Sunday, 23 September 2018

Tarihin Sarkin Kano Abbas

Sarkin Kano Muhammad Abbas

Sadiq Tukur Gwarzo
   Shine sarkin Kano na hamsin da ɗaya, kuma na takwas a jerin Sarakunan fulani da suka mulki Kano. Shi ɗa ne ga Marigayi Sarkin Kano Abdullahi Maje Karofi, watau ƙani yake ga Galadima Yusufu da kuma Sarki Alu Babba.
   Babu takamaimen lokacin da aka haifeshi kasancewar Hausawa basu cika kiyaye ranakun haihuwa ba a wancan lokacin, amma dai an samu cewar ya zama sarkin Kano a watan mayu na shekarar 1903 miladiyya har kuma zuwa shekarar 1919 bayan rasuwarsa aka binneshi a Nassarawa (daga nan ya samo sunan Maje Nassarawa) sai ɗansa Shehu Usmanu ya gajeshi.  Gwamna Lugard ne ya naɗa shi sarauta sa'ar da yaci kano da yaƙi.
  Ga yadda hawa mulkinsa ya kasance:
Kamar yadda aka sani, Mabiya Galadima Yusufu sunyi bore ga Sarki Tukur bayan rasuwar Sarki Muhammadu Bello, wanda ya kai ga yaƙin Basasar Kano. Daga bisani aka hallaka Sarki Tukur, Alu ƙani ga Galadima Yusufu wanda ya rasu a Garko tun kafin soma yaƙin, ya zamo Sarkin Kano. A wannan lokacin sai ya naɗa ƙaninsa Abbas muƙamin Wambai.
   Ana haka sai turawa suka zo kano, sarki Alu ya shirya tafiya Sokoto tare da tawagarsa tun kafin isowarsu, ciki kuwa harda wambai Abbas, inda ya danƙa amanar gari a hannun Sarkin Shanu.
   Bayan Sarki Alu ya juyo daga Sokoto, sai ya sauka a ƙasar zamfara, anan ne kuma mai ɗakinsa tazo da dare a sukwane ta sanar masa cewar turawa sun ƙwace iko da kano, wanda a cikin daren yayi hawa a ɓoye ya bar jama'arsa.
   Koda gari ya waye sai ragowar mutane suka shiga neman Sarki Alu, amma rasa shi da sukayi yasa suka yanke shawarar cigaba da tafiya zuwa kano. Inda a yankin kwatarshi wannan runduna ta haɗu da turawa masu neman Sarki Alu, waɗanda bayan sun karɓe ikon Kano suka nemeshi suka rasa, sai suka bar wasu turawan riƙon kano, suka biyo sahun Sarki Alu zuwa Sokoto.
    Waziri Amadu ne ke jagorancin wannan tawaga, anyi wannan haɗuwa ne kuma a wani daji da ake kira 'Dajin Rubin' (Tana kuma iya yiwuwa turawa ne suka sanyawa dajin wannan suna saboda mutuwar ɗanuwansu Reuben a dajin)
  Da gamuwar su sai faɗa ya kaure a tsakani. Aka soma fafatawa, dakarun waziri Amadu suka afkawa turawa da sara da suka, yayin da suma turawa suka mayarwa da dakarun martani da harbi.
   Sai dai cikin abinda baifi awa ɗaya ba, turawa suka karya lagon wannan tawaga suka kuma watsa ta. Ya zamana an kashe wasu, wasu kuma suna zube a kakkarye harsashi yayi misu lahani, yayin da saura suka shige daji da gudu suna masu neman tsira da rayukansu..
