zamo tamkar uba ne mai ɗora wanda yake so shugabanci a garin.
 Daga shi sai Also, sannan sai Abdullahi ya fara mulki a zamanin da Fulani suka karɓe sarauta.
Akwai manyan gidajen da har yanzu ake ambata a garin, waɗanda sukayi gadon shugabancin garin, da kuma jarumta tun kafin jihadin fulani, misalin su shine; Gidan Nazundumi, Gidan Dankali, Gidan Butsatsa, da Gidan Gigo.
KUKAR ƳAR FULANI
Akwai wata kuka mai tarihi a wannan gari mai suna kukar ƴarfulani. Ita ƴar fulanin aljanna ce wadda ake da yaƙinin akan wannan kuka gidan ta yake.
Ance a zamanin baya, tana taimakon garin lokacin da yaƙi ya taso, ko kuma wani mugun abu ya nufo garin, inda take sanya sarƙa ta kanan-naɗe mahara.
Ance kuma a zamanin mulkin sarki Abdullahi na garin, yana sanyawa a kai mata ƙwaryar nono da farin goro duk ranar juma'a, ita kuma takan yin shewa da godiya yadda duk wanda ke garin sai ya ji.
TARWATSEWAR KAFIN DABGA
Kafin garin kafin Dabga ya samu raguwar mazauna, ya kasance shahararre mai cike da mutane wanda ya kasance daga gari-gari akan zo masa don yin fatauci.
Sannan garin yayi yaƙe-yaƙe da biranen dake kusanci da ma na nesa misalin Gammo da Ƙiru, har ma ana cewa ba a taɓa cin garin da yaƙi ba.
Sai dai wata annoba da ta faɗawa garin ce tayi sanadiyyar ɗaiɗaicewar sa.
Ance wata baƙar aljana ce ta rinƙa halaka mutane.
Idan dare yayi sai tayi shewa, tace 'Kun Taru?', to fa duk wanda yayi ko da gyaran murya a wannan daren ba zai wayi gari ba. Daga nan aka sanyawa annobar suna 'Kun-Taru'.
Don haka aka rinƙa wayar gari da gawarwakin mutane burjik waɗanda ta halaka, hakan yasa mutanen garin da dama suka ƙaurace masa.
A yanzu dai, garin Kafin Dabga yana nan ƙarƙashin garin Karaye, a jihar kano.

