Sunday, 10 December 2017

LABARIN BAWA DORUGU 7

LABARIN BAWA DORUGU, BAHAUSHEN DAYA FARA
ZAGAYA TURAI
Kashi na bakwai.
Daga Sadiq Tukur Gwarzo
Dorugu yaci gaba da cewa ;-Da muka gama shirin zuwa
Timbuktu sai muka tashi. Kwanan mu ashirin muna
tafiya daga kukawa, kana muka isa zinder. Muka zaga
ciki, suka bamu gida muka sauka.
Zinder gari ne Karami, amma yana da girma, don sun
gewaye shi da dutse. Da muka zauna a garin nan naga
mutanen garinsu kakata. Na sami wani yaro abokina
nace masa ya tafi ya fadawa kakata ina cikin zinder,
don ta sanarwa Ubana yazo ya daukeni, yanzu Da nake
ba bawa ba. Sai dai banyi tunanin dan aiken ya tafi ba!
Don banji labarinsa ba, amma akwai wadansu mutane
hausawa da sukace nabisu zasu kaini ga ubana, sai
naki yarda, don kuwa ina jin tsoron zasu iya sayar dani
na koma bauta.
Da muka tashi daga nan, sai muka zaga muka kwana a
bayan gari. Anan ne naga turba mikakka wadda take
kaiwa izuwa Kundawoshe, garin kakata. Na nunawa
Abega nace masa kaga turbar nan har garin kakata.
Muka tashi daga wurin nan muka shiga wajen Kanche,
na tambayi wasu mutane nace "ko kunsan ubana?"
Sukace yaya sunan sa? Nace "sunan sa kwage".
Sukace kai dan kwage ne mai kidan duddufa?" Nace
musu "I". Suka ce ubanka ya zago nan jiya, ya dawo
daga kanche. Da naji haka sai naji tausayi.
Nan ma muka tashi muka shiga daji, daga nan muka
zaga cikin birnin katsina da marece. Muka tsaya a
bayan birnin, wadansu mutane suka shiga cikin birni
suka fadi ga Sarki cewa akwai baki a wajen gari, Sarki
ya bada izini aka nema mana gida, sannan muka shiga.
Gidan mu shigifa ne, anyita da tavo. Katsina gari ne
babba, yana da itace. Amma shashin garin babu
mutane, don yaki ya watsa su ( Tarihi ya nuna cewa A
wannan lokacin Maradi da Katsina suna adawar yaki
sosai), ga gonaki a cikin gari, daga nan ne akwai
itatuwan rimi da yawa masu tsawo. Da audugansu ake
yin lufuda da alfayami na kyasta wuta. Acikin gidanmu
wani balarabe ya mutu wanda ya biyomu tun daga
borno, sunansa sherif. Muka fadi ga sarki, sarki yasa
aka gina masa kushewa a cikin gidan da muka sauka.
Aka sashi cikin sabon alkamura, aka gyatta shi, sannan
aka sakashi cikin kushewa.
Sharif shine kaman mutumin Allah, don kowanne
mutum baki yana cewa idan sharif yasa hannunsa a
cikin wuta bata konashi, na tava jin labarin wani sharif
daya sami yara suna kama kifi, sai suka sashi acikin
wuta, sai yasa hannun sa acikin wutar, ya danko kifin.
Karya ne ko gaskiya ne ban sani ba.
Kasuwar katsina da kyawun gani take. Suna sayar da
nama, zannuwa, auduga da-dai abubuwa masu yawa.
Da zamu fita daga katsina, saida mutane da yawa suka
bimu don suyi mana rakiya kamar yaki, don dajin nan
bashi da kyau, domin akwai mutane masu taren hanya.
Da safe ne muka tsaya ga wani wuri da akwai ruwa,
muka dauki ruwa bisa ga rakuma, muka wuce mukayi
tafiya rana duka, har rana ta fadi, da dare yayi muka
tsaya don mu huta kadan.
Da safe muka wuce, amma fa rakuma sukaki tafiya
saboda kishirwa. Sai mai doki ya sauko daga doki ya
kora rakumi, idan doki yaki tafiya ya kwance sirdin
dokin ya dora aka, sannan ya kora dokin nasa. Idan
