Sunday, 10 October 2021

TARIHIN ALH SAFIYANU MADUGU, HAMSHAƘIN ƊAN KASUWA


 TARIHIN ALH SAFIYANU MADUGU, HAMSHAƘIN ƊAN KASUWA

Shine Alhaji Safiyanu Madugu, ɗan Ali  (wanda akafi sani da suna MADUGU MAIRAWANI) ɗan Abdullahi, ɗan Muhammadu, bafillatani a jinsi, haifaffen birnin kano, ƙwararren ɗan kasuwa, mai kyauta da kyautatawa, mai yawan ƙasƙantar da kai wanda baya son a yabeshi. Shine ya kafa kamfanin 'A.S Madugu & sons Ltd wanda ya shahara a fagen dillacin kayayyakin masarufi, sannan daga baya ya kafa kamfanin 'Dala foods' wanda yake samar da kayayyakin abinci misalin ganyen shayin CITY TEA, KUNUN TSAMIYA, da FURA.

 An haifi Marigayi Alhaji Safiyanu Madugu a garin Kano, a gidan masaƙa wanda yake cikin  unguwar ceɗiyar ƙuda a cikin birnin kano, a shekarar 1938. Sunan mahaifin sa Alhaji Ali Madugu amma yafi shahara da suna 'Madugu Mai Rawani', mahaifiyar sa kuwa sunan ta Hajiya Hadiza Yusuf, ita haifaffiyar unguwar Daurawar koki ce cikin birnin kano.


KARATUN SA

Karatun addini marigayi Alhaji Safiyanu Madugu ya soma runguma tun da ƙuruciyar sa kasancewar ya taso a gidan girma da mutumci, gidan fatauci da riƙo da addini.

Haka kuma ya yi karatun boko, amma ba a makarantar Primary ko Elementary ba, sai dai an samu cewa da girmansa cikin shekarar 1960 da ɗoriya, ya shiga wata makarantar dare mai suna IGBO UNION dake Sabon Gari ta kano , wacce ta zama makarantar 'Mai kwatashi' a halin yanzu. Da daddare suke zuwa shi da abokanansa domin karatun yaki da Jahilci.

ƘURUCIYAR SA

Mahaifinsa Alh Ali Madugu ne ya soma sanya shi cikin harkokin ciniki tun bayan soma ɗagawar sa, domin ya zama ya soma buɗe ido a lamurorin kasuwanci. Alhaji Safiyanu Madugu ya soma kasuwanci tun yana ƙarami, yana mai hawa keke daga kasuwar kurmi zuwa kasuwar sabon gari don saro kayayayakin siyarwa. A haka ya girma har kuma ya bunƙasa a kasuwanci.

Haƙiƙa Allah Ta'ala ya albarkaci Alhaji Safiyanu Madugu da abubuwa guda biyu, na ɗaya shine kyakkyawar mu'amala  a cikin harkar kasuwaci sa na biyu kuwa shine haƙuri.

RASUWAR SA

 Allah ya karɓi ran Alhaji Safiyanu Madugu a ranar litinin, 3 ga watan fabrairu na shekarar 2003 (3/2/2003) a halin jinya a asbitin Mallam Aminu dake birnin Kano.  Ya rasu da misalin ƙarfe 1:00 na rana.

Alhaji Safiyanu Madugu ya rasu ya bar mata huɗu da ‘ya’ya talatin da tara (39), maza sha tara (19) mata ashirin (20).

NB: Wannan tsakure ne daga littafin Tarihin Alh Safiyanu Madugu mai ɗauke da tarihin rayuwar sa da kuma salon kasuwancin sa.

Da fatan Allah ya rahamshe shi amin

No comments:

Post a Comment