Saturday, 23 October 2021

MAGANIN BIRI KAREN MAGUZAWA: LABARIN WANI MUTUM DA MATAR SA

 MAGANIN BIRI KAREN MAGUZAWA

Wani mutum ne ya ƙwazzabi matarsa, a kullum sai ya Sami hanyar da yabi ya Ci mata mutunci, yana zagin iyayenta anini-anini. Daga yace 'duk inda aka fito na tabbata kin haɗa jini da makaɗa', sai ya ce 'wane ɗan gidan ku yayi mini Kama da wani kuturu da na sani.'.

 Haka dai, yana mata Matuƙar cin mutunci.  Idan dare ya yi ta ce ya raka ta bandaki sai ya ce 'ai da ma na san ke jikar Yambashirwa ce (wato masu zawayi a kasuwa)'.


Tana nan cikin wannan hali kullum idan ya yi mata sai dai ta haɗe kai da guiwawu ta yi ta kuka, in ta kare ta share hawayenta amma ba ta taɓa gwada rama zaginsa ba. 

Rannan sai ga wani kawunta ya zo ya sanarmata cewa anyi  haihuwa a gidansu. Bayan sun gaisa ya sha ruwa, sai ya ce mata, "Amma naga duk kin rame kamar da ke ake miya".

 Yarinya da ta samu kafa Sai ta kwashe

duk labarin ƙuƙumin da take ciki ta labarta wa kawunta. Da ya ji haka sai yace, "Ya yi da gwannai. Ai duk wanda ya ci tuwo da mu miya ya sha. Idan rashin kunya yake taƙama muna marhabin da shi."

Sai ya shawarta mata cewa ta sami lokaci su tafi wurin bikin nan tare da shi.

Ta kuma gaya masa cewa a gidan kawun nata za su sauka.

Hakan ta haddasu.

 Ranar biki sai ga yarinya tare da mijinta a gidan kawun nan nata. Aka kawo wa mijin fura da zuma kamar ta harbe shi don zaki, ya sha.

Da ƙare sha sai ya ce, "Allah sarkin baiwa, watau ko gidan ƙaho kamar kawun nan naki ana shan fura da zuma. Ko kuwa an yi ne don in zata ya daina ɗanbashirwanci?"

  Ita dai ta kanne, bata ce masa komai ba.

Can an jima aka shiga kawo masa nama soyayye mai maiƙo.

 Shi kuwa sai ɗorawa yake yana cewa, "Oh, ashe ragon gidan mayu ma yana da mai. Mu dai Allah ya mai da mu gida lafiya kada a yi balangu da kurwar mutum." 

Haka dai aka yi ta kawo masa gara iri-iri shi kuma yana ci yana yankan ƙauna kamar

yadda ya saba.

Da dare ya yi lokacin bacci ya zo sai kawun yarinyar ya kira shi ya ce masa,

"Saboda yawan jama'a mun rasa ɗakin da za mu ba ka kai da matarka. Sai dai

za mu yi maka shimfiɗa a can dakin yara tun da yau ne kawai gobe za ku tafi gida".

Bako ya ce, "Ai ba kome."

Aka je aka yi masa shimfida, sannan aka kira yaran da suke dakin aka ce musu in dare ya yi duk abin da suka ji bakon nan ya yi kada su ce kome.

 Bayan kowa ya kwanta sai wani ƙanin yarinyar nan ya tayar da mutumin nan kamar

yadda aka shirya masa, ya ce, "Na manta in gaya maka cewa idan dare ya tsala

kada ka kuskura ka fita waje ko da sunan tofaar da yau. Dalili kuwa shi ne saboda a ƙauyen nan namu akwai wasu fatalwoyi da suka kai mana ƙul. Duk wadanda suka gwada fitar dare daga wanda za a tarar an kwakule wa idanu, sai wanda za a tarar ba hannaye da ƙafafuwa duk an cire, mu dai Allah ya tsare kawai".

Bako ya Ce, "Amin. Ai ka ga gara da na sani yanzu in na kwanta abina sai da asuba ko?"


Abisa wannan shiri sai kawun matar nan ya je ya dauko damin karan dawa biyu da ya shirya wata dabara da su. Wannan sai ya daura masa farin zane ɗayan kuwa ya daura masa baƙin zane, ya yi musu wasu yan dabaru suka ƙara tsawo.

 Idan ka gan su sai ka zata wasu aljanu ne a tsaye. Ya kawo ya jingine a jikin bango daidai kofar dakin da bakon nån yake, ya koma ya kwanta abinsa.

CIKin toye-toyen nan da aka yi wa bako da rana ashe an barbaɗa wani maganin sa gudawa an hada da yaji. Can mutumin nan na Cikin barci sai magani ya fara aiki. Cikinsa ya murd'a ƙwarrai. 