kuwa doki karfinsa ya kare, sai ya fadi. Ka wuce
kabarshi. Haka mukai ta tafiya daga safiyar nan har
marece. Muka iske wani gari na manta sunan sa,
amma yana da mutane, gashi da kyan gani.
Muka kafa lemomin mu a bayan garin. Kwanan mu
kamar biyu anan, mutanen garin suna kawo mana
abubuwan saye kamar su gujjiya, hatsi, albasa, barkono,
igiya da wasu abubuwan da yawa, har ma da irinsu
ciyawar dawaki, harawar rakumi ko wake, sai mu kuma
mu basu kudi da allura.
Da muka tashi daga nan, sai muka shiga wani daji
amma babu abin tsoro sosai. Da marece muka isa wani
gari inda Sarkin sokoto yayi shirin yin yaki dasu. Muka
kafa lemar mu kusa da inda sarkin Sokoto ya kafa
tashi. Sarkin sokoto ya aiko mana da raguna hudu don
nama da kudin kasa ya bamu taiki biyu (saidai dorugu
bai san kyautar da wannan tawaga tasu tabaiwa Sarkin
ba). Da muka kwana anan da dare kuraye suka zo,
wani balarabe ya ganosu, yayi ihu yace da maganar
arab "azurub!, azurub!" Ma'ana "ku harba, ku harba".
Samarin mu suka tashi maza suka harba bindiga, suka
tambayeshi menene? Yace "Kura!". Suka fashe da
dariya. Suna tsammanin barawo ne da fari. Ni kuwa sai
naji tsoro da naji kurace, don a waje muke kwana.
Dama ina da wani zane, sai na nadeshi kaman kamu
biyu a wajen kafafuna harma yafi kaina girma. Wani
saurayi ya tambayeni da borno "afi nanga ate?" Wai
don mi kayi haka? Nace "in kura tazo, idan ta gani
zatayi tsammanin wajen tudun can kainane, ni kuwa da
naji tana gwaguiwa sai nayi Kara".
Munyi kwana biyu anan, sai muka tashi muka cigaba da
tafiya. Muka sauka a wani gari wanda idan sarkin
sokoto ya gaji da zaman cikin birni, yake ziyarta don
hutawa. Anan muka zauna har sarki ya dawo daga
yakin daya tafi. Ina tsammanin mun zauna wata biyu
anan. Wannan gari yana da dadin zama, acikin sa
akwai mutane masu yin fulatanci, amma dai sunfi yin
hausa. Idan munce "wannan" sai suce "wanga".
Har wani yaro ya tambayeni yace "ina tsammanin kai
ba bahaushe bane, don harshenka ba kamar namu bane
mu sakkwatawa". Nace masa na san hausa kwarrai don
ni ba-tuntume ne, amma kai dan sokoto ne. Daga nan
sai muka shiga sokoto, sarki ya bamu gida nagari.
Kullum sai mu daurawa Abdulkarim sirdi mu shiga zaga
gari. Garin yana da girma, amma ba acike yake da
mutane ba. Suna da shanu daban dana Inliz. Shanunsu
masu tozo da tsawon kafa ne, bayansu kamar na
bauna, abu daya da zance daban da tumakinsu kuma
shine suna da tsawo.
Mu bamu iya yin zane da gashin tumakin mu, amma
mutanen Timbuktu sunayin zane da gashin tumakinsu
don yana da tsawo kamar tumakin Ingila. Tumakin
larabawa kuwa suna da gashi, wutsiyansu nada girma...
Daga nan sai muka tashi, muka zagaya ta wani gari
sunan sa Gwandu. Kwana hudu ko biyar daga sokoto.
Garin nan nada girma, kuma daga cikin dutse yake,
amma tsammani na suna jin tsoro don suna kusa da
daji. Suna yin maganar hausa kamar sakkwato, muka
zauna kamar wata daya ana, daga nan muka tashi
muka zaga wani gari ana kiransa Birnin Kebbi. Muna
zuwa wajen faduwar rana muka ji ihu daga wata
unguwa nesa garemu. Ashe yaki ne. Ina tsammanin
babu wanda yaje ya tayasu, suka cinye garin suka
tafi......

No comments:

Post a Comment