MAHANGAR MU AKAN TALAUCI DA MATSALAR TATTALIN ARZIKI A NIGERIA.
(Gaskiya ɗaci gareta)
24-janairu-2016
Tare da SADIQ TUKUR GWARZO
Assalamu alaikum
Duba da matsanancin halin da talakawan ƙasa ke ciki, gami da tsare-tsare wadanda hukumomi ke dauka don saisaita lamurori a ƙasar nan, ya sanya mu yin duba gami da yin wannan rubutu.
DALILAN DA KE SANYA TALAKA CIGABA DA ZAMOWA CIKIN TALAUCI, ATTAJIRI KUMA YA CIGABA DA ZAMOWA CIKIN ARZIKI
A shekarar 2007, wani hasashe da ofishin mai kula da hada-hadar kudi na al'ummar ƙasar Amurka (Congressional Budget office) yayi, ya nuna cewar duk wasu tsare-tsare da gwamnatoci ke aiwatar wa ga 'yan ƙasa, attajirai kurum yafi amfana, domin kuwa talakawa na ƙara cigaba da zamowar su cikin talauci ne.
Ga kadan daga abinda bincikensu ya nuna;
TALAKAWA: A tsawon shekaru talatin, samun kudin su ya haɓaka ne da kaso goma sha takwas kacal. (Ma'ana talakan da yake samun dalar Amurka ɗaya a tsawon wancan lokaci, har yanzu baya samun dala biyu)
MATSAKAITA: A tsawon shekaru talatin, samun kudin matsakaitan mutane ya ƙaru ne da kashi 40 kacal.
ATTAJIRAI: A tsawon shekaru talatin, samun kudin attajirai ya haɓaka ninkin-ba-ninkin da kashi 275. ( wannan labari yana da matuƙar kyau idan aka haɗa shi da yanayin da talakawan nigeria suke daga shekaru talatin zuwa yau)
Haka kuma a shekarar 2010-zuwa-2011, lokacin da tattalin arzikin Amurka ya fadi warwas, hasashe ya nuna cewa rashin aikin yi da talauci sun ƙaru sosai, har ma akace Amurkawa miliyan arba'in da shidda, wadanda a baya suke da rufin asiri ne (matsakaitan mutane) suka fada sahun talakawa. Hakan ne ya nuna cewa a duk Amurkawa guda shidda, biyar talakawa ne, ɗaya ne attajiri. Mutanen da a baya suke daukar dawainiyar wasu, ya zama sun koma ta kansu sukeyi. Wannan kuma sai ya haifar da ƙaruwar munanan laifuka gami da rashin kwanciyar hankali a ƙasar ta Amurka.
Har ila yau, a wani bincike da masana siyasar duniya suka gabatar, sun lura da cewa manyan shugabannin duniya masu farin jinin mabiya, suna haduwa da baƙin jini, ko dusashewar farin jini yayin da suka hau karagar mulki, saboda yadda suke gaza aiwatar da ainihin muradun da mabiyan nasu suka zabe su akai.

Misali; Franklin Delano Roosevelt da Adolf Hitler, dukkansu shugabanni ne da tarihi ba zai mance farin jinin su a wurin mabiyan su ba, har ma sun hau karagar mulki cikin soyayyar al'umma madaukakiya, amma kuma sun bar mulki cikin baƙin jinin jama'a.
Amurkawa sun zaɓi Franklin Roosevelt ne a lokacin da suke mawuyacin talauci, tsammanin su da zarar ya hau mulki zaiyi ƙoƙarin magance wannan matsala, amma sai akayi rashin sa'a, jim kaɗan da hawan sa mulki sai ya tunkari yaƙi tare da ƙara tsunduma Amurka cikin Ƙangin karyewar tattalin arziki.

