Saturday, 23 October 2021

LABARIN FALKE DA BAƘO: ZAMAN DUNIYA IYAWA NE

 FARKE DA BAƘO


Wani falke ne yake cin kasuwar wani gari mai nisan tafiyar kwana goma sha biyar daga garinsu. Shi wannan falken sana'arsa ita ce sayar da auduga. To duk sa'ar da ya zo wannan garin sai ya sauka a gidan wani mutum sababbensa.

Saboda irin sakayyar da falken nan ke yi wa mai masaukinsa, idan kasuwa ta watse, sai ya zama ba shi ba ma har jakunansa ba su rasa abin taunawa.

Wata rana sai falken nan ya zo, suna hira da mai masaukinsa a zaure, Sai ga wani mutum ya zo daga shi sai lagensa, ya ce yana neman masauki. 

  Falke da mai masaukinsa suka riƙa yiwa mutumin nan kallon uku kwabo. Kai daga Karshe falken nan ya ce shi bai amince a baiwa wannan masauki ba don ba su san Ko wane

iri ne shi ba.

   Da mutumi ya ji haka sai ya ce, "Don kun gan ni CIKin wannan kama shi ya sa za ku wulakanta ni? To ai ni ma mai gidan kaina ne yanzu ma shanu na kai kurmi na sayar. Tafiya ce ta mayar da ni haka".

Sai ya ɗaga hammatarsa ya jawo wani burgami ya ce, "Ni ma ga tawa dukiyar, mai irin wannnan kuwa me zai tsaye tsiwace-tsiwacen dukiyar wani."

Ya zazzage jakarsa suka ga kudi irin wanda ba su taɓa gani ba. Nan da nan hankalin falke ya tashi, sai zare ido yake yana lasar baki. Mai gida kuwa sai ya ce da mutumin nan, "don Allah ka yafe mu. Ka san halin duniyar tamu mutumin yau abin tsoro ne."

Falke kuma sai ya ce "Shi kenan a yi masa masauki tare da ni, ka ga na huta da kwana ni daya".

Da bakon nan ya ga masaukinsa sai ya ce to zai isa kasuwa domin kuwa gobe ranar kasuwa. 

Ya kama hanya ya tafi. Yana isa kasuwa sai ya sami

wani lungu ya cire kudinsa daga cikin burgami ya cuccusa su cikin bantensa ya sayi dakuwa ya cusa cikin burgamin kamar ba a cire kome daga cikinsa ba.

Baƙo ya kama hanya ya koma masauki

Da dare ya yi aka zauna ana hira sai farken nan ya yi shimfida ƙasa da inda jakar mutumin nan take rataye.

Ana cikin hira sai ya yi hamma, ya yi mika da wayo ya mike hannunsa ya taɓo jakar nan ya ji  har yanzu kudin na nan. Da an ɗan jima duk sai ya yi haka.

 Can sai ruwan sama ya ɓarke kamar da bakin kwarya, sai bakon nan ya lunsashe idanunsa ya shiga minsharin ƙarya kamar ya yi bacci.

 Da farken nan ya ji gari ya yi tsit sai ya zabura ya figi burgamin nan taf da dakuwa ya auna da gudu daga shi sai gajeren wando ga shi ana ruwa.

 Da baƙo ya ga haka sai ya tashi sannu ya tafi ya tayar da mai gidan ya ce masa "Ka ji abin da mutumin nan ya yi mini".

Gari na wayewa sai mai gidan ya dauki bakon nan suka tafi suka shaida wa sarkin garin abin da ya faru. Sarki ya sa aka kama jakunan falke da kayan audugarsa aka sayar aka ba bakon nan aka ce ya ci da hakuri Allah ya saka masa.

Bako kuwa sai ya raba kudin nan biyu ya ba mai masukinsa rabi, rabi kuwa ya tara almajirai da nakasassu ya yi ta sadaka.

   Ya bar garin ana ta yi masa addu 'ar Allah ya kiyaye gaba. 









No comments:

Post a Comment