Sunday, 23 September 2018

Tarihin Sarkin Kano Abbas

Sarkin Kano Muhammad Abbas

Sadiq Tukur Gwarzo
   Shine sarkin Kano na hamsin da ɗaya, kuma na takwas a jerin Sarakunan fulani da suka mulki Kano. Shi ɗa ne ga Marigayi Sarkin Kano Abdullahi Maje Karofi, watau ƙani yake ga Galadima Yusufu da kuma Sarki Alu Babba.
   Babu takamaimen lokacin da aka haifeshi kasancewar Hausawa basu cika kiyaye ranakun haihuwa ba a wancan lokacin, amma dai an samu cewar ya zama sarkin Kano a watan mayu na shekarar 1903 miladiyya har kuma zuwa shekarar 1919 bayan rasuwarsa aka binneshi a Nassarawa (daga nan ya samo sunan Maje Nassarawa) sai ɗansa Shehu Usmanu ya gajeshi.  Gwamna Lugard ne ya naɗa shi sarauta sa'ar da yaci kano da yaƙi.
  Ga yadda hawa mulkinsa ya kasance:
Kamar yadda aka sani, Mabiya Galadima Yusufu sunyi bore ga Sarki Tukur bayan rasuwar Sarki Muhammadu Bello, wanda ya kai ga yaƙin Basasar Kano. Daga bisani aka hallaka Sarki Tukur, Alu ƙani ga Galadima Yusufu wanda ya rasu a Garko tun kafin soma yaƙin, ya zamo Sarkin Kano. A wannan lokacin sai ya naɗa ƙaninsa Abbas muƙamin Wambai.
   Ana haka sai turawa suka zo kano, sarki Alu ya shirya tafiya Sokoto tare da tawagarsa tun kafin isowarsu, ciki kuwa harda wambai Abbas, inda ya danƙa amanar gari a hannun Sarkin Shanu.
   Bayan Sarki Alu ya juyo daga Sokoto, sai ya sauka a ƙasar zamfara, anan ne kuma mai ɗakinsa tazo da dare a sukwane ta sanar masa cewar turawa sun ƙwace iko da kano, wanda a cikin daren yayi hawa a ɓoye ya bar jama'arsa.
   Koda gari ya waye sai ragowar mutane suka shiga neman Sarki Alu, amma rasa shi da sukayi yasa suka yanke shawarar cigaba da tafiya zuwa kano. Inda a yankin kwatarshi wannan runduna ta haɗu da turawa masu neman Sarki Alu, waɗanda bayan sun karɓe ikon Kano suka nemeshi suka rasa, sai suka bar wasu turawan riƙon kano, suka biyo sahun Sarki Alu zuwa Sokoto.
    Waziri Amadu ne ke jagorancin wannan tawaga, anyi wannan haɗuwa ne kuma a wani daji da ake kira 'Dajin Rubin' (Tana kuma iya yiwuwa turawa ne suka sanyawa dajin wannan suna saboda mutuwar ɗanuwansu Reuben a dajin)
  Da gamuwar su sai faɗa ya kaure a tsakani. Aka soma fafatawa, dakarun waziri Amadu suka afkawa turawa da sara da suka, yayin da suma turawa suka mayarwa da dakarun martani da harbi.
   Sai dai cikin abinda baifi awa ɗaya ba, turawa suka karya lagon wannan tawaga suka kuma watsa ta. Ya zamana an kashe wasu, wasu kuma suna zube a kakkarye harsashi yayi misu lahani, yayin da saura suka shige daji da gudu suna masu neman tsira da rayukansu..
  Anan ne Wambai Abbas ya jagoranci wata tawaga suka gudu daga wannan yaƙin tare da nufowa birnin Kano.
  Sai dai tun kafin su iso, tuni har labari yazo ga turawan da suka rage a kano, waɗanda aka barsu a gari da zimmar su tsare garin tunda sun karɓe iko dashi.
   Ai kuwa tun kafin dakarun su iso, sai turawan suka haɗa tawaga suka nufi wajen ganuwa, suka jejjeru suna sauraren su.
   Bayan misalin awa guda suna jira, sai ga dakarun sun karaso.
   Turawan nan suka tsaida waɗannan dakaru, sannan suka karɓe dukkanin makaman dake jikkunan su.
  Daga nan aka basu damar shiga garin kano bisa sharaɗin kowa gidansa kurum zai nufa, banda kuma yinkurin tada tarzoma.
  Anyi haka a lokacin tsakiyar sanyi na wannan shekarar.
   Daga nan kuma, sai Turawa bayan sun koma gida suka shiga neman shawarwari daga gurin Larabawa mazauna kano akan wanda ya kamata a naɗa sarki a kano musamman wanda ya fito daga zuriyar Abdullahi Maje Karofi.
  Sai larabawan nan sukace ai kuwa Wambai Abbas ne yafi dacewa, tunda babban su waziri Amadu ya rasu.
  Sai turawa suka amsa da cewar haka nan ne.
 Sai dai fa duk da haka, turawa sun shiga tambayar Manyan kano na wancan lokacin dake zaune a birni, cewar wa ya dace ayiwa sarki, sai suma ɗin kuwa suka ce abaiwa Wambai Abbas sarauta.
  To kunji yadda sarki Abbas ya zama sarki na farko a kano a zamanin turawa. Shi suka ɗorawa nauyin kwantarwa da mutanen Kano hankali ma zamanin, sannan ya rinƙa kiran duj waɗanda sukayi hijira saboda zuwan turawa Kano su komo gida.
   A zamanin mulkinsa jirgin ƙasa ya soma zuwa kano, har wata rana turawa suka buƙaci yahau domin a ɗana shi.
   Ai kuwa Sarki Abbas yahau jirgi, mutanen Kano duk suka firgice dube da jin kuwwarsa, wadda basu taɓa jin irin taba.
  Labari ya nuna cewar har mutan kano sun fara zunɗen cewa turara ƙarya sukeyi, wayau kawai sukayi domin su tafi da Sarki Abbas su kashe, amma daga bisani sai Allah ya dawo dashi gida lafiya.
   Har ila yau, a zamanin sa ne aka tara ɗaukacin sarakunan Arewa a kano domin tarben wakilin Sarkin Ingila, shine ma har Sarkin Zazzau na zamanin Shehu ya rera shahararrar waƙar nan tasa mai taken 'Zuwan mu Birnin Kano'.
  A zamaninsa har ila yau aka gins makarantar Elemantare ta farko a kano, aka soma shirya gidan tarihi na Kano tare da wasu ayyuka masu yawa.
  Haƙiƙa Sarki Abbas yana da karamci da son jama'a, kuma yayi matuƙar ƙoƙarinsa wajen kare haƙƙin Kanawa daga turawa masu mulkin mallaka a zamaninsa duk kuwa da kasancewar umarninsu yake bi, sannan cigaba mai yawa ya riski kano a mulkinsa.
   Dafatan Allah ya rahamsheshi Amin

No comments:

Post a Comment