Mutumi ya tashi zaune yana wani nannauyan numfashi. Can kuma sai ciki ya lafa. Har barci ya soma kama shi sai kuwa cikinsa ya kuma murɗawa.

 Ya zabura.

 A wannan karon fa ciki ya ce bai san rangwame ba.


Tun yana zaune nar ya mike tsaye gumi na karyo masa sai runtse ido yake kamar wanda ake caka wa allura.

Da azaba ta yi masa yawa sai ya yi tunanin fita waje ƙila ma fatalwa ba ta zo ba.

 Yana bud'e kofa sai ya yi kaciɓis da abubuwan nan da kawun yarinya ya

kafa. Nan da nan ya jawo kyauren daki kub ya mayar ya rufe yana cewa, "Wai!!! yau na yi arziki da an kwakule idanuna." 

Ciki ya ƙara murɗa wa mutumi tun yana tsaye har ya kai tsugune. 

Da ya ga kamar idan bai yi zawon nan ba zai

mutu sai ya ce wa yaran nan, "Kuna ji?",

 ya ga ba su motsa ba. Ya sake cewa,

"Kuna ji?!!"

 ya ga ba su motsa ba. Sai kawai ya kwale ya tsuguna cikin dakin nan ya tsulala zawonsa har kashi uku, ya koma ya kwanta abinsa yana cewa "Kai ai gara haka."


Washegari sai babban cikin yaran ya tashi ya ce, "Hm'mm'" ya rike hanci,  "ga tsinannun yara. Yanzu ku rasa inda za ku baje mana zawayi sai cikin ɗaki? Ku tashi marasa kunya"

 Ya doddoke su suka yi waje. 

Da mai gida ya ji ana kaiya kaiya sai ya ce wa babban cikin yaran, "Menene ne"?

Sai yaron ya ce, ""Kashi suka yi mana a daki, wajen ba ya shakuwa."

Maigida ya zo ya duba ya ce, ""Kai wadannan akwai 'yan banza, yanzu ba ku tashi ba ni kunya ba sai da surukai suka zo mana. To duk wanda ya yi zawon nan ya kuka da kansa, don sai na barbaɗa magani cikinsa ya kumbura ya fashe."


Ya tafi yana zage-zage mutanen gida duk suka fito. Ya dauko wata jaka ya fitar da wani ƙunshin magani daga cikinta. Ya ce, "Yanzu ina barbada wannan magani cikin ko wane ne ya kumbura tim har ya fashe. Me ake da dan da zai kai ka ga kunya?"

Yara wannan ya ce, "Ni dai ba ni ba ne". Wancan ya ce, "Ni dai ban farka ba."


Maigida ya ce, "Ai ko wane ne sai uwashi ta yi kuka." 

Ya damƙo magani zai barbada sai baƙon nan ya rike hannunsa ya ce, "Tsaya kawu kada mu yi ɓarna, in dai don ni ne wallahi na yafe. Ka bar su matsuwa ce ta sa su yin haka."

Mai gida ya ce, "Ai ba don kai ba, idan na kyale gobe ma haka za ta faru. Bari ka gani ko wane kafiri ne yau uwarsa ta rasa shi." Yayi wuf zai sa magani sai bako ya sake rike hannunsa ya ce, "Tsaya. Gaskiya 'yar Allah da wannan d'an ƙaramin na fari ni na yi shi, amma han san wanda ya yi waɗancan biyun ba,"

Mai gida ya ce, "To in kai ka yi shi ai mun san lalura ce. Saboda haka bari a zuba kan wanda ba kai ka yi ba." 

Mai gida ya je zai zuba magani akan kashi, sai baƙo ya riƙe shi, ya ce,

"Dakata, kai wannan ma ina tsammani nine na yi shi, amma fa na manta ko ni ne ko ba ni ne ba."


Mai gida ya ce, "To tun da ba ka tabbata ba bari a sa kaɗan yadda ko wane ne zai wahala kam amma ba zai mutu ba". 

Mai gida ya yi kamar zai zuba sai bako ya tare shi ya ce, "Tsaya. Don Allah a ɗauka a kan shi ma nine na yi, Amma ka ga wancan, mai yawan can, ba ni na yi shi ba."

Mai gida ya ce, "To, shi ke nan. Tun da ka nuna iya waɗanda ka yi ai ba kome. Shi kuma mai wancan ya mutu sai wani." 

Ya matsa kusa da tarin zawon nan mai yawa ya dumbuzo magani zai sa sai baƙo ya cafke hannunsa ya ce,

"kai tsaya dai in faɗi gaskiya, ko kuwa? Tun da dai nan gidanmu ne ba na wasu ba, ba wani abin ɓoyo. Wannan ma ni na yi shi kada a tsaya ana wahala."

