Friday 22 December 2017

TUNAWA DA ALH MUHAMMADU DANKABO

MARIGAYI MAMMAN DAN KABO: BA RABO DA GWANI BA..Tare da SADIQ TUKUR GWARZO

A ranar Litinin din nan, 4 ga watan Afrilun shekara ta2016 ne Marigayi Alhaji Muhammad Adamu dan kabo, tsohon Jarman kano, kuma wanda ya kirkiri kamfanin tashi da sauka na jiragen sama mai suna 'Kabo Air' zai cika shekaru goma sha hudu da rasuwa. Allahu Akbar, Allah ya jikan sa.Kafin rasuwar sa, an sanshi da fafutikar neman na kansa. Tarihi ya nuna irin gwagwarmayar daya sha har daga baya ya samu nasarar kafa kamfanin Kabo Air. Ya fara aiwatar da kamfanin tun yana aronjiragen sama, har Allah ya bashi damar mallakar jiragen sa na kansa. Hakika Marigayi Mamman DanKabo, mutum ne mara girman kai, mai taimakon addini da son talakawa musamman ma 'yan arewa. Labarun sa suna nan sun cika gari, kamar misalin wani lokaci da 'yan arewa suka taru a lagos suna son dawowa arewa domin aiwatar da bikin Sallah, gashi kuma saura jirgi daya ya rage a Airport, jirgin ma Dan kabon ne zai hawo ya dawo gida. Ance da zuwan sa ya bada umarnin cewa kowannen su ya shiga jirgin a kaishi kano kuma a kyauta. Da isar su kano kuma, kafin mutanen su sauka tuni yayi nasa wuri, domin yardar Allah yake buqata ba godiyar mutanen ba.Haka kuma Marigayi Mamman dan kabo gwani ne afannin kyauta. Idan kana jin labarun kyaututtukan sa, zaka iya cewa duk kasar hausa babu kamar sa. Shine Mutumin da yake biyawa 'yan rakiya kujerar Makkah sukutum har kuma ya basu kudin guzuri. Shine mutumin da duk makotansa da 'yan uwansa babu wanda bai bashi kujerar makkah ba. Har takai ga cewa a yanzu bazaka je kauyukan Kabo ba, har sai ka samu mutane sama da hamsin wadanda ya biyawa Hajji. Shine kuma wanda duk shekara yake cika tireloli da abinci ya aikasu garuwa domin arabawa 'yanuwansa da sauran mabukata.Marigayi Mamman dan kabo ya shahara wajen taimakon mutane. Yasha daukar dawainiyar karatun'ya'yan talakawa, ya taimakawa 'yan siyasa babu adadi wajen samun Nasarar su, ya kuma taimaki sarakuna da sauran kusoshin gwamnati.Da aka tambayi Maigirma Dan Masanin Kano Alh yusuf maitama sule akan marigayi Dankabo, sai yace "Abinda na sani akan marigayi Mamman dan Kabo shine yana da halin dattako da taimako ga dukwanda yazo gareshi. Gaba dayan mu zamuyi rashin sa. Allah yasa aljanna ce makomar sa"Alhaji Dr Aliyu Modibbo ma ya bayyana shi da cewamutum ne marar girman kai a wata firar sa da jaridar aminiya har yake cewa " A shekarar 1987, marigayi Alh Mamman dan kabo yaje Los ageles garin da nake karatu, sai wani abokin mu yace ga Jarma zaizo, inje in taryeshi a filin jirgin sama, babuwanda zai daukeshi. Na dauka wani tsoho ne, sai naje da motata na daukeshi, ashe yazo siyan jirgin sama ne a garin da nake wanda ake kira long beachcalifornia.."Marigayi Mamman Dan kabo mutum ne mai matukar bin iyaye tare da kyautatawa iyalan sa. Harma an taba ganin sa ya dukursawa Mahaifiyar tasa, ita tana zaune a bayan mota shi kuma yana waje alhali ana yayyafin ruwan sama alokacin. A haka ta zage gilas tayi masa maganganu, ya kuma amsa cikin girmamawa. Na kusa dashi sun tabbatarda cewa sam baya yin jayayya da umarnin Mahaifiyarsa, duk inda yake kuma da zarar ta kirashi zaizo gareta, sannan kuma yana farantawa ahalinsa.Marigayi dan kabo, dattijon arziki, abokin talakawa, abokin sarakuna, abokin attajirai, abokin sojoji, kuma abokin malamai. Shine Jarman kano, Hakiminkabo, Oruwase of Urhoboland, Adah Idah-ke Erubutuof Calabari, kuma shine Sardaunan Kagoro. Allah yajiqansa.Allah ya karbi ran wannan bawan Allah yana da shekaru sittin, sa'o'I kalilan bayan anyi bikin cikar sa shekaru sittin a duniya, ranar 4 ga watan afrilu na shekarar 2002. A lokacin kuma yana cikin kokarin gina filin saukar jiragen sama a Karamar hukumarsa ta kabo, abinda akayi hasashen zai janyowa kano da arewacin Najeriya arziki mai tarin yawa. Mutuwarsa ita ta hana gudanar da wannan aiki.A hakika, har abada sunan sa bazai daina amo ba, kuma ba za'a daina ambaton alherin saba. Hakika anyi rashin dattijon arziki mai halin dattako. DafatanAllah yayi rahama a gareshi, Allah ya albarkaci iyalinsa, Allah kuma ya baiwa attajiran mu damar koyi da aiyukansa na alheri. Amin

No comments:

Post a Comment