Monday, 12 August 2019

TARIHIN NUFE: KAFUWAR ƘASAR NUFE Kashi na huɗu

TARIHIN NUFE: KAFUWAR ƘASAR NUFE
Kashi na huɗu
SADIQ TUKUR GWARZO
    Marubuci Buhari Daure ya ruwaito a littafinsa 'Tarihi da Al'adun Mutanen Najeriya' cewa kafuwar ƙasar Nufe ya wanzu a wajajen ƙarni na goma sha shidda ne. Inda yace asalin Nufe dana Igala ɗaya ne, sai wani ɗan sarkin masarautar Idah mai suna Tsoede yayi gudun hijira tare da kafa masarautar Nupe wadda ta haɗe ƙauyukan Beni, Bidda, Benu, Debo, Tafiya, Doka, Gaba, Dibo da Kupa.
Amma binciken Dr. Sidi Tiwugu Shehi ya kawo ra'ayoyin masana da yawa  saɓani da wannan.
Daga ciki akwai masu cewa asalin Nufawa zuriyar wani balarabe ne mai suna Uqba bn Nafiu wanda ya baro ƙasar su ta larabci tare da zama a ƙasar Nupe.
Wasu kuma suka ce Nufawa sun fito ne daga wani Mafarauci balaraben Misira mai suna Abdulaziz wanda ya gudo daga ƙasar sa ya sauka a Doko Dazi cikin ƙasar Nufe dashi da ahalinsa. Daga nan aka sanya musu suna 'Nefiu' da yaren ƙabilar Beni daya tarar, wanda ke nufin 'wanda ya gudo daga wani wuri' .
Sannu a hankali sai sunan ya sauya zuwa Nufe ko Nupe.
Wasu kuma sunce Asalin Nufawa daga ƙasashen Katsina, Kano da wasu makusanta suke. Har ma Clapperton yace sunan Sarkin su Tsoede, kuma sun zo ƙasar Nupe ne daga wani birni da ake kira Attah Gara.
   Shikuwa Ndagi Abdullahi ya tafi akan cewa Nufawa suna kakannin Hausawa, Yarabawa da Inyamirai. Inda yace zuriyar Nufawan ce ta fantsama tare da samar da waɗannan yaruka (ko ace ƙabilu)
Amma dai masani S.F Nadel ya raba Nufawa gida huɗu daga abinda ya kawo a littafinsa mai suna 'Social Symbiosis and Tribal Organisation'. Ga rukunan kamar haka:-
Rukuni na ɗaya sune Ndachezhi, watau Mafarauta kuma asalin mazauna ƙasar Nupe waɗanda akace suna zazzaune a ƙauyuka sama da shekaru dubu da suka gabata.
Rukuni na biyu sune Esozhi, suma asalin Nufawa ne waɗanda suka jima a ƙasar Nufe har ma suka  kafa birnin Kutigi.
Rukuni na uku sune Benu, waɗanda suka yo hijira daga ƙasar Bornu. Su kuwa da yawansu malaman addinin Islama ne da masu fatauci, daga baya ne suka samu ikon wasu yankunan Kutigi.
Sai Rukuni na huɗu waɗanda ake kira Konu, waɗanda asalinsu bayi ne da aka kamo wurin yaƙi daga ƙasashen Yarabawa, daga baya aka ƴantar dasu tare da basu mazaunai a ƙasar Nupe.
Sannan binciken masana kimiyya da aka gudanar a yankunan Jebba, Giragu, Tada, Oyo-ile, Esie-oba da wasun su ya nuna cewar ƙasar Nupe tana ɗauke da mutane tun sama da shekaru 3000 zuwa dubu 10,000 kafin haihuwar Annabi Isah A.S.
Wannan yasa ake hasashen cewar asalin ƙabilun da suka rayu a wannan yanki wanda ya mamaye yankin Abuja da wasu yankunan tsakiyar Nigeria, sune suka haifar da ƙabilun Yarabawa, Inyamirai, Nupawa, Igala, Idoma, Ebira da Gbayi.