  Anan ne Wambai Abbas ya jagoranci wata tawaga suka gudu daga wannan yaƙin tare da nufowa birnin Kano.
  Sai dai tun kafin su iso, tuni har labari yazo ga turawan da suka rage a kano, waɗanda aka barsu a gari da zimmar su tsare garin tunda sun karɓe iko dashi.
   Ai kuwa tun kafin dakarun su iso, sai turawan suka haɗa tawaga suka nufi wajen ganuwa, suka jejjeru suna sauraren su.
   Bayan misalin awa guda suna jira, sai ga dakarun sun karaso.
   Turawan nan suka tsaida waɗannan dakaru, sannan suka karɓe dukkanin makaman dake jikkunan su.
  Daga nan aka basu damar shiga garin kano bisa sharaɗin kowa gidansa kurum zai nufa, banda kuma yinkurin tada tarzoma.
  Anyi haka a lokacin tsakiyar sanyi na wannan shekarar.
   Daga nan kuma, sai Turawa bayan sun koma gida suka shiga neman shawarwari daga gurin Larabawa mazauna kano akan wanda ya kamata a naɗa sarki a kano musamman wanda ya fito daga zuriyar Abdullahi Maje Karofi.
  Sai larabawan nan sukace ai kuwa Wambai Abbas ne yafi dacewa, tunda babban su waziri Amadu ya rasu.
  Sai turawa suka amsa da cewar haka nan ne.
 Sai dai fa duk da haka, turawa sun shiga tambayar Manyan kano na wancan lokacin dake zaune a birni, cewar wa ya dace ayiwa sarki, sai suma ɗin kuwa suka ce abaiwa Wambai Abbas sarauta.
  To kunji yadda sarki Abbas ya zama sarki na farko a kano a zamanin turawa. Shi suka ɗorawa nauyin kwantarwa da mutanen Kano hankali ma zamanin, sannan ya rinƙa kiran duj waɗanda sukayi hijira saboda zuwan turawa Kano su komo gida.
   A zamanin mulkinsa jirgin ƙasa ya soma zuwa kano, har wata rana turawa suka buƙaci yahau domin a ɗana shi.
   Ai kuwa Sarki Abbas yahau jirgi, mutanen Kano duk suka firgice dube da jin kuwwarsa, wadda basu taɓa jin irin taba.
  Labari ya nuna cewar har mutan kano sun fara zunɗen cewa turara ƙarya sukeyi, wayau kawai sukayi domin su tafi da Sarki Abbas su kashe, amma daga bisani sai Allah ya dawo dashi gida lafiya.
   Har ila yau, a zamanin sa ne aka tara ɗaukacin sarakunan Arewa a kano domin tarben wakilin Sarkin Ingila, shine ma har Sarkin Zazzau na zamanin Shehu ya rera shahararrar waƙar nan tasa mai taken 'Zuwan mu Birnin Kano'.
  A zamaninsa har ila yau aka gins makarantar Elemantare ta farko a kano, aka soma shirya gidan tarihi na Kano tare da wasu ayyuka masu yawa.
  Haƙiƙa Sarki Abbas yana da karamci da son jama'a, kuma yayi matuƙar ƙoƙarinsa wajen kare haƙƙin Kanawa daga turawa masu mulkin mallaka a zamaninsa duk kuwa da kasancewar umarninsu yake bi, sannan cigaba mai yawa ya riski kano a mulkinsa.
   Dafatan Allah ya rahamsheshi Amin

