Friday, 7 July 2023

JIDAL

 JIDAL


Ance SARKI  RANAU ne ya soma zama a wurin. Wasu na cewa yazo daga Gaya ne ko yankin Rurum.

Daga ɗansa BAJADALI aka samo sunan JIDAL.

JIDAL tsohon birni ne da mutane suka rayu a cikinsa, akwai fadoji da sarakuna suka zauna, sannan garin zagaye yake da manyan duwatsu.

An rinƙa samun saɓani da rashin jituwa tsakanin Sarakin Jidal Bajadali da waɗansu fadawansa waɗanda suka yi rayuwa da iyayensa.


Ance BAJADALi yayi sarauta da ƙasaita bayan gushewar Ranau, ya zauna a fadar cikin kogo. Watakila shine akewa laƙabi da 'Zamna Kogo'.


Wani basarake ya zama abokin hamayyarsa, wanda bisa tallafin fadawansa aka hilace shi aka halaka shi.


Wani zamanin kuma, anyi wata sarauniya a JIDAL mai suna MAIRAMU, itama a saman dutse ta rayu.

Da akwai gagarumin tsaro da sarƙaƙiya kafin zuwa fadar zamna kogo da ma duk fadojin da sarakunan JIDAL suke rayuwa.

Har yanzu kufen JIDAL yana nan a ƙasar RANO, kuma da akwai abubuwan ban mamaki na tarihi da akan iya gani acan.

Wednesday, 5 July 2023

TARIHIN KAFUWAR KATSINA

 ASALIN KAFUWAR KATSINA DAGA LITTAFIN TARIHIN KATSINA


Sadiq Tukur Gwarzo


KAFUWAR Birnin Katsina

Ga abinda yazo daga littafin tarihin Katsina

(Kitabu Taarikh Ummaratu Hazihil Qaryatu Al-mashhuratu bi- Katsina min binaaiha ila yaumina haza” 


Da sunan Allah Mai Rahama Mai  jinkai, godiya ta tabbata ga Sarkin Sarakuna. Mun fada, Amma Allah ne mafi sami. Tabbas, Wannan ne tarihin Wannan  shahararren birni Mai  suna Katsina tun daga kafuwarsa kawo yanzu. Wasu masanan tarihin sun ruwaito cewa tsohon birnin ya gabaci Adaamus (ance wani shahararren Sarki ne da aka taba yi a Kasar Hausa) da shekaru 4. Sannan masanan sun tafi akan cewa  BAGANI JARGO wanda ya Gina ganuwar birnin ya sarauci Katsina tare da zuriyarsa har tsawon shekaru dubu uku da hamsin kafin zuwan  SANAWU (Wanda a zamaninsa Musulunci ya shigo Katsina) wanda ya dauki gabarar sarautar birnin. 

 To Amma, Sanawu, da Bagawu da Katsina, sun kasance shahararrun 'ya'yan Bawo ne, Kuma sun wanzu a mulkin Katsina na tsawon lokaci. Sun yi mulki na tsawon shekaru dari Tara.

Daga nan sai MUHAMMADU JANHAZO, dashi da zuriyarsa sun shimfida mulki na tsawon shekaru dari biyu da ashirin.  

  Har ila ya, an ruwaito cewa TSAGA RANA ya shafe shekaru hamsin da bakwai (  Masani Dr Yusufu Bala Usman ya ambace shi a matsayin Sarki na bakwai, ya yi sarauta a wuraren 1767-68)

Sa'annan ya baiwa babban dansa mulki, sunan sa WARI MAI-KYERAAYI, wanda ya shafe shekaru goma Sha uku Yana sarauta (ya mulki Katsina daga 1649-1660. 

(A zamanin mulkinsa ne ya yaki Kano, Abdullahi Yana sarautarta. Ance sai da ya taba rarakar Kanawa har sai daya tuke dasu zuwa kofar Kansakali ta birnin Kano sannan ya juyo).

 Sannan ya Mika mulki ga GIMA da ga Daqaasariy, shima ya shafe shekaru talatin da biyar yana sarauta, daga Nan sai AGWARAGI ya karba Wanda yayi mulki tsawon shekaru arba'in da biyu. (Ance shine Sarkin Katsina na takwas, ya yi mulkiba wajajen 1778-96. Tarihi ya KIYAYE cewa Agwaragi shahararren Sarki ne, a zamanin sa.ne Katsina ta kwaci Wata takobindaga hannun Sarkin Gobir a zamanin da ake Karin battar yaki tsakanin Katsina da Gobir din, sunan takobin Bee-bee. Har yanzu, nasarar Katsinawa akan Gobirawa na daya daga ababen alfaharin Katsinawa;  a duba KATSINA: a historical document wanda Centre  Regional de Documentation Pour la Tradition Orale Niamey ta wallafa a 1970.)

 Daga shi sai GWOZO, maruwaitan tarihi sunce ya shafe shekaru talatin da bakwai Yana sarauta. Sauran shekaru Sha ukun da suka rage, sarakuna irinsu     MUHAMMADU AL-ZAAHID wanda bai Jima kan sarautar ba, har manya nesanta kansa daga  abubuwan duniya har ma Daya karshe ya yanke shawarar murabus yin daga sarauta, watakila shine silar lakaba Masa suna  Al-Zaahid (Mai gudun duniya). 

Akwai da yawansu wadanda muka manta sunayensu tare da lokutan da suka yi mulki kafin tukewarsu zuwa ga Mallam Umar (Ummarun Dallaje Wanda ya kafa tutar Shehu Usmanu a Katsina, Kuma Wanda aka wallafa littafin a zamanin sa 1807-1835). Karshe! (Godiya ga SALISU BALA Wanda ya alkinta Mana shi)


ASALIN Sunan Katsina

Labari mafi inganci shine, sunan tsohon birnin Katsina 'DURƁI TA KUSHEYI'. Sunan mutanenta Durɓawa. Wasu na cewa asalin Durɓawa maguzawa ne tsatson mutanen NOK da Kwatarkwashi dube da kaburburansu da aka samo masu tsayi kamar falwaya