Sai yaran nan duk suka fashe da dariya mai gida ya dubi surukin nan nashi ya ce, "Kai wane irin mutum ne da za ka rasa wurin da za ka, ka yi zawo sai gidan surukanka. Ka gan ka dai ba ka gaji kunya ba. Tun da kuma ka yi mana zawo a nan, ai ba inda ba za ka iya yin zawo ba har a masallaci. To wa ma ya sani ko gado ka yi ba mu sani ba muka dauki 'yarmu muka ba ka. Ni ai tun ranar da ka

zo nan na dubi idanunka na gan su kamar idanun wanda ya sha nonon maita na Ce auren nan a yi dai amma sai ka kai mu ga kunya. Yanzu bari i Kira makwabta su gani su shaide mu, ke kuma.."

Ya ce da matar, "ki tafi gidan AIkali ki yi ƙara.. Kai Sarki ma ya kamata ya ji wannan maganar don a aika har mutanen garinku su zo."

Da mutumin nan ya ji haka sai ya faɗi kwance yana dibar kasa yana afi yana cewa, "Na tuba na bi Allah na bi ka kawu don Allah ka yi min sutura kada mutanen garinmu su ji." Kawun yarinya ya ce nan fa ɗaya, lallai sai jama'a sun sani. 

Da mijin matar nan ya ga ba Sarki sai Allah sai ya je gabanta ya rike ƙafafunta yana cewa ya tuba ita ma ta yi masa gafara kada mutane su sani. 

Can dai da ita da duk sauran matan bikin nan suka shiga ba mai gida hakuri. Kai da ƙyar dai suka ciwo kansa. Ya ce wa mutumin nan, "To tashi ka tafi garinku kada ka ƙara yin zawo, ka ji ko? Yanzu na yafe ka."

Mutumin nan ya tashi ya dawo gida shi kadai. Bayan 'yan kwanaki matarsa ta dawo ta same shi.

Daga ranar nan ko awakin gidan su yarinyar nan ya gani kunyarsu yake ji balle mutane. Ita kuma daga lokacin nan ta sami lafiya.

LABARIN FALKE DA BAƘO: ZAMAN DUNIYA IYAWA NE

 FARKE DA BAƘO


Wani falke ne yake cin kasuwar wani gari mai nisan tafiyar kwana goma sha biyar daga garinsu. Shi wannan falken sana'arsa ita ce sayar da auduga. To duk sa'ar da ya zo wannan garin sai ya sauka a gidan wani mutum sababbensa.

Saboda irin sakayyar da falken nan ke yi wa mai masaukinsa, idan kasuwa ta watse, sai ya zama ba shi ba ma har jakunansa ba su rasa abin taunawa.

Wata rana sai falken nan ya zo, suna hira da mai masaukinsa a zaure, Sai ga wani mutum ya zo daga shi sai lagensa, ya ce yana neman masauki. 

  Falke da mai masaukinsa suka riƙa yiwa mutumin nan kallon uku kwabo. Kai daga Karshe falken nan ya ce shi bai amince a baiwa wannan masauki ba don ba su san Ko wane

iri ne shi ba.

   Da mutumi ya ji haka sai ya ce, "Don kun gan ni CIKin wannan kama shi ya sa za ku wulakanta ni? To ai ni ma mai gidan kaina ne yanzu ma shanu na kai kurmi na sayar. Tafiya ce ta mayar da ni haka".

Sai ya ɗaga hammatarsa ya jawo wani burgami ya ce, "Ni ma ga tawa dukiyar, mai irin wannnan kuwa me zai tsaye tsiwace-tsiwacen dukiyar wani."

Ya zazzage jakarsa suka ga kudi irin wanda ba su taɓa gani ba. Nan da nan hankalin falke ya tashi, sai zare ido yake yana lasar baki. Mai gida kuwa sai ya ce da mutumin nan, "don Allah ka yafe mu. Ka san halin duniyar tamu mutumin yau abin tsoro ne."

Falke kuma sai ya ce "Shi kenan a yi masa masauki tare da ni, ka ga na huta da kwana ni daya".

Da bakon nan ya ga masaukinsa sai ya ce to zai isa kasuwa domin kuwa gobe ranar kasuwa. 

Ya kama hanya ya tafi. Yana isa kasuwa sai ya sami

wani lungu ya cire kudinsa daga cikin burgami ya cuccusa su cikin bantensa ya sayi dakuwa ya cusa cikin burgamin kamar ba a cire kome daga cikinsa ba.

Baƙo ya kama hanya ya koma masauki

Da dare ya yi aka zauna ana hira sai farken nan ya yi shimfida ƙasa da inda jakar mutumin nan take rataye.

Ana cikin hira sai ya yi hamma, ya yi mika da wayo ya mike hannunsa ya taɓo jakar nan ya ji  har yanzu kudin na nan. Da an ɗan jima duk sai ya yi haka.

