Tuesday 12 December 2017

FALSAFA: WANZUWAR HALITTU A DUNIYOYIN SAMA

WANZUWAR HALITTU A DUNIYOYIN SAMA By Sadiqtukur Gwarzo. Duk da kasancewar ko anan duniyar mu ta earth, har yanzu masana na tababar sahihiyar hanyar da rayuwa ta wanzu, amma dai tun da jimawa binciken masana ya nuna lalle da alamar halittu masu rai dake rayuwa a duniyoyin sararin samaniya. Akwai masanan da suka tafi akan cewa asalin rayuwar mutum a duniyar mu ta faro ne daga cakuduwar qananun halittu nau'in bakteriya, yayin da wasu kuma suka jajirce akan cewa dukkan wani abu mai rai dake rayuwa a wannan duniya asalinsa zuwa yayi daga wata duniyar, dadai sauran zantuka da dama. Abinda ya fara tabbatar da wancan hasashen aukuwar rayuwa a duniyar sama shine dirar kumbo 'vickings' akan duniyar mars a shekarar 1976. Ance ya dira ne akan wani zagayayyen dandamali kusa da wani wawakeken rami wanda masana sukayi hasashen cewa shekaru biliyan hudu da suka gabata Ruwa ne tunjim acikin ramin. Hotunan da kumbon ya turo nan duniya kuwa sunyi nuni da shige-da-fice na iskokin numfashi ciki harda oksijin. Wannan yasa gungunn masanan da suka tura kumbon sukayi hasashen akwai halittu a boye masu numfashi a duniyar, har ma suka ce binciken nasu kamar misalin kaji sauti ne amma ka rasa abinda ya fitar da sautin. Wannan binciken kuma shine ya bude kafar samar da kirkirarrun labarai da fina-finai akan halittun duniyar sama misalin 'war of the world', Apes of the planet of the sun' da wasunsu, a Inda aka rinqa bayyana su da suffofi daban-daban. Wani masanin kimiyyar sararin samaniya mai suna Farfesa Chandra Wickarama, ya tabbatar da cewa akwai halittu masu rayuwa a sararin sama bayan wani bincike daya gudanar. Shine ma yake cewa "Hakika kauyanci ne ace mune kadai masu rai a fadin daukacin duniya (universe), ni inada tabbacin akwai halittu masu rai a wasu gurare da dama" Daga nan kuma sai ya kafa hujja da hotunan wata halitta mai kama da mutum-mutumi da wani madubin bincike mallakin Farfesa Milton Wainwright da tawagarsa ya dauko yana mai cewa irin wadannan abubuwa daga wata duniyar sama suka nufo duniyar mu, domin bazai yiwu ace daga wannan duniyar ya tashi sama ba. Shidai wancan mutum-mutumi an bayyana cewa yana tattare ne da sinarai samfurin kabon da oksijin, irin wadanda suke ajikin mutane. Kuma masanan da suke bincike akansa sunce abin yana yawo ne a saman duniyar mu da misalin nisan mil dari biyu daga dandamarin kasa. A ra'ayin Farfesa Chandra mutum ma asalinsa daga sama yake kamar yadda yake cewa "idan akayi la'akari da qwayoyin halittar dan adam na DNA, za'aga suna kamnceceniya ne da varus, kuma akwai yawa-yawan wadannan suffofi a sararin samaniya. Kenan zata iya yiwuwa tun daga can sama DNA suka fara harhaduwa sannan suka sauko nan kasa suka kara haduwa da kananun halittu, daga bisani suka rikita zuwa mutum. Manufa ta dai shine duk inda aka samu kananun halittu, to tabbas dayan uku ne. Kodai ace suna tare da manyansu, ko anyi manyan sun gabata, ko kuma a hankali zasu rikide zuwa manyan." A wata mukala da wasu masana biyu Dr. Seth shostak da Dr. Dan wethmer suka gabatar a gaban kwamitin binciken Sama na majalisar dokokin amurka, sunyi bajekolin manyan dalilan da yasa masana keda yakinin akwai rayuwa a duniyar sama, ga kadan daga ciki; 1. A shekar 1976, kumbon Vicking bayan dirarsa a duniyar Mars, ya hango wasu sinadaran mahadai masu nuni da wanzuwar Rai acan. 2. A shekarar 1977 kuma wani madubin hangen nesa na Jami'ar Ohio ya jiyo wani sauti kamar ance WOW a sama wanda har yanzu anrasa ma'anarsa. 3. A shekarar 1996 ne aka samu sawun halittu akan wani baraguzi babba daya duro Atlanta daga Sararin Samaniya. 4. A cikin shekarar 2001 da 2002 duk anjiwo motsin halittu a watan Europa na duniyar Jupiter. 5. Har ila yau, a shekarar 2007 wani mai bincike Joop Kooper ya gaskata ikirarin da wasu masana 'yan kasar Russia sukayi dangane da wanzuwar kananun halittu a duniyar Mars. Domin shima yace ya hango alamomin hakan. A wannan shekarar ta 2014 ne dai hukumar NASA ta ware kudi dala Miliyan Hamsin ga wasu gungun masa rukuni bakwai don yi bincike gami da samo amsar wasu tambayoyi guda uku da hujjoji kwarara. Ga tambayoyin kamar haka; 1. Shin akwai halittu irin mu dake rayuwa a daukacin duniya? 2. Shin wanne hali ke wanzar da rayuwa daga sinadarai? 3. Shin tayaya za'a iya gane abubuwa rayayyu dake a wajen duniyar mu?.. Allah ya bada sa'a Amin Daga Sadiq Tukur Gwarzo 08060869978

No comments:

Post a Comment