Saturday, 13 July 2019

TARIHIN HAUSANDA HAUSAWA: MAHANGA TA 7

TARIHIN HAUSA DA HAUSAWA: MAHANGA TA 7
Sadiq Tukur Gwarzo

Littafin 'Hausawa da Maƙwabtan su' wanda turawan mulkin mallaka da haɗin guiwar wasu hausawa suka samar mai ƙunshe da tarin zantuka  game da tarihin Hausawa da maƙwabtan su ya danganta asalin Hausawa ga Borno.
   Aka ce Sarkin Borno na da wani bawa mai suna Bawo, babu wanda ya san asalin sa, ko dangin sa. Amma abinda aka sani shine Sarkin Borno ya jiɓanta shi a kan biranen Hausa guda bakwai da ake kira Hausa bakwai yana mai riƙe dasu yana tattara haraji tare da kula da lamurorin su, har ya haifi ƴaƴa bakwai.
   A zamanin da ya ga alamun mutuwa sai ya sarautar da waɗannan garuruwa ga ƴaƴayen nasa. Kowannen su ya bashi birni guda.
  Har aka ce wanda ya sa a Daura ba namiji bane, mace ce mai suna Daura. Saboda haka ake ambaton garin da sunanta.
   Haka kuwa itace babba a cikin ƴaƴansa, itace ƴaruwar sarkin katsina da sarkin Kano da sarkin Gobir, domin dukkan su uwarsu ɗaya.
   Kuma sarkin Burmi da Sarkin Zazzau uwarsu ɗaya. Sarkin Rano kuwa shi kaɗai ne wurin uwarsa.
Saboda haka sai ya zamana ƴaƴayen sun cigaba da bayar da harajin ƙasashen su zuwa Daura, daga nan kuma ana aikawa Borno zuwa ga Sarkin ta.
Sarkin Gobir Bawa kaɗai ne ya ƙi bada harajin nan, sai kuwa yaƙoƙi suka rinƙa aukuwa tsakanin garuruwan da Borno, daga bisani ya ƴamtar da ƙasashen Hausa daga Borno.
Wannan abu tabbatacce ne a cikin labarun da aka faɗe su, haƙiƙa asalin su ƴaƴa ne, su ne ragowar Kibɗawa. Su kuma Kibɗawa sune jama'ar Fir'auna da suka tafo daga Misira suka cika garuruwan Ahira har suka tafi Gobir suka fitad da waɗanda suke cikinta, sune waɗanda suka mallake ta daga ƴaƴan Bawo suka karɓe sarauta daga hannun mutanen wajen. Suka rinƙa yin aiki daga abinda suka iske ƴaƴan Bawo suna yi, suna masu biyan haraji har zuwa lokacin da Bawo ya hana biya.

Monday, 10 June 2019

MAHANGA TA 8: HAUSA DAGA YANKIN ASIA

MAHANGA TA 8: HAUSA DAGA YANKIN ASIA
SADIQ TUKUR GWARZO

Wannan mahanga ta kalli kachokan ɗin harshen Hausa ne wanda Hausawa ke amfani dashi tare da yanke hukuncin cewa asalin Hausawa daga yankin Asia suke.
  Harshen Hausa dai ɗaya ne daga rukunin harsuna kimanin 250 masu suna 'Afro-Asiatic languages',  (Semito-Hamitic), waɗanda aka fi samu  a Arewaci da yammacin Afirka, Kasashen Larabawa da wasu tsibirai na yankunan Yammacin Asia.
  Asalin wannan suna dai na 'AFRO-ASIA' wanda ya haɗa kalmomin Africa da Asia watau ya fito ne daga wani   Ba Amurke masanin Harsuna  mai sunaJoseph H. Greenberg.
  Sannam dashi da wasu Masanan  sun yi hasashen cewa dukkan waɗannan harsuna kimanin 250 sun fito ne daga wani harshe guda ɗaya wanda akayi hasashen ya wanzu a duniya kimanin shekaru 15,000 kafin haihuwar Annabi Isah A.S.
  Ance mutanen yankin Urheimat da suke zaune a Asia tun a wancan taohon zamami ne suke amfami da harshen, kafin daga bisani wasu dalilai suka rinka sanya mutanen yin hijira gami da bazama cikin duniya, ta yadda har bayan shekaru kimanin dubu 17 harsuna 250 sun fita daga jikin yaren nasu.
Masana sun yi hasashen cakuɗuwar ƙabilu da harasa a kusan ɗaukacin yankunan duniya, don haka aka tsammaci wasu daga waɗancan zuriya ne suka keto bahar Maliya zuwa yankin Afirka da zama tare da barbazuwa a tsawon lokaci, inda zuwa yau harshen ya rarrabu zuwa gidaje 5.
 1. Egyptian ( Yankin Tekun Nilu)
2. Amazigh (Berber; Arewacin Africa da Tsakiyar Sahara)
3. Chadic (Tsakiyar Africa, da yankin Tafkin Chadi. Harshen Hausa na ciki).
4. Cushitic (Yankin da ake kira Horn of Africa), da
5. Omotic (Kudu maso yammacin kasar Ethiopia).
  Daga abubuwan da masana suka kalla wajen danganta waɗannan harsuna da juna akwai yanayin fatar masu amfani da harsunan, da kuma falsafar harasan kansu, ko ace wasu jigogi dake tattare da harussan baki ɗaya.
   Misali, harshen Hausa daya fito daga gidan Chadic, an kalli abubuwa da dama kamar kalmar 'Mashi', da yadda jam'in ta ke komawa zuwa  'Masu' wajen sauyawar 'h' da 'i' zuwa 's' da 'u'. Haka kuma an kalli yadda a harshen ake amfani da kalmar 'ka' wajen danganta mallakin Namiji da kuma kalmar 'Ki' wajen danganta mallakin mace, abinda kusan yazo ɗaya a dukkan rukunin harussa aka sanya su a gida ɗaya.
  A karshe, mahangar tana nuni da cewa Asalin masu harshen Hausa mutane ne jikokin wasu ƙabilu da suka rayu a yankin Asia dubunnan shekaru da suka gabata.
Farfesa Ibrahim Malumfashi, da Marubuci Ado Ahmad gidan Dabino MON na daga marubutan da suka yi rubutu akan mahangar.