Thursday, 20 September 2018

YADDA AKE BIKIN SALLAH A ƘASAR HAUSA

YADDA AKE SHAGULGULAN SALLAH A ƘASAR HAUSA

Hausawa nacewa 'Sallah biki, ɗaya Rana'. Ma'ana, Sallah wani lokaci ne na biki duk da kasancewar Rana ɗaya akeyin Sallah ɗin.
Sallah ibada ce da addinin musulunci ya sunnata, wadda aduk shekara akeyi sau biyu, babba da ƙarama, to amma anan ƙasar Hausa ba ibadar ƙaɗai akeyi ba, ana haɗawa ma harda wasu lamurori na biki. Akwai abubuwa kala-kala da akeyinsu a lokacin wannan biki, wasunsu ma har mutane na ɗaukarsu a matsayin abubuwa na addini, alhali kuwa na al'ada ne. Wanda kuma hakan ke nuni da cewa irin shagalin bikin dake tattare da ranar Sallah tun da jimawa yske anan ƙasar Hausa.
Daga cikin abubuwan da akeyi don bikin sallah akwai:
1. Ɗinkin sabbin kayan Sallah
 Tun kafin ranar sallah zakaga mutane nayin tanajin sabbin kaya dasu da iyalansu wanda zasu sanya domin murnar zagayowar wannan lokacin biki da ibada mai albarka.
2. Tanajin Kayam miya
Sallah biki ce, a biki kuwa an sani anaci ana sha. Don haka tun kafin isowarta zakaga mutane na tanajin kayan abinci da nasha wanda za'ayi amfani dasu a lokacin wannan biki mai albarka.
3. Tanajin Rago a sallar layya
A lokacin gabatowar babbar sallah, kasuwanni na cika da dabbobi misalin rakuma, shanu da kuma raguna. Hakan nada nasaba da abinda yazo a koyarwar addinin islama na yanka rago ko dabba mai lafiya don yin hadaya da ake kira layya a lokacin wannan biki.
4. Zuwa idi ranar sallah
Idan ranar sallah tazo, maza da mata, yara da manya na sanya sabbin kaya, suci ado da komai sabbi gwargwadon sukunin da mutum yake dashi sannan a tafi bayan gari, zuwa wani fili da aka ware wanda ake kira masallacin idi. Anan ne ake sallatar sallah raka'o'i biyu mai ɗauke da kabbarori, watau faɗin 'Allahu Akbar Allahu Akbar' aƙalla guda goma sha biyu baki ɗaya. Idan an idar, sai kaga mutane sun cika da murna suna gaisawa da juna, daga nan sai liman yayi nasiha garesu sannan su dawo gida.
5. Abinci ranar sallah
Akwai abinci da ake girkawa a ranar babbar sallah, koda yake wasu basa yin girkin sai kashe gari.
Wannan abinci shine ake rarrabawa gida-gida na maƙwabta da ƴanuwa.
A lokacin da ake da sukuni a gari, a kusan kowanne gida anayin wannan girkin, suna kuma rarrabawa izuwa makwabta. Tayadda zakaga an tara abinci kala kala misalin funkasau, tuwo, waina, shinkafa da sauransu a mazubai.
6. Yanka rago
Ana dawowa daga sallar idin babbar sallah ake yanka ragon layya ko kuma duk dabbar da aka tanadar domin yin wannan hadaya da ita. Liman ne ke fara yanka nashi a masallacin idi. Daga nan kuma sai a shiga gyaran dabbar. Zuwa kashe garin sallah sai a shiga suya.
7. Ziyara Gidan ƴanuwa da abokan arzika
Ana ziyara zuwa gidajen ƴanuwa da abokan arziƙa a lokacin bikin sallah. Anan ne kuma ake bada goron sallah, koda yake yanzu an sauya abin, kusan kuɗi ake bayarwa yayin wannan ziyara.
Wanda yafi wani ƙarfi shine ke bayar da wannan kyauta. Don haka a wani lokacin, wanda yaje ziyara ke bayarwa, yayin da a wani juyin wanda aka zowa ne ke bayarwa.
8. Zuwa kallon Hawan sallah
Mazauna manyan birane dake nan ƙasar hausa suna zuwa gidan sarki domin kallon hawan sallah.
A kano, sarki nayin hawa bayan saukowa daga masallacin idi da ake kira 'Hawan daushe'. Daga baya kuma sai hawa masu suna hawan nasarawa, hawan ɗorayi, hawan fanisau su biyo baya.
9. Zuwa wuraren shagulgula
misalin gidan zoo
Yara da manya kanje wuraren da aka kawwame don yin shagalin sallah, inda akasari makaɗa da mawaka da masu barkwanci ke taruwa don nishaɗantar da al'umma.
  Misalin irin wannan wuri a kano shine gidan namun daji da akafi kira da gidan zoo. Inda yara da manya ke taruwa don kallon namun daji, wasu kuma ke zagayawa wurin kallon makaɗan kalangu da makaɗan zamani.

