ASALIN KANO
(Fassarar Tarihin asalin Kano kamar yadda ya fito daga tsohon kundi mai suna 'TARIYK ARBAB BALADIL LAZIY MUSAMMA KANO' watau 'KANO CHRONICLE' da turanci, wanda aka gutsura shi a littafin 'HAUSAWA DA MAKWABTAN SU' littafi na biyu' )
SADIQ TUKUR GWARZO
Littafin ya soma kamar haka:-
Wannan tarihi ne na ma'abotan wannan gari wanda ake kira Kano. Shugaban su shi ne Barbushe, shi kuwa daga ƙabilar Dala yake. Shi Dala mutum ne baƙi, kakkaura, ƙaƙƙarfa, mafarauci ƙwarai. Ya kasance ya kan kashe giwa da sandar sa, ya saɓo ta a kansa, yayi tafiya da ita kamar mil tara.
Ya zo garin nan, ba a san asalin sa ba. Da zuwan sa sai ya gina gidansa a saman dutsen Dala, ya zauna akan sa, shi kaɗai tare da matan sa da ƴaƴansa bakwai, huɗu maza uku mata.
Sunan babban ɗansa Gargaji, shine kakan Buzami.
Buzami kuwa shine uban Barbushe. Shikuwa Barbushe, shine ya gaji dukkan halayen Dala tun daga sanin tsafi har zuwa ƙarfi da sihirinsa da rinjaye ga ƴanuwansa, domin haka sai ya zamo shugaba a zamanin sa.
Ga sunayen fadawan Barbushe;
-Gunzago: gidan sa yana a ƙarƙashin Gwauron dutse daga gabas.
- Gagiwa uban Rubu wanda yake kama giwa da igiya saboda tsabar ƙarfin sa.
-Gubanasu
-Ibrahimu
-Bardoje
-Nisau (wanda garin Panisau ya samu daga sunan sa)
- Kamfatau
- Duje
-Janberi
-Gamakora
-Safataro
-Hangugu
-Gardangi.
- Ɗan buru: wanda gidan sa yake a jigirya.
-Jan Damisa: wanda gidan sa yake a magwan. Sunan sa Ruma, kuma shine kakan Rumawa. Tun daga Guga har zuwa Salanta ana danganta su da shi, ana ce musu rumawa, su jama'a ne masu yawa.
- Hamɓarau: gidan sa yana Tanagar.
-Gunbarjado: gidan sa yana Panisau, kuma shi ɗa ne ga Nisau.
A wancan zamani na Barbushe, mutane kan taso tun daga Tuda zuwa Ɗan-baƙoshi, haka kuma tun daga Duji har zuwa Ɗankwai, dukkan su suna taruwa a wurin Barbushe a daren salla biyu, domin shine babban su cikin tsafi.
Sunan inda gunkin su yake ajiye 'Kakuwa', sunan gunkin kuwa 'Tsumburbura', domin itaciya ce da ake ambatonta 'Shamus', sunan mutumin da yake zaune a ƙarƙashin ta dare da rana 'Mai Tsumbura'.
An kewaye itaciyar da gini ne, babu mai shiga cikin ginin sai Barbushe, duk kuwa wanda ya shiga sai ya mutu nan take.
Barbushe kuwa baya saukowa daga saman dutsen Dala sai idan ranakun idi biyu sun gabato. A lokacin ne mutane ke zuwar masa da ga gabas da yamma, kudu da arewa, waɗansu da baƙar kaza, waɗansu da baƙin bunsuru.
Idan sun gama taruwa a ƙarƙashin dutsen Dala a ranar jajibere kenan bayan la'asar, sai Barbushe ya fito daga gidansa da dare tare da makaɗansa. Ya na mai kururuwa da ƙarfi yana cewa "Babban jimina aka sa mun gama kara-gaga laya Tsumburbura"
Mutane kuma sai su amsa masa da cewa "Ga Tsumburbura, Kanawa, ga wajen Dala".
Daga nan sai su ɗunguma tare dashi zuwa saman tsauni wurin gunki. Da isar su gurin gunkin sai kowa ya yanka abin da yazo da shi.
Sa'an nan sai Barbushe ya shiga cikin ginin shi kaɗai, yana mai cewa "Ni magajin Dala da kun ƙi da kun so ku bini ba ra'ayi ba"
Su kuma mabiyan suna kewaye ginin da gunki Tsumburbura take tsirara suna masu cewa " Mai gida bisa kan dutse, Ubangijin Mama, bi mun bi ka ba ra'ayi", a haka zasu wakana har huduwor alfijir sa'annan su tsaya suci abinci.
Daga nan sai Barbushe ya fito ya basu labarin dukkan abinda zai faru acikin shekarar da zasu shiga, har ma da baƙon da zai shigo ƙasar su na alheri ko na sharri.
Shine ma ya basu labarin gushewar mulkin su, da sarewar itaciyar shamus da suke yiwa bauta har ma da ƙonewar ta, da kuma gina wani masallaci a jikin dutsen Dala.