Sunday, 26 May 2019

TARIHIN FULANI A WATA MAHANGAR

TARIHIN FULANI

SADIQ TUKUR GWARZO

  ASALIN KALMAR FULANI


Mal Ahmad Usman Bello, shugaban kungiyar Fulani ta kasa mai suna FULDAN, bafullatani ne Batoranke, kuma masani akan tarihin jinsin sa, a wata zantawa da mu kayi dashi ya faɗa mana wasu ƙarin mahangai game da tarihin Fulani.
   Da fari dai, masanin ya faɗa cewar tabbataccen tarihi shine wanda yazo a Alkur'ani da Hadisai, amma duk wani abu wanda ba shiba kan iya zamowa gurɓatacce, don haka bai ɗoru akan cewa wajibin duk abinda ya faɗa shine na gaskiya ba.
   A cewar sa asalin sunan Fulani shine Tuta (Futa Toro), kuma suna cikin tsoffin kabilun duniya ne. Shi sunan Futa din sun samo shine daga kakansu/uban su da ake kira Futa, kuma shi jika ne ga Annabi Nuhu. Ta wajensa aka samar da Samudawa da Adawa, don haka faɗin Ta Ala a Alkurani (IRAMA ZA TUL IMAAD) da kabilar su yake, domin an samu cewa an taɓa kiran su da suna Iramawa.
  Daga bisanin saboda yawaitar su ga yake-yake, sai aka rinka kiransu da suna Fatah, ma'ana Jarumai. Sannu a hankali kuma aka koma ambaton su da suna Futa.
Yanayin zaman su a wurare kuwa shine silar sauyawar sunayen su, ta yadda ake kiran wasu Futa Toro, ma'ana Futawa mazaunan Toro, da Futa Masina, Futa Jallo, Futa Falgo da sauran su
   A cewar masanin, shi wannan sunan na FULANI, ya samo asali ne a yammacin afirka, sanda suka haɗu da kabilar MANDINKA wajen zama, waɗanda suma kusan fulani ne a halaye da ɗabiu.
Mallam Ahmad ya tafi akan cewa Fulani kabilar farko ce da suka soma zaman Afirka, kuma sune suka zo da addini yammacin Afirka, amma fa addinin Yahudanci. Shikuwa kowa ya sani addini ne na jinsi, ba na kowa da kowa ba.
Don haka idan fulanin sun tara ƴaƴan su, su kan sanar musu da cewa 'Ana Hulɓe (Fulɓe) Allah'. Ma'ana mu masu tsoron Allah ne, kada kuyi abinda Mandinkawa abokan zaman mu suke aikatawa. Daga nan sai mandinkawa masu zuwa ganin su suka rinka kiransu da suna Fulah, kafin daga bisani sunan ya rinka sauyawa zuwa Fullata, da Fulɓe.
ASALIN BAFILLATANI
  MAHANGA TA ƊAYA
Mallam Ahmad ya sanar mana da cewa Bafillatani ya samu ne daga jikin Annabi Nuhu A S.
 Asalin zuriyar sa kuma a yankin Ɗurun Sinin take da zama. Anan ne har Annabi Musa A.S ya riske su a zamanin sa lokacin da aka saukar masa da Attaurah. A lokacin suna masu bautar shanu, don haka sai ya kira iya kabilar sa Bani Israila zuwa bautar Allah makaɗaici.