Sunday, 16 September 2018

TARIHIN ASALIN ZAMFARAWA, BIRNIN DUTSI DA LABARIN ƳAR GOJE

TARIHIN ASALIN ZAMFARAWA: LABARIN BIRNIN DUTSI DA GIMBIYA ƳARGOJE



Birnin Dutsi wanda a halin yanzu yake ƙarƙashin Masarautar Zurmi dake Jahar Zamfara,  nan ne akace Zamfarawa suka Fara yada zango, a lokacin da suka riski ƙasar Hausa daga wurin zaman su na asali dake Gabas ta tsakiya.
 Jagoran su, da ake kira Dakka ne ya fara Sarauta a wannan Gari na Dutci/Dutsi a wajajen Shekarar 1300 AD.
 Ance Waɗan nan Mutanen (Zamfarawan Farko ) masu tsayi ne da girman jiki  sosai , kusan wannan ne dalilin da ke sanyawa ana alaƙan ta su da Jinsin Samudawa.
Haka kuma Kaburburan su da ke Dutci /Dutsi a halin yanzu ma wani babban misali ne na irin girman Jikin nasu.
Bayan Mutuwar Sarki Dakka Wanda shine Mahaifin Sarauniya Argoje/Yargoje, an yi Sarakuna biyu kafin ta samu damar ɗarewa kan Karagar Mulki.
 Ance Ƴargoje tayi Mulki a tsakiyar ƙarni na 13 miladiyya.
 Kuma ta Shahara a lokacin ta , domin har a dajin Kuyambana da ke ƙasar Ɗansadau ta Jahar Zamfara ta yanzu takan Zauna da Majalisar ta , tana yanke hukunci akan lamurran da suka shafi al'ummar ta.
A Yanzu haka akwai wata fitilar ta da ke ajiye a ginin hukumar Adana Kayan Tarihi da al'adun Gargajiya na Jahar Zamfara wanda ake dangantawa da ita.
 Bayan Rasuwar ta a Dutci /Dutsi sai aka naɗa ƙanenta mai suna Bakurukuru a matsayin Sabon Sarki.
Sarki Bakurukuru ɗan Dakka ne ya ƙirƙiri Sabuwar Hedikwatar Zamfarawa,  Mai Suna Birnin Zamfara daga ƙarshe-ƙarshen ƙarni na 13 zuwa farko-farkon ƙarni na 14 , shune silar da zamfarawan suka tashi daga Dutci/Dutsi zuwa can Birnin Zamfaran, inda sunan Gonar Alkalin Zamfarawan ya amshe sunan Birnin na Zamfara.
A Wannan Wuri ne suka yi Mulki har lokacin da Gobirawa suka ƙwache Birnin daga hannun su a cikin ƙarni na 17.

Sunday, 9 September 2018

HIKAYA MAFI TSAYI A DUNIYA

HIKAYA MAFI TSAYI A DUNIYA.