Haka ma Adolf Hitler, jamusawa sun lamunce masa ya hau kan mulki cikin gagarumar soyayya saboda suna tsammanin shine kadai ɗan kishin ƴasa, wanda zai iya warkar da annobar talauci da ta biyo bayan yaƙin duniya na ɗaya da Jamus ta gwabza, amma da hawan sa karagar mulki sai ya ƙara cusa ƙasar Jamus a cikin yaƙin da yafi na baya tsamari.
Makamancin haka ne ya auku ga shugaba obama, wanda ya hau mulki cikin farin jini sosai a karo na farko, amma a karo na biyu ya gamu da raguwar masoya, domin ya gaza warkar da ƙishirwar mabiyansa (daga baya ma sai gashi jamiyyar sa ta faɗi warwas a mulki).
Wadannan duk abubuwa ne da zasu haska mana abinda zai iya faruwa a ƙasar mu Nigeria dai-dai da abinda yake faruwa ayau. Tunda dai munji Imam ibn khaldun na cewa "abinda ya faru a jiya, shine ke bada labarin abinda ke faruwa ayau. Abinda ke faruwa a yau kuwa, shine ke haska abinda zai auku a gobe".
A ƙasar nan, muna iya cewa mutane biyu ne attajirai. Ɗaya sunan sa Dan siyasa, dayan kuwa Dan kasuwa ake yi masa laƙabi. Kusan dukkan su, suna amfanuwa ne da gwamnati, suna kuma taka doron bayan talaka ne don samun arziƙi. Dan siyasa, sai jama'ar talakawa sun zabe shi zaici mulki sannan ya samu zarafin juya lalitar al'umma, haka ɗan kasuwa wanda yake samun arziki ta hanyar sayarwa da al'umma hajojinsa.
Maganar gaskiya itace, dukkan wani tsare-tsare da gwamnati ke ɗauka domin sauƙaƙawa talakawa sau tari, wadancan mutanen biyu take taimakawa. Sauran talakawa kuma take ƙara ƙuntatawa. Yawansu kuwa dai-dai yake da biyu bisa goma, ma'ana ayanzu, muna iya cewa acikin mutanen Najeriya goma, mutane takwas talakawa ne masu neman na abinci, mutum biyu ne attajirai. Ita kuwa gwamnati, wasu mutane da ake kira 'Bureaucrats' ne ke tafiyar da ita.. mutane ne 'yan jari hujja wadanda basu san zafin talauci ba, idan za'a siyar da shinkafa buhu daya akan naira dubu dari, litar man fetur akan naira dubu, ba zasu damu ba.
Ku duba ma'anar kalmar 'Pain' a dikshinari, talaka shi kaɗai yasan zafin talauci, tunda a cikin sa yake. Talakan nan kuma ya zaɓi wannan gwamnati ne don ta yi masa maganin matsalar tsaro da talauci da suka addabeshi. Kamar misalin mutum ne yana tsananin jin ƙishirwa, sai ya aiki wani ya kawo masa ruwa, idan ɗan aiken yayi jinkiri, dole wannan mutumi ya ƙara tura wani dan aiken domin samun biyan buƙatar sa. Don haka matsawar wannan gwamnati zata yi nuƙusani wajen sassauta tsadar rayuwa, ko warware matsalolin tsaro, dole ne farin jinin shugabanta ya ragu kamar yadda abin ya faru a Amurka da Jamus.
Masana ilimin tsimi da tanaji, sunyi mana bayanin yadda abubuwa ke yin tsada ko arha, ga abinda suke cewa "idan kayayyaki suka yawaita a kasuwa, dole farashin su ya karye. Idan kuwa sukayi ƙaranci, dole darajar su ta hau". Don haka, idan har dagaske gwamnati tayi shirin sauƙaɗawa talakawa, muna iya cewa bata kyauta ba yadda ta samar da ƙarancin kayan abinci a ƙasar nan (gwamnati ta hana shigowa dasu) domin ba tayi wani tanaji na azo a gani ba. Ya kamata ta fara baiwa 'yan ƙasa taki da iri na nomanta, sannan ta baiwa 'yan kasuwa damar kafa kamfanoni, in yaso idan aka yi noma sai tace ta hana shigowa da hatsi yadda tilas ayi amfani da kayan gida, amma wallahi abinda tayi a yanzu ya sanya al'umma cikin tsanani, kuma hakan kuskure ne.
Batu na gaskiya, tilas ne mu fadawa shugaban mu kuma masoyin mu gaskiya. Idan har ya samu matsala a mulkinsa, dukkan mu ne muka samu matsala.
Abinda zai yi maganin karyewar tattalin arzikin ƙasa shine gwamnati ta bada agajinta wajen ganin an bude ƙananun masana'antu, ta sauƙaƙa haraji, sannan tayi tanajin duk abinda take tunanin ana buƙatar sa a cikin gida, daga bisani sai a tilastawa 'yan ƙasa dogaro da wadannan masana'antun. Wannan ne kurum zai habaka dogaro da kai, gami da samar da dumbin ayyukan yi a ƙasa.

Idan da zamu bibiyi tarihin ƙasahen china, Indiya da Iran, da mun tabbatar da wadannan abubuwa. Amma a yanzu, tsarin da gwamnati ta dauka na nuna cewar talauci zai cigaba da wanzuwa a ƙasar nan har nan da shekaru biyu da rabi, babbar matsalar shine, dole ne rashin zaman lafiya ya ƙaru a ƙasar saboda talaucin da yawa-yawan 'yan ƙasa ke fama dashi, sai dai idan gwamnatin zata ƙaro makamai ne yadda zata rinƙa kashe 'yan ƙasarta da kanta.
Shi fa mulki dan Hikima ne, shi yasa Hausawa ke cewa idan aka ciza, sai a hura. Idan bala'I yayi bala'I, sai ka ga talaka ya dai na tsoron mutuwa, daga nan sai ya fara fito-na-fito da gwamnati. Wannan ne yasa Marigayi Umar 'Yar aduwa yaci nasarar mulkinsa (Allah yajiƘansa) domin yayi hikimar sulhu da 'yan tawayen Naija Delta wadanda talauci yasa basa tsoron mutuwa. Shi kuwa talakan ƙasar nan, ya kamata ya mayar da kai wajen neman ilimin neman dukiya gami da sarrafa ta, ta yadda zai matsa daga halin da yake ciki zuwa na gaba, sannan kuma ya sani, duk abinda gwamnati za tayi, attajirai zata ƙarawa arziƙi. Kuma ba zata iya karya su ba. Idan aka cire tallafin mai, attajirai aka taimakawa domin zasu siyo a waje da sauƙi, suzo su siyar da tsada a gida. Haka kuma idan an hana shigowa da shinkafa, attajiran dai aka ƙara taimakawa, domin sune ke da kudin yin gagarumin noma, wasunsu kuwa tuni sunyi hasashen aukuwar hakan, kuma sunyi tanajin kayan abinci daro-daro, don haka a hankali zasu rinƙa fitowa dasu suna siyarwa al'umma da tsada.
Madalla da Abraham Lincoln (tsohon shugaban amurka) wanda yake cewa. "You cannot strengthen the week by weakening the strong.
You cannot help the wage earner by pulling down the wage payer"
A ƙarshe, muna fatan Allah ya ganar da shugannin mu, Allah ya dora su bisa tafarki na gaskiya. Amin
Dg Sadiq Tukur Gwarzo

No comments:
Post a Comment