Shiyasa sai Bani Isra'ila suka yi kwaɗayin a sanya musu abin bauta kamar yadda futawa suke yi, har kuma Musa Samiri ya shagaltar dasu tare da sanya musu ɗan mariki a matsayin abin bautar Annabi Musa A .S.
 Sai daga baya Annabin Allah Musa ya gane lamarin, sannan ya kira shugaban su mai suna Tori ya karbi addini, shine har akayi bikin karɓar sa ranar asabar a jikin dutsen Ɗuri Sina. Fulani na kiran bikin 'Larki'. Har kuma sukan ce "RaduTori Sinin", watau ga Inda Tori ya musulunta wajen nuni da Ɗuri Sinin.
A wannan zamanin, sai kabilar Futah ta kasu. Wasu suka karbi addinin Annabi Musa bisa biyayya da shugaban su Tori, wasu kuma suka bijere, inda sukayi Hijira zuwa Afirka ta Kudu, daga jikin su kabilun Chusi da ake kira Totsi yanzu suka fita, da sauran kabilun da suka mamaye yankunan.
ASALIN BAFILLATANI: MAHANGA TA BIYU
  Akace asalin Fulani tare da Yahudawa suke da zama. Don haka kusancin su ke sanyawa ake kiransu da sunan Yahudawa. Kuma su mayaƙa ne mara sa tsoro waɗanda basa rabo da makami, sannan suna matukar ɗaukaka ranar asabar sama da sauran ranaku saboda tarayyar su da yahudawa. Sannu a hankali suka famtsama yankin Afirka ta Yamma.
ASALIN FULANI: MAHANGA TA UKU
Wannan mahangar kuma ta nuna cewa Fulani tsatso ne daga zuriyar Annabi Ayyuba A.S..
Akace a lokacin da ya zama dattijo yana wa'azi a gefen tekun Indiya, sai aka bashi wata mace aure wadda bata son sa. Don hakan idan dare yayi sai ta guje masa zuwa bayan ɗaki, acan kuma sai sheɗan ya rinka zuwar mata yana tarawa da ita. A haka har ta samu rabon yaro namiji wanda baya magana da kowa.
Akayi magana akan yadda ta samu wannan yaro dube da rashin tarayyar ta da maigidanta, amma Annabi Nuhu yace a kyale ta a matsayin matar sa, daga bisani hakan ya cigaba da faruwa har ta sake haifar yarinya mace.
 Don haka waɗannan mace da namijin da suka girma sune suka fara amfani da yaren su sabo na Fulatanci.
  MAHANGA TA 4
A kwai kuma mahanga ta huduhar ila yau daga Mallam Ahmad Usman mai cewa asalin Fulani Rumawa ne. Kabilun Rum (Romans) ne makiyaya da suke zaune a karkara. Lokacin basasar Rum bayan kisan Julius Caesar sai ya zamana babu tsaro a kasar ta Rum. A dalilin haka da yawansu su ka rika kwararowa cikin Africa don kubutar da dukiyoyinsu. Cudanyarsu da wasu kabilun Africa ne ya samar da yaren fulatanci. Lokacin wannan kaura tare suka shigo Africa da mazauna yankin Sisley makiyaya. Wadannan kabilun mazauna Sisley su Fulani ke Kira Sissilɓo wato mutanen Sisley, da Hausa muna kiransu sulluɓawa. Har a yau dinnan da yawa daga cikin sulluɓawa ba sa amsa sunan Fulani.

