Saturday, 4 May 2019

TARIHIN BAUCHI 6

TARIHIN ƘASAR BAUCHI
SADIQ TUKUR GWARZO
Kashi na shidda

Bayan rasuwar Sarkin Bauchi Yakubu sai ɗansa Ibrahimu ya gaje shi. Shikuwa sai da ya shafe shekaru arba'in bisa karagar mulkin Bauchi.
   A shekatar farko ta mulkin Ibrahimu ne ya tara runduna tare da tafiya Angas yaƙi. A can ne ya buga gagarumin yaƙi da mutanen, ya kashe na kashewa ya kama na kamawa, sannan ya koma Bauchi da ganima mai yawa.
   Babu jimawa sai ya sake fita yaƙi zuwa Montwal, yaje ya kore su sannan ya koma Bauchi da zama..
  A shekarar mulkin sa ta biyu ya tafi yaƙi da wani mayaƙi mai suna Hamza. Ya gamu dashi ya yaƙe shi, ya watsa taron rundunar sa, ya kashe na kashewa ya kama na kamawa, sannan ya koma gida Bauchi.
   Bayan shekaru biyu kuma sai ya ciri runduna zuwa Tabula, ya zauna a ƙofar ta tsawon shekaru takwas. A cikin shekara ta bakwai da zaman sa a ƙofar Tabula ne ɗan uwan sa Salmanu ya mutu yana tare dashi. Jim kaɗan da faruwar haka sai ya ƙulla amana da kafiran wajen mazauna dutse sannan ya koma gida.
   Sai dai, Ibrahim sarkin Bauchi ya koma gida da shekara ɗaya ne ya samu labarin cewa dukkan kafiran duwatsu sun warware amanar da aka ƙulla dasu.
  Don haka ya shirya yaƴi ya tafi Das da ake kira Bununu (sunan Sarkin su Mummini) ya yaƙe ta. Daga nan ya tafi Duwa tare da sarkin Kano da Sarkin Zaria da Sarkin Gombe da Shehun Borno suka yaƙe ta.
  Daga nan sai ya tafi Gamawa tare da Sarkin Kano suka yaƙe ta.
 Bayan wannan kuma sai ya tafi Duguri yayi yaƙi da mutanen ta, sannan ya sake komawa Das yayi yaƙi, ya ƙara komawa Duguri ya sake gwabba yaƙi.
   Haka kuma Sarkin Bauchi Ibrahim ya yaƙi Jimbim, amma daga nan bai sake fita yaƙi ba, sai ya tafi Rauta ya zauna yana aikawa da hare hare zuwa abokan gaba, har kuma ya nemi a tuɓe shi daga sarauta a ɗora ɗansa Usmanu.
   Abinda ya nema kuwa shi ya samu, inda aka naɗa ɗansa Usmanu sarki, ya koma Bauchi da zama, yayin da mahaifin sa Ibrahimu ya cigaba da zama a Rauta. 

No comments:

Post a Comment