DAGA SADIQ TUKUR GWARZO

A wani zamani mai tsawo daya shuɗe, a daular larabawa, anyi wani hamshakin sarki mai ilimi da hikima.
  Wannan sarki yana da yawan neman ilimi, gami da yawan sauraron hikayoyi tun yana karami. Don haka ya zamana ya kiyaye mafi yawan hikayoyin da alummar zamaninsa ke labartawa mutane, har takai ga cewa da-zarar mai bada labari ya soma labarta masa wata hikaya, kafin yakai karshenta, wannan sarki zaice dakata, ai nasan wannan hikaya, ba itace karshen ta kaza da kaza ke faruwa ba?
  Da Sarkin yaga kamar ya kure masu bada hikayoyi na fadarsa, sai yasa akayi shela cewar yana so azo masa da hikaya mafi tsawo a duniya wadda zata bashi dariya, shikuma yasha alwashin zai bada gagarumar kyauta ga duk wanda yaci nasarar yin haka.
   Ai kuwa mai shela yabi kwararo-kwararo yana sanarwa, mutane kuma suka rinka ɗungomowa ga sarki, suna masu bada labarin hikayoyin da sukaji daga iyaye da kakanni, amma duk babu wanda yazo da wata hikaya wadda sarkin bai santaba, balle har yaji wani sabon abin dariya acikinta.
  Ana haka sai ga wani yaro karami ya karaso, yanaso akaishi gaban sarki domin yazo da dogon labarin dazai baiwa sarki, yana da tabbacin zai kayatar da sarki.
  Har Mutane sun soma hantararsa saboda ganin yaro neshi alhali ga manya sun gaza, amma dai sarki yace a iso dashi gabansa.
  Da yaro yai gaisuwa gaban sarki, sai ya fara bada labarinsa kamar haka:-
   Akwai wani mutum mai suna Mugambo, acici ne na hakika. Bai taɓa koshi ba a tarihin rayuwarsa. Duk tulin abinda ka bashi sai ya cinye, kuma bazai ce maka ya koshi ba. Har takai yakanyi shelar cewa wanene zai iya kosar dashi koda sau ɗaya ne a rayuwarsa?
 To Rannan dai sai sarkin garin mai Suna Sarfin, yace zaiyi maganin wannan acici, don haka a kawo shi gabansa zai ciyar dashi.
  Sarki yasa aka yi abinci daro-daro kala-kala sama da daro ɗari, aka kawo abinsha tulu-tulu, sannan aka zaunar da Mugambo, akace ga abinci, kayi taci har saika koshi
   Mugambo ya russuna gaban sarki cikin girmamawa, sannan yace Ranka ya daɗe, waɗannan duk nawa ne? Cikin farin ciki. Daga nan ya zauna dirshan kamar mai ɗaukar karatu, sannan ya soma cin abinci.
  Mugambo yayi taci, yayi taci, yayi taci, yayi taci, yayi taci.... Yaro mai bada hikaya yayi ta maimaita kalmomin yayi taci.. Yayi taci.. Yayi taci.. Tun daga safe har yamma.
  Sarki ya daka masa tsawa, yace kai yaro, wannan wanne irin labari ne haka sai maimaita abu ɗaya kakeyi?
  Yaro yace Ranka ya daɗe, daro sama da guda ɗari fa aka tara masa a gabansa, ga kuma abinsha duk a gabansa, a yanzu kuwa a labarin ko daro ɗaya bai kammala ci ba.
   Yaro yaci gaba da cewa da yaci yaci yaci, sai kuma yasha abinsha, yasha abinsha, ya kara shan abinsha, sannan ya cigaba da cin abinci.
  Yayi taci.. Yayi taci... Yayi taci.... Yayi taci....
  Sarki ya tuntsure da dariya, yace lallai wannan labari ne mafi tsawo dana taɓa ji.. Nasan zanuɓiya sgafe kwanaki ɗari an maimaita waɗannan kalmomi.. Kai fadawa ku kawowa wannan yaro kyaututtukansa ya tafi ya bamu wuri.
  Aka baiwa yaro tulin kyaututtuka, aka ɗora shi akan rakumi tare da kyaututtukan , sannan aka haɗa shi da bawa guda ya rakashi gida.
  Yaro ya zauna bisa rakuminsa cikin farin ciki, sannan ya cigaba da cewa Sai Mugambo yayi taci.. Yayi taci.. Yayi taci...
  Alummar wajen kuwa duk sai suka kwashe da sowa...