Saturday, 25 May 2019

MAHANGAR MU AKAN TALAUCI DA MATSALAR TATTALIN ARZIKI

MAHANGAR MU AKAN TALAUCI DA MATSALAR TATTALIN ARZIKI A NIGERIA.
(Gaskiya ɗaci gareta)

24-janairu-2016

    Tare da SADIQ TUKUR GWARZO

Assalamu alaikum
    Duba da matsanancin halin da talakawan ƙasa ke ciki, gami da tsare-tsare wadanda hukumomi ke dauka don saisaita lamurori a ƙasar nan, ya sanya mu yin duba gami da yin wannan rubutu.

   DALILAN DA KE SANYA TALAKA CIGABA DA ZAMOWA CIKIN TALAUCI, ATTAJIRI KUMA YA CIGABA DA ZAMOWA CIKIN ARZIKI
   A shekarar 2007, wani hasashe da ofishin mai kula da hada-hadar  kudi na al'ummar ƙasar Amurka (Congressional Budget office) yayi, ya nuna cewar duk wasu tsare-tsare da gwamnatoci ke aiwatar wa ga 'yan ƙasa, attajirai kurum yafi amfana, domin kuwa talakawa na ƙara cigaba da zamowar su cikin talauci ne.
   Ga kadan daga abinda bincikensu ya nuna;
TALAKAWA: A tsawon shekaru talatin, samun kudin su ya haɓaka ne da kaso goma sha takwas kacal. (Ma'ana talakan da yake samun dalar Amurka ɗaya a tsawon wancan lokaci, har yanzu baya samun dala biyu)
MATSAKAITA: A tsawon shekaru talatin, samun kudin matsakaitan mutane ya ƙaru ne da kashi 40 kacal.
ATTAJIRAI: A tsawon shekaru talatin, samun kudin attajirai ya haɓaka ninkin-ba-ninkin da kashi 275. ( wannan labari yana da matuƙar kyau idan aka haɗa shi da yanayin da talakawan nigeria suke daga shekaru talatin zuwa yau)
   Haka kuma a shekarar 2010-zuwa-2011, lokacin da tattalin arzikin Amurka ya fadi warwas, hasashe ya nuna cewa rashin aikin yi da talauci sun ƙaru sosai, har ma akace Amurkawa miliyan arba'in da shidda, wadanda a baya suke da rufin asiri ne (matsakaitan mutane) suka fada sahun talakawa. Hakan ne ya nuna cewa a duk Amurkawa guda shidda, biyar talakawa ne, ɗaya ne attajiri. Mutanen da a baya suke daukar dawainiyar wasu, ya zama sun koma ta kansu sukeyi. Wannan kuma sai ya haifar da ƙaruwar munanan laifuka gami da rashin kwanciyar hankali a ƙasar ta Amurka. 
   Har ila yau, a wani bincike da masana siyasar duniya suka gabatar, sun lura da cewa manyan shugabannin duniya masu farin jinin mabiya, suna haduwa da baƙin jini, ko dusashewar farin jini yayin da suka hau karagar mulki, saboda yadda suke gaza aiwatar da ainihin muradun da mabiyan nasu suka zabe su akai. 
Misali; Franklin Delano Roosevelt da Adolf Hitler, dukkansu shugabanni ne da tarihi ba zai mance farin jinin su a wurin mabiyan su ba, har ma sun hau karagar mulki cikin soyayyar al'umma madaukakiya, amma kuma sun bar mulki cikin baƙin jinin jama'a.
   Amurkawa sun zaɓi Franklin Roosevelt ne a lokacin da suke mawuyacin talauci, tsammanin su da zarar ya hau mulki zaiyi ƙoƙarin magance wannan matsala, amma sai akayi rashin sa'a, jim kaɗan da hawan sa mulki sai ya tunkari yaƙi tare da ƙara tsunduma Amurka cikin Ƙangin karyewar tattalin arziki. 