Kuma yace musu "Wani mutum zai zo wannan gari tare da rundunarsa, ya mallakemu".
Sai suka ce masa "Don me ka faɗi haka? wannan magana ce fa mummuna".
Sai yayi shiru, sannan yace "da sannu zaku ganshi da alfarmar Tsumburbura! idan bai zo a zamanin ku ba, zai zo a zamanin ƴaƴanku, ya mallaki dukkan wanda ya samu a cikin wannan ƙasa dukkan ta, ya sa a manta daku duk da jama'ar ku, zai bayyana da ƙabilar sa zamani mai tsawo".
Jama'ar Barbushe suka yi baƙin ciki ƙwarrai, suka gaskata abinda ya faɗa domin sun san baya musu ƙarya. Har ma suka ce "yaya za muyi mu kawad da wannan lamari?"
Sai yace dasu " Babu yadda za ku yi sai haƙuri!".
A haka suka wanzu cikin nadama bisa gushewar da mulkin su zaiyi mai tsawo har sa'ar da Bagauda yazo kano tare da runduna tasa a zamanin ƴaƴan waɗancan mutane na lokacin Barbushe, (amma wasu sunce zamanin jikoki ne), bai samu kowa ba daga makusantan Barbushe sai Janberi, da Hamɓarau, da Gardangi, da Jandamisa, da Kamfatau.
Da waɗannan mutanen suka ga lamarin Bagauda sai suka ce "wannan mutumin shine wanda Barbushe ya bamu labari".
Jamberi yace " Na rantse da Tsumburbura idan aka bar su a cikin wannan ƙasa, da sannu zasu mallake mu har mu zama kamar ba kome ba".
Mutane suka ƙi jin maganar sa, suka bar su suka zauna, suka ce "A ina Bagauda zai samu ƙarfin da zai rinjaye mu?"
Bagauda ya zauna da rundunar sa a Gazarzawa, suka gina gidaje a cikin ta, suka zauna watanni bakwai, sannan suka tafi Sheme.
A wancan zamani, daga Jakara zuwa Damargu, ana giran sa da suna Gazarzawa.
Daga Jakara zuwa Santolo, ana kiran sa da suna Zadawa.
Daga Santolo zuwa Barku, sunan sa Fankui.
Daga Bampai zuwa Wasai ana kiran sa da Raura.
Daga Watari zuwa dutsin karya sunan sa Dundunzuru.
Daga Santolo zuwa shike sunan sa Sheriye.
Daga Damargu zuwa Kazaure sunan sa Sheme.
Daga Barku zuwa Kara sunan sa Gauɗe.
Daga Kara zuwa Amnago shine Gaji.
Sai kuma daga Mashi zuwa Ringim da ake kira Tokawa.
Ma'abotan wannan ƙasa wanda Bagauda ya same su a cikinta suna mulkin garinsu, ba su bin kowa sai Tsumburbura da duhuwar sa Jakara.
Ana ambaton ta (jakara) da suna Kurmin baƙin ruwa, domin shi ruwa ne baƙi, duhuwa ta kewaye shi, ana kiyaye dukkan musiba da ita da gunkin su. Ta faro ne tun daga Gurgumasa har zuwa Dausara.
Ƙiraranta da zartakenta basa yin motsi har sai idan musiba ta gabato garin kano, sai aji tayi kururuwa sau uku, hayaƙi ya rinƙa fitowa daga cikin Tsumburbura, wanda ke cikin tsakiyar ruwa.
Daga nan sai su nemi baƙin kare su yanka a ƙarƙashin Tsumburbura, kuma su yanka baƙin bunsuru a cikin duhuwar.
Idan har hayaƙin da kururuwar suka ƙaru to tabbas sai wannan musibar ta sadu dasu, idan kuwa basu daɗu ba to musibar ta kau kenan. Sunan wannan duhuwar 'Madama', kuma sunan Tsumburbura Randaya.
Ga sunayen waɗanda suka soma riƙe sarautar kano tun a zamanin farko:-
- Mazauda, shine babbansu, shine kuma kakan sarkin Makafi.
- Giji-giji shine sarkin Maƙera.
- Bugazau sarautar sa dafa giya.
- Hamburki sarkin magani kenan mai warkar da dukkan cututtuka.
- Ɗan ɓuntiya shine mai yawan tafiya cikin garuruwa da daddare, shine kakan kurmawa (sarautar kama masu laifi kenan)
- Doron-maje shine sarkin Samari.
- Jandodo shine sarkin makaɗan gunduwa da kuru.
-Magaji shine kakan Maguzawa, shine mai fitar da ƙarfe daga ƙasa ya narka shi.
- Asanne shine kakan mawaƙa, shine sarkin Rawa.
- Bakwanyaƙi shine sarkin Maharba.
- Awar shine kakan Awarawa, shine mai yin gishirin Awar, kuma sarkin Ruwan dukkan ƙasar.
Dukkan waɗannan su goma sha ɗaya, kowannen su yana da ƙabila tasa daban da jama'a mabiyan sa masu yawa, kuma dukkan su sune asalin KANO..
No comments:
Post a Comment