 Can sai ruwan sama ya ɓarke kamar da bakin kwarya, sai bakon nan ya lunsashe idanunsa ya shiga minsharin ƙarya kamar ya yi bacci.

 Da farken nan ya ji gari ya yi tsit sai ya zabura ya figi burgamin nan taf da dakuwa ya auna da gudu daga shi sai gajeren wando ga shi ana ruwa.

 Da baƙo ya ga haka sai ya tashi sannu ya tafi ya tayar da mai gidan ya ce masa "Ka ji abin da mutumin nan ya yi mini".

Gari na wayewa sai mai gidan ya dauki bakon nan suka tafi suka shaida wa sarkin garin abin da ya faru. Sarki ya sa aka kama jakunan falke da kayan audugarsa aka sayar aka ba bakon nan aka ce ya ci da hakuri Allah ya saka masa.

Bako kuwa sai ya raba kudin nan biyu ya ba mai masukinsa rabi, rabi kuwa ya tara almajirai da nakasassu ya yi ta sadaka.

   Ya bar garin ana ta yi masa addu 'ar Allah ya kiyaye gaba. 









Sunday, 10 October 2021

TARIHIN ALH SAFIYANU MADUGU, HAMSHAƘIN ƊAN KASUWA


 TARIHIN ALH SAFIYANU MADUGU, HAMSHAƘIN ƊAN KASUWA

Shine Alhaji Safiyanu Madugu, ɗan Ali  (wanda akafi sani da suna MADUGU MAIRAWANI) ɗan Abdullahi, ɗan Muhammadu, bafillatani a jinsi, haifaffen birnin kano, ƙwararren ɗan kasuwa, mai kyauta da kyautatawa, mai yawan ƙasƙantar da kai wanda baya son a yabeshi. Shine ya kafa kamfanin 'A.S Madugu & sons Ltd wanda ya shahara a fagen dillacin kayayyakin masarufi, sannan daga baya ya kafa kamfanin 'Dala foods' wanda yake samar da kayayyakin abinci misalin ganyen shayin CITY TEA, KUNUN TSAMIYA, da FURA.

 An haifi Marigayi Alhaji Safiyanu Madugu a garin Kano, a gidan masaƙa wanda yake cikin  unguwar ceɗiyar ƙuda a cikin birnin kano, a shekarar 1938. Sunan mahaifin sa Alhaji Ali Madugu amma yafi shahara da suna 'Madugu Mai Rawani', mahaifiyar sa kuwa sunan ta Hajiya Hadiza Yusuf, ita haifaffiyar unguwar Daurawar koki ce cikin birnin kano.


KARATUN SA

Karatun addini marigayi Alhaji Safiyanu Madugu ya soma runguma tun da ƙuruciyar sa kasancewar ya taso a gidan girma da mutumci, gidan fatauci da riƙo da addini.

Haka kuma ya yi karatun boko, amma ba a makarantar Primary ko Elementary ba, sai dai an samu cewa da girmansa cikin shekarar 1960 da ɗoriya, ya shiga wata makarantar dare mai suna IGBO UNION dake Sabon Gari ta kano , wacce ta zama makarantar 'Mai kwatashi' a halin yanzu. Da daddare suke zuwa shi da abokanansa domin karatun yaki da Jahilci.

ƘURUCIYAR SA

Mahaifinsa Alh Ali Madugu ne ya soma sanya shi cikin harkokin ciniki tun bayan soma ɗagawar sa, domin ya zama ya soma buɗe ido a lamurorin kasuwanci. Alhaji Safiyanu Madugu ya soma kasuwanci tun yana ƙarami, yana mai hawa keke daga kasuwar kurmi zuwa kasuwar sabon gari don saro kayayayakin siyarwa. A haka ya girma har kuma ya bunƙasa a kasuwanci.

Haƙiƙa Allah Ta'ala ya albarkaci Alhaji Safiyanu Madugu da abubuwa guda biyu, na ɗaya shine kyakkyawar mu'amala  a cikin harkar kasuwaci sa na biyu kuwa shine haƙuri.

RASUWAR SA

 Allah ya karɓi ran Alhaji Safiyanu Madugu a ranar litinin, 3 ga watan fabrairu na shekarar 2003 (3/2/2003) a halin jinya a asbitin Mallam Aminu dake birnin Kano.  Ya rasu da misalin ƙarfe 1:00 na rana.

Alhaji Safiyanu Madugu ya rasu ya bar mata huɗu da ‘ya’ya talatin da tara (39), maza sha tara (19) mata ashirin (20).

NB: Wannan tsakure ne daga littafin Tarihin Alh Safiyanu Madugu mai ɗauke da tarihin rayuwar sa da kuma salon kasuwancin sa.

Da fatan Allah ya rahamshe shi amin