Haka ma Adolf Hitler, jamusawa sun lamunce masa ya hau kan mulki cikin gagarumar soyayya saboda suna tsammanin shine kadai ɗan kishin ƴasa, wanda zai iya warkar da annobar talauci da ta biyo bayan yaƙin duniya na ɗaya da Jamus ta gwabza, amma da hawan sa karagar mulki sai ya ƙara cusa ƙasar Jamus a cikin yaƙin da yafi na baya tsamari.
 Makamancin haka ne ya auku ga shugaba obama, wanda ya hau mulki cikin farin jini sosai a karo na farko, amma a karo na biyu ya gamu da raguwar masoya, domin ya gaza warkar da ƙishirwar mabiyansa (daga baya ma sai gashi jamiyyar sa ta faɗi warwas a mulki).
   Wadannan duk abubuwa ne da zasu haska mana abinda zai iya faruwa a ƙasar mu Nigeria dai-dai da abinda yake faruwa ayau. Tunda dai munji Imam ibn khaldun na cewa "abinda ya faru a jiya, shine ke bada labarin abinda ke faruwa ayau. Abinda ke faruwa a yau kuwa, shine ke haska abinda zai auku a gobe".
   A ƙasar nan, muna iya cewa mutane biyu ne attajirai. Ɗaya sunan sa Dan siyasa, dayan kuwa Dan kasuwa ake yi masa laƙabi. Kusan dukkan su, suna amfanuwa ne da gwamnati, suna kuma taka doron bayan talaka ne don samun arziƙi. Dan siyasa, sai jama'ar talakawa sun zabe shi zaici mulki sannan ya samu zarafin juya lalitar al'umma, haka ɗan kasuwa wanda  yake samun arziki ta hanyar sayarwa da al'umma hajojinsa.
   Maganar gaskiya itace, dukkan wani tsare-tsare da gwamnati ke ɗauka domin sauƙaƙawa talakawa sau tari, wadancan mutanen biyu take taimakawa. Sauran talakawa kuma take ƙara ƙuntatawa.  Yawansu kuwa dai-dai yake da biyu bisa goma, ma'ana ayanzu, muna iya cewa acikin mutanen Najeriya goma, mutane takwas talakawa ne masu neman na abinci, mutum biyu ne attajirai. Ita kuwa gwamnati, wasu mutane da ake kira 'Bureaucrats' ne ke tafiyar da ita.. mutane ne 'yan jari hujja wadanda basu san zafin talauci ba, idan za'a siyar da shinkafa buhu daya akan naira dubu dari, litar man fetur akan naira dubu, ba zasu damu ba.
   Ku duba ma'anar kalmar 'Pain' a dikshinari, talaka shi kaɗai yasan zafin talauci, tunda a cikin sa yake. Talakan nan kuma ya zaɓi wannan gwamnati ne don ta yi masa maganin matsalar tsaro da talauci da suka addabeshi. Kamar misalin mutum ne yana tsananin jin ƙishirwa, sai ya aiki wani ya kawo masa ruwa, idan ɗan aiken yayi jinkiri, dole wannan mutumi ya ƙara tura wani dan aiken domin samun biyan buƙatar sa. Don haka matsawar wannan gwamnati zata yi nuƙusani wajen sassauta tsadar rayuwa, ko warware matsalolin tsaro, dole ne farin jinin shugabanta ya ragu kamar yadda abin ya faru a Amurka da Jamus.     
