Sunday, 19 May 2019

LABARIN BOKONI, MAFARAUCIN DA YA ZAMA DUTSE

LABARIN BOKONI: MAFARAUCIN DA YA ZAMA DUTSE

Sadiq Tukur Gwarz, GGA
     08060869978
      A gabashin garin Rogo dake cikin jihar Kano, akwai wasu tarin duwatsu masu tsohon tarihi, waɗanda ake tsammanin wani abin mamaki ne ya faru har aka same su shekaru sama da dubu ɗaya da suka gabata.
Manya daga duwatsun sune ; Tayaka, Namijin Bokoni da Amaryar Bokoni.
Dutsen Amaryar Bokoni yana da tsayi da kuma doro, sannan a saman sa akwai kogo da kuma wuraren zama waɗanda kamar an yi sune don hutawa. Sai kuma wasu duwatsu masu kama da tanderu a ƙasa. Ana kiran kogon dutsen da suna 'Zauren Amaryar Bokoni'.
A saman dutsen Tayaka kuwa, wasu duwatsu ne a jere masu siffa irin ta buhunan hatsi.
Daga nam sai dutsen Namijin Bokoni da ke nesa kaɗan da waɗannan manyan duwarwatsu, wanda bishiyoyin kukoki suka yiwa geman ya.
Labarin Bokoni
Daga abinda muka ji a wannan yanki, Bokoni jarumi ne irin mutanen zamanin-da, zamanin da kusan maguzawa ke nuna jarumtar farauta a cikin kungurmin dazuka.
Don haka a wancan lokacin Bokoni ya tsallaka wata masarauta tare da neman aure. Kuma cikin sa a aka bashi duk kuwa da kasancewar akwai wanda yake matukar sonta.
Da aka yi biki aka watse, sai masu ɗaukar amarya suka taho da ita zuwa gidan Bokoni dake wannan yanki inda ya zama Rogo ayau.
Sai dai zuwan su keda wuya sai ga mahara sun yo gungu sun nufo su da nufin ɗauke amarya baki ɗaya. Wanda hakan ya tashin hankulan dukkan mutanen dake wurin.
 Ance tawagar Amarya nan take ta watse, kowa ya shiga neman mafita.
Anan ne Ango Bokoni ya shiga neman tsari daga abinda yayi imani dashi. Don haka akace ya roki rikiɗewa zuwa dutse tare da Amaryar sa.
Ance abinda ya faru kenan tsawon zamani da ya shige wanda zuwa yau sai dai tashin zance.
Daga bisani duwatsun sun zamo maɓoyar ɓanyan namun dazuka wamda har ta kai ga mitane na shayin gittawa ta yankin ma baki ɗaya.
Sai dai labarin yayi kama da abinda aka ce ya faru a Dutsen Amare dake Ƙasar Ƙaraye, inda ake iya hango alamar dutse mai kama da Amarya tayi lulluɓi. Da wasu duwatsun masu kama da gangunan kiɗa.
Don haka babu wani binciken kimiyya zuwa yau daya taɓa tabbatar da aukuwar irin waɗannan lamurori.
Amma dai  muna iya gaskata wuraren a matsayin tsoffin mazaunan maguzawa da suka rayu shekaru masu yawa da suka gabata.

No comments:

Post a Comment