MAZA GUMBAR DUTSE: AYYUKAN ASUSUN TALLAFIN MAN FETUR (PTF) NA GWAMNATIN JANAR SANI ABACHA, WANDA SHUGABA BUHARI YA JAGORANTA
Daga Sadiq Tukur Gwarzo
A watan Oktoba na shekarar 1994, marigayi Shugaba Sani Abacha dake mulkar Nigeria a lokacin, ya bayyana Karin kudin man fetur. Wannan abu ya tada kura a kasar nan, wanda yasa 'yan kasa suka rinka korafi suna masu nuna adawar su ga wannan Karin farashi.
Hakan tasa Shugaba Abacha yin dogon tunani da nazari akan lamarin. Na farko dai bai kara farashin man fetur ba sai bisa wasu muhimman dalilai, sannan kuma shi ba shugaba bane mai son uzzurawa al'ummar daya ke mulka, kamar yadda ake yawan jiyo shi yana cewa "an gina gwamnati ne don al'umma, ba don aci riba ba", don haka sai ya Kirkiro da wani asusu, wanda zai ragewa al'umma radadin talaucin da suke ciki, zai kuma ciyar da kasar gaba. Sunan asusun shine 'Petroleum Trust Fund' (PTF), sunan shugaban asusun daya nada shine Janar Muhammadu Buhari, sai wani mai suna chief Tayo Akpata a matsayin sakatare. An kuma kaddamar dasu a watan Maris na shekarar 1995. Daga nan shugaba Sani Abacha ya rinka turo musu da kudade, sukuma suna gudanar da ayyukan alheri.
Da fari, al'ummar Najeriya basu gaskata gaskiyar Shugaba Abacha akan wannan kuduri ba, amma daga bisani hakika kowa ya gani a Kasa. Ga misalan aikace-aikacen da Asusun ya gunadar:-
1. Fannin lafiya ya samu babban tagomashi, domin kuwa an gina manyan asibotoci a karkashin asusun, an kuma gyara kusan kowanne babban asibiti a kasar nan.
* Sannan an siyo Motocin daukar marasa lafiya (Ambulance) masu yawan gaske tare da rarrabasu izuwa asibitocin kasar nan.
*An tura da tabarau ga asibitoci don rarrabawa masu matsalar idanu kyauta.
* An siyo kayayyakin kula da masu cutar kanjamau tare da magunguna a karkashin shirin (HIV/AIDs Intervention programme), inda ake bayar dasu kyauta ga mabukata.
* An bude ofisoshin sayar da magunguna a karkashin tsarin (PTF drug Revolving fund) a duk manyan asibitoci, inda ake siyarwa da jama'a magani kasa da yadda farashin sa yake a kasuwa ko a sauran shagunan da bana gwamnati ba. Akan haka ne ma aka taba kama wani jami'in gwamnati yana son karkatar da akalar magungunan, daga karshe shugaban asusun Buhari ya fusata da hakan, sannan ya kai jami'in gaban kuliya inda aka garkame shi.
2. Gine-gine. Wannan asusu, yayi gine-gine masu tarin yawa akasar nan. Sannan an kawar da rashawa a tsarin kwangila, domin asusun yana kwace kwangilar sane ga duk wanda yayi masa wasa. Misalin gine-ginen sune;
*Ginin rukunin gidaje a wuse dake abuja(Residential estate) don sawwakewa ma'aikata mallakar muhalli cikin rahusa. *Fara Gina Matatar ruwa a okpella.
* Gina babban titin express dake tsakanin Enugu da onicha.
* Sannan an gyara wasu manyan tituna a sassan kasar. Inda aka zuba musu kwalta mai inganci tare da gina musu magudanan ruwa.
3. Ilimi. Wannan asusu ya samar da tallafi ga fannin ilimi. An gina makarantu masu yawa a cikin wannan shiri. Har yau gine-ginen dakunan karatu a jami'o'I da kwalejoji wanda asusun PTF ya gina suna nan dauke da tambarin asusun. Al'umma shaida ne, asusun ya rarraba littattafai da abin rubutu kyauta ga dalibai.
4. Abinci. Asusun ya samar da kayyakin abinci a farashi mai rahusa,inda ake siyarwa mutane a farashi kasa da farashin kasuwa.
5. Ciyar da tattalin arzikin kasa gaba. Wannan asusu yayi dabarar baiwa 'yan kasa kwangilar duk wasu ayyuka da zai gabatar. Sannan kuma yana sanya sharadin cewa dole ne dan kwangila ya siyo kayansa anan gida najeriya (sai dai idan abinda ake bukata ba'a yinsa a gida). Akan haka akace kamfanonin magani irinsu Emzor pharmaceuticals, dana siminti kamar Leferge dana fenti misalin IPWA ltd da wasunsu sun amfana har suna daukar ma'aikata. Wannan abu ya taimaka wajen kara habaka tattalin arziki, tare da samar da aikin yi.
6. Samar da motocin sufuri masu zirga-zirga da jama'a akan farashi mai rahusa a karkashin shirin (PTF subsidise commercial vehicle)
A karshe, Bayan rasuwar Janar Sani abacha, Shugaba Obasanjo ya sauke shugaba Buhari tare da nada mallam Haruna Adamu shugaban asusun. A wannan lokacin asusun na dauke da kudi sama da Naira biliyan dari. Shine akace Shugaba Buhari ya tara ma'aikatansa tare dayi musu jawabin bankwana, sannan yace duk wani abu da akeson bincikawa yana nan a rubuce. Daga nan ya sauko daga saman bene ya shiga motar sa ya nufi Daura.
Obasanjo yayi bincike matuka kafin ya rufe wannan asusu, amma duk adawar sa ga Marigayi Sani Abacha bai taba fitowa fili ya zargi asusun PTF ba, hukumar EFCC kuwa bata taba gayyatar Shugaba Buhari don tuhumar sa da almundahana a cikin asusun ba.
Dafatan Allah yajikan Janar Sani Abacha, Allah ya taimaki Shugaba Buhari akan shugabancin kasa da yakeyi. Amin
Daga Sadiq Tukur Gwarzo
08060869978

No comments:
Post a Comment