Sunday, 10 December 2017

LABARIN BAWA DORUGU 1

YAKE-YAKE DA KAMEN BAYI A KASAR HAUSA: LABARIN BAWA DORUGU; BAHAUSHEN FARKO DAYA FARA ZAGAYA TURAI.
 
Gabatarwa
Wannan labari, Dr J. F Schon ne ya karbe shi daga bakin shi kansa
Dorugun a shekarar 1883 aka wallafa shi a kasidun kasar england a wajejen shekarar 1885. An karbi labarin ne kuma ta hanyar Dorugu yana bada labarin a cikin harshen hausa, shikuma Dr Schon yana rubutawa da turanci. Sannan kuma shi wannan Dorugun, bawa ne bahaushe wanda mai binciken sassan Africa ta yamma Dr Barth ya siya yana kan hanyarsa ta komawa gida Germany bayan zuwan sa kasar hausa, kuma ya isa dashi England da Germany a wajejen shekarar 1856. A wajajen shekarar 1906, ance turawan mulkin mallaka sun dauki Dorugu aikin koyarwa, inda ya rinka koyar da dalibai a garin Zangeru dake arewacin Najeriya.
Don haka wannan labari somin tabi ne kafin mu kawo muku tarihin zuwan Dr Barth da wani abokin sa mai suna Adolf Overweg kasar hausa tun a wajajen shekara ta 1850.
Asha karatu lafiya.

  YARIN TAR DORUGU

  Dorugu ya fara da cewa " Sunan garinda aka haifeni dambanas, kusa
ne ga birnin kanje, domin  tafiyan yini daya ne kacal tsakani daga
dambanas.  Ubana ya zamo a tare da uwata kuma sunansa kwage.  Amma  adam ne ainihin sunansa; sunan uwata kuwa kande. Ta haifi kanena, Bakurau, da kanwata Simanta ana ce mata Ta- roko. Mu wadannan uku anhaifemu a gari daya.
Ubanmu ya zamna a garin nan shekaru dayawa yana kidi da dundufansa ;
yana yin kuma aiki a gonarsa karama ; amma mu bamu iya yin aiki ba
kwarai, don bamu girma ba.
   Da naga ubana da uwata suna yin wahala a gona sai nacewa ubana :
Inaci inasha amma bana iya yin komi? ina so ka bani baiwa in yi noma, yace mani, kai ba ka girma ba ga aiki, ka
zamna har shekara maizuwa, kana im baka baiwa ka yi aiki.  Amma ina,
sai  na fara yin kuka, don ina so inyi aiki. Da muka taffi gidda, sai ya fadi ga
makiri (mai sana'ar kiri), ya kira mani baiwa, sai kuwa makiri ya kira
mani baiwa, da ya kare, sai ubana ya kawo mani, ni kuwa sai murna.
   Da gari ya waye muka tashi, muka taffi da safe zuwa gona.  Uwata ta zamna a gida tana yin tuwo ; da nufin kadan ta kare, ta kawo mana ga gona.
Idan sun tsaya  chin tuwo, ni ba na so in tsaya inci tuwo, don ina jin dadin noma.
Ubana  yakan taffi, ya kirawoni, har yakan ce kaci mana, kaci tuwonka,
mufa  mun kare namu, kana sai in tafi, inci tuwona.
    Da muka ga shekarar nan babu hatsi dayawa a cikin gonar nan, Sai ubana ya bar gonar, yayi wata kusa a gida. Da muka noma wannan ta kusa da
gida mun samu hatsi, amma ba dayawa ba. Bari ma, muna da wota gona ta
auduga. Koyaushe dani da ubana muna zuwa nan; amma kanwata ba ta
lafiya. Rannan uwata ta  tafi tare da mu, da maraice yayi  muna kan dawowa daga gonar auduga, sai na gano kanena dagga bisa tudu (yana dagga cikkin gidda) da wani yaro karami a tare da shi. Uwata ta ce ga ubana : wannan Bakurau ne da Taroko ! mun yi mamaki, mukace, kaga ta
samu lafia har ta fita waje tana yin
warginta? Amma da muka isa cikin giddan, sai na gani yaro nan ba kanwata
bace. Na yi gudu na shigga  cikkin daki, na kira sunanta, nace taroko
! taroko ! Amma ban ji  ta amsa ba. Sai na tabbata, bata yin  motsi.
Ga wurinda ta kwanta duk ya cika da dalale ; kana na sani
ta mutu ; na yi kuka sosai.
Da ubana ya gani, sai ya dauketa, ya dubeta bar hawaye suka zuba kasa
daga idanuwansa.  Uwata kuwa tana ta yin kuka ; amma kanena bai san
komi ba, kasan yaro ba wayo.
  Ubana ya tambayeshi : ka bata
fura ? yace, eh, ka bata ruwa ? ya che, eh. Sai ubana baice komai ba.
Can kuma sai yace, tundan bata mutu ba da yunwa to da kyau. Ya kira
wani abokinsa ya che masa ya gina masa kushewa abizne ta a ciki. Da
mutumin  ya gina kushiwar sai ya sanya
itace daga chiki. Aka rufeta da zane, ya
dauketa, ya kaita, ya sata a chikkin kushiwa ya dora itace dagga bisa
ga bakin kushewar, ya rufeta duka da itache, kana ya zuba kasa dagga bisa, ya lufeta da kyau.
   Da muka kwana  gari ya waye, ubana yace ga uwata : me zamu saya mu
yi mata sadaka? sai ta che masa, mu sayi wake dan ayi  abinci, akai
gaban manyan mutane, ya che, da kyau.
Ya taffi ya sayo wake, ya kawo mata.  Ta dauko hatsi tayi fura, ta dafa wake; muka
dauka muka kawo gaban  manya mutane a dandali. Da suka ci wake suka
sha fura suka kare, sai mallamai sukayi alfatiya, muka taffi muka zamma.

LOKACIN YAKI

Bayan mutuwan kanwata sai naji labarin yaki yana zuwa ga garinmu. Muka
tashi da dare, muka gudu tafiyan kwana biyu ko uku. Ashe, labarin
karya ne ba gaskia ba. Da gari ya waye mutane suna ganin diyansu sun
gaji da tafiya; ni dakaina ina yin kuka sabida gajiya, kadan anji
jariri yana kuka sai  ace
ga uwasra, ki bashi nono ya sha, don ya yi kawai !
Da muka zamna dagga cikin daji, ina tsammanin wadansu mutane sun dawo
cikin gari sai suka ga garin mu babu mutane shine
suka  dawo suka   fada mana
amma akwai wani mutum, maisata, ya zauna daga cikkin gari, ya sace
abubuwa da yawa kuma ya
zauna har muka dawo. Sai dai da muka dawo sai muka samu garin mu
ankoneshi da wuta, ashe barawo maisata shi ne, yasa wuta ga gari ; sai
giddan ubana, da giddan wata tsohuwa, sune, wuta ba ta tabasu ba. Amma
mun tarar da dakin ubana,
jaki, da awaki, da tumaki, da kaji sun shigga
ciki suna wargi.
Da muka samu garinmu babu abu da ya tabashi sai wuta sai muka shiga
muka zauna, mata suka shiga
neman tukwanensu, ba su samu ba har suka zagaya ga giddan mutumin nan
suka samu tukwanensu
daure acan. Sai kowacce mace ta dauki tukunyarta ta taffi ga giddanta.
Mafarin jin labari yaki ke nan.

#SadiqTukurGwarzo
08060869978

No comments:

Post a Comment