Sunday, 10 December 2017

TARIHIN BAKIN MUTUM 11

Tarihi: Asalin Bak'in Mutum da Mazaunin sa
   (Kashi na goma sha ɗaya)

Daga Sadiq Tukur Gwarzo

 Fir'auna Taharqa shine na hudu a sahun jerin bak'aken fata da suka mulki egypt. Sunan sa ya fito sosai a gurare daban-daban acikin littafin Babil mai tsarki. Ance Yayi mulki na tsawon shekaru 26, ya kuma yi gine-gine da dama da har yau tarihi ke tunawa dasu a egypt.
  Taharqa ya gudu daga egypt izuwa garin Napata, birnin da daular kushawa bakaken fata yake kenan, sa'ar da fafatawar egypt da Syria tayi tsamari. A lokacin mulkin sane mutanen syria suka yawaita kawowa egypt hari da niyyar kwace ikon garin tare da fadada k'asar su. Amma ance daga baya ya dawo a shekarar 669BC, inda bai jima ba kuma ya kara komawa Napata, acan ya mutu.
  Tantamani shine aka bayyana a matsayin dan Taharqa. Shine kuma akace Fir'auna na karshe a jerin bakaken fatar da suka mulki egypt, domin ya samu nasarar kwace kasar daga hannun siriyawa, wadanda suka karbe mulki daga wurin mahaifin sa, amma daga baya siriyawan dai suka k'ara cin galaba a kansa, suka kori kushawa izuwa Napata, garin dake kudancin egypt.
   Masana tarihi sun fadi cewar karyewar daular syria a shekarar 590BC ya baiwa egypt damar korar siriyawa daga garin su tare da d'orawa da mulki. Ance sunan Fir'aunan daya kwace mulki Psamtik. Shine kuma bayan ya fara mulki yabi kushawa har daular su dake Napata ya fatattake su tare da rusa garin saboda samun labarin da akace yayi na cewar bakaken fata na shirye-shiryen sake kawowa egypt yaki.  A wannan lokacin ne Bakaken fata suka gudu tare da dawo da daular su garin Merwa (Meroe), wanda ke kasar Sudan a yau.
   Akwai sabani da dama dangane da kafuwar wannan gari na Meroe tare da dawo da daula izuwa gareshi. Farfesa Joshua J. Mark yayi bayanin cewa garin Merwa ya kafu ne a tsakankanin manyan hanyoyin fatauci, sannan kuma ya samu k'asaita a tsakankanin shekara ta 800BC zuwa shekara ta 350 miladiyya.
  Shine ma har yake cewa "akwai k'arancin sani a game da yadda garin Merwa ya girma tare da shahara. Amma dai an samu cewa birnin ya bunk'asa da arziki a wancan lokaci har takai ga sarkin Farisa Cambyses ya taba yin hawa da niyyar zuwa garin don kwace ikon sa, amma saboda wahalar sahara bai samu damar karasowa ba."
  Idan kuwa har wannan maganar ta tabbata, muna iya fahimtar cewa garin Merwa ya kafu ne akan hanya, tsakanin daular Napata da kuma wasu daulolin dake baya da garin, wadanda a yanzu bamu samu labarin su ba.
   Amma dai, dangane da Merwa, akwai wani zancen kuma, wanda aka bayyana cewar a shekara ta 666BC ne sarkin daya gaji sarkin kushawa Aspelta ya dawo da masarautar sa garin Merwa bayan dakarun egypt sun tarwatsa garin Napata kenan. Yayin da wasu ke cewa arzikin Merwa ne ya janyo hankalin sarakunan ta suka dawo uzuwa garin.
   Atakaice dai, mulkin kushawa ya jima a garin Merwa. Kusan duk wani dabi'u da al'adu na mutan Egypt d'aya ne dana mutanen Merwa, tun daga kan bautar allolin gumaka, makarantun ilimai, siye-da-siyarwa, sanya matattun sarakuna a kaburburan pyramid, da sauransu. An samu cewa mata sun taka rawar gani sosai a mulkin daular Merwa. Akwai sunayen Sarauniyoyi mata da yawa a jerin wadanda suka mulki Merwa. Ana musu lak'abu ne da kalmar 'Kandake'. Kuma mafiya yawan dakarunsu suna amfani ne da kwari da baka masu dafi, kamar dai yadda aka samu a wuraren maguzawan da suka rayu a yankunan mu shekarun da suka gabata. Sannan kuma an rink'a samun yak'i yana faruwa a lokuta daban-daban tsakanin egypt da Merwa.
    A karni na d'aya miladiyya ne kabilar Beja (Medja) ta kwace mulkin merwa. Itama bakar fata ce ba bakuwa bace, kuma tayi kokarin k'arawa masarautar daraja. Amma dai ance kafuwar daular Aksum a garin Adulis dake yankin Ethiopia a yau ya kawo rarrabuwar daular izuwa biyu tare da fara dusashe garin Merwa.
Koda  yake, dangane da masarautar Aksum, nan ma akwai maganganu masu tarin yawa akwn ta. Amma dai a takaice, ance garin Aksum ne ya fara kafuwa lokaci mai tsawo, kuma ance wani mai suna Za-Haqala shine sarkin garin na farko. A hankali ya rinka fadada garin, har yayi karfi tare da ballewa daga daular kushawa. Daga baya ne daular ta koma birnin Adulis da kafuwa.
  A karni na hudu miladiyya ne kuwa akace Sarkin daular Aksum mai suna Ezana ya dira a Merwa tare da rusa ta. Ya kone garin kurmus. Wannan yasa mutanen garin suka fantsama izuwa makwabtan garuruwa don neman tsira. Tun daga wancan lokacin kuma labarin Merwa ya shafe a doron kasa, sai yanzu da masana suka dira a yankin suke sake tunowa dashi..
  Alhamdullahi. Anan zamu dakata da wannan rubutu. Godiya ta tabbata ga Ubangijin Talikai wanda shine mafi sani ga dukkan bayi. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad (S.A.W).
Daga Sadiq Tukur Gwarzo
        08060869978


No comments:

Post a Comment