Sunday, 10 December 2017

TARIHIN TSOHON BIRNIN HAUSAWA: GODIYA

Tarihin Tsoffin Biranen Hausa: Baɗari da Goɗiya.

  Daga Sadiq Tukur Gwazo

Garin Goɗiya
   Garin goɗiya nan ne ake cewa idan kayi dare yayi anajin sawun wucewar wata macijiya sark'a rakwachaf-rakwachaf sannan kuma ana iya haduwa da wata goɗiya ja dake zaz-zagayawa kwararo kwararo na garin. Shine garin da har gobe ba'a shiga da Amarya ta kofar fada, idan kuwa aka shiga da ita an canfa cewa mutuwa zatayi babu jimawa.  Har ila yau, nan ne tsohuwar daular hausa, cibiyar kasuwanci, garin jarumai da mayaka.
  Tarihi ya nuna cewa wani Bamaguje mai suna Goɗiya ne ya fara zama a garin, don haka shine wanda ya sari garin kenan. Wasu mazauna garin sun shaida min cewa garin goɗiya ya girmi garin Kano da kafuwa da shekaru Arba'in, kuma goɗiya da Bagauda wanda ya sari kano suna da alaka duk dadai zuwa yanzu ba'asan alakar tasu ta jini bace ko kuwa ta kabila ce.
    Koda yake, tana iya yiwuwa tazarar kafuwar garin kano da goɗiya yayi kasa da shekaru arba'in, domin kuwa mutan goɗiya sun tabbatar da cewa garin Baɗari ya girmi garin nasu da kafuwa, sannan kuma a baɗari an sanar damu cewa Bugau wanda ya sari garin yaya ne ga bagauda, kuma ya kafa Baɗari da shekaru takwas sannan Bagauda yaje ya kafa kano. Idan kuwa haka ne, tana iya yiwuwa tazarar kano da Goɗiya shekaru huɗu ne rak ba arba'in ba kamar yadda suke fada.
    Amma dai abune mai muhimmanci da sha'awa shiga tsohon gari irin Goɗiya. Tun daga nesa na fara hango alamomin dake tabbatar da tsohuwar rayuwa ta maguzawa a yankin, kamar kwatankwacin alamomin da na gani a Baɗari da kuma tsohon Birnin Guɗe.
  Wasu abin tunawa a garin shine rijiyoyinsu masu tsohon tarihi. Rijiyoyin uku ne, akwai wata mai suna Ilallawa, sai kuma Gawo da Holo. Tarihin su ya gushe a bakin mutane. Wani dattijo mai shekaru sama da ɗari da haihuwa ya shaida min cewa babu wanda zai iya sanar dakai lokacin da aka haka rijiyoyin.
   Amma shaharar garin wajen yaki da kasuwanci da tsubbu irin na maguzawa har yanzu bai gushe a zukatan mazauna garin goɗiya ba.
    Wani ya fada min cewa ba'a taɓa cin garin da yaki ba, sannan kuma duk shirin mutum ba'a ciwa goɗiya alwashi. Dana tambaye shi karin bayani sai yake cewa" Garin goɗiya nada ganuwa da kofofi waɗanda idan yaki yazo duk mutanen birni da kauye ke tururuwa izuwa ciki, sai a kulle garin. Sannan duk wanda ya nufo garin da sharri to bazai ganshi ba, tun daga nesa zai ga garin ya bace bat."
   Dangane da kasuwanci kuwa, wani ya faɗa min cewa a tarihi, ada can, duk yankin nan babu wasu manyan garuruwa sama da Kano, Goɗiya da kuma Baɗari. Don haka daga nesa akeyo takakka izuwa garin don siyan kayan masarufi.
   Wani kuma ya kara tabbatar mini da cewa ko sanda garuruwa irin su karaye da shanono suka kafu, garin goɗiya suke zuwa su sayi likkafani idan anyi musu rasuwa. Sannan har yanzu akwai Gidan karofi, inda akace bayin sarkin kano ne suka zo suna yin aiki a wajen tun asali. Sannan akwai Gidan Kunge, inda akace asali Kungen shahararren maɗinki ne, da kuma gidan Qwalwa, wanda shima akace mutum ne wanda ya shahara a sana'ar rini da bugu.
   Amma fa a harkar kafi irin na gari (ko ace tsubbu), wannan abu ne tabbatacce cewar maguzawan asali suna da wasu sirrika da suke amfani dasu wajen cimma burikansu.
  Har yanzu ance ba'a iya fitar da doki idan dare yayi daga wata unguwa mai suna 'yan sarki. Domin na hadu da wanda yace min ya gwada haka yafi sau huɗu. Idan nima inaso nazo ya bani na gwada. Sai nace masa nagode.
 A cewar sa, idan kazo tsakan-kanin katanga-da-katanga na fita daga garin kana bisa doki da dare, sai dai kawai kaga dokin yayi rimi sama yana kokarin yadda kai. Kuma duk yadda kayi bazai wuce ba, kai kace wani abin tsoron ya hango yake hanashi tafiya.
  Zuwa yanzu dai, babu takamaimen tarihin asalin abinda ya faru har aka yi wannan abu mai hana dawaki fita daga unguwar.
   A fannin mulki kuwa, ance godiya tayi suna tsawon zamani daya shude. Gashi ma har yanzu tsoffin tamburan ta guda uku suna nan, babu kuma wanda yasan lokacin da akayisu. Koda yake, wani zance ya nuna kamar musaya akayi da tsohon tambarin goɗiya da kuma na kano. Wasu suna ganin asalin Goɗiya tambari ɗaya gareta na azurfa wanda idan aka buga shi har a kasar katsina ana jinsa. Daga baya sai kano tayi musayar su da bada nata guda biyu, ɗayan tambarin kuwa yana iya zama na garin baɗari ne, dalilin zuwansa kuma na iya zamowa silar auratayya ko yaki kamar yadda ya faru tsakanin Baɗari da Getso.
    Amma dai, abu mafi sha'awa a goɗiya shine dutsen 'Yar Maradun. Na jima ina jinsa, sau a bana muka hadu.
   Wannan dutse yana dauke da sawun kafar mutum ne. Da kuma sawun goshi.. Sai kuma dutsen ya rabe biyu tsakanin inda sawun goshin yake da kuma sawun tafin kafar. Daga wuri-wuri akace mutane ke zuwa su kwakuli sawun domin neman tubarraki.
   Labaru kala-kala naji game da wannan abin al'ajabi.
Shahararre ciki shine cewar:- Wannan Sawu Na Annabi Muhammad (S.a.w) ne yazo wajen yayi Sallah. Inda dutsen ya rabe biyu kuma akace wai inda ya ajiye takobinsa ne.
  Duk dadai bamu taba jin wata ruwaya data nuna cewar Annabi Muhammad (S.a.w) yazo wani uzuri kasar Hausa ba, amma nafi ganin Wannan zance ne na Malamai..
  Ana yiwa goɗiya kirari da "Gyarai Tsohon nama, Goɗiya ta ɗan Tama mai gezar alharini, tsintsiya maɗaurinki ɗaya kowa yajeki sai ya dawo..
 
    

No comments:

Post a Comment