   Masana ilimin tsimi da tanaji, sunyi mana bayanin yadda abubuwa ke yin tsada ko arha, ga abinda suke cewa "idan kayayyaki suka yawaita a kasuwa, dole farashin su ya karye. Idan kuwa sukayi ƙaranci, dole darajar su ta hau". Don haka, idan har dagaske gwamnati tayi shirin sauƙaɗawa talakawa, muna iya cewa bata kyauta ba yadda ta samar da ƙarancin kayan abinci a ƙasar nan (gwamnati ta hana shigowa dasu) domin ba tayi wani tanaji na azo a gani ba. Ya kamata ta fara baiwa 'yan ƙasa taki da iri na nomanta, sannan ta baiwa 'yan kasuwa damar kafa kamfanoni, in yaso idan aka yi noma sai tace ta hana shigowa da hatsi yadda tilas ayi amfani da kayan gida, amma wallahi abinda tayi a yanzu ya sanya al'umma cikin tsanani, kuma hakan kuskure ne.
   Batu na gaskiya, tilas ne mu fadawa shugaban mu kuma masoyin mu gaskiya. Idan har ya samu matsala a mulkinsa, dukkan mu ne muka samu matsala. 
Abinda zai yi maganin karyewar tattalin arzikin ƙasa shine gwamnati ta bada agajinta wajen ganin an bude ƙananun masana'antu, ta sauƙaƙa haraji, sannan tayi tanajin duk abinda take tunanin ana buƙatar sa a cikin gida, daga bisani sai a tilastawa 'yan ƙasa dogaro da wadannan masana'antun. Wannan ne kurum zai habaka dogaro da kai, gami da samar da dumbin ayyukan yi a ƙasa. 
 Idan da zamu bibiyi tarihin ƙasahen china, Indiya da Iran, da mun tabbatar da wadannan abubuwa. Amma a yanzu, tsarin da gwamnati ta dauka na nuna cewar talauci zai cigaba da wanzuwa a ƙasar nan har nan da shekaru biyu da rabi, babbar matsalar shine, dole ne rashin zaman lafiya ya ƙaru a ƙasar saboda talaucin da yawa-yawan 'yan ƙasa ke fama dashi, sai dai idan gwamnatin zata ƙaro makamai ne yadda zata rinƙa kashe 'yan ƙasarta da kanta. 
   Shi fa mulki dan Hikima ne, shi yasa Hausawa ke cewa idan aka ciza, sai a hura. Idan bala'I yayi bala'I, sai ka ga talaka ya dai na tsoron mutuwa, daga nan sai ya fara fito-na-fito da gwamnati. Wannan ne yasa Marigayi Umar 'Yar aduwa yaci nasarar mulkinsa (Allah yajiƘansa) domin yayi hikimar sulhu da 'yan tawayen Naija Delta wadanda talauci yasa basa tsoron mutuwa. Shi kuwa talakan ƙasar nan, ya kamata ya mayar da kai wajen neman ilimin neman  dukiya gami da sarrafa ta, ta yadda zai matsa daga halin da yake ciki zuwa na gaba, sannan kuma ya sani, duk abinda gwamnati za tayi, attajirai zata ƙarawa arziƙi. Kuma ba zata iya karya su ba. Idan aka cire tallafin mai, attajirai aka taimakawa domin zasu siyo a waje da sauƙi, suzo su siyar da tsada a gida. Haka kuma idan an hana shigowa da shinkafa, attajiran dai aka ƙara taimakawa, domin sune ke da kudin yin gagarumin noma, wasunsu kuwa tuni sunyi hasashen aukuwar hakan, kuma sunyi tanajin kayan abinci daro-daro, don haka a hankali zasu rinƙa fitowa dasu suna siyarwa al'umma da tsada.
   Madalla da  Abraham Lincoln (tsohon shugaban amurka) wanda yake cewa.        "You cannot strengthen the week by weakening the strong.
  You cannot help the wage earner by pulling down the wage payer"
  A ƙarshe, muna fatan Allah ya ganar da shugannin mu, Allah ya dora su bisa tafarki na gaskiya. Amin
  Dg Sadiq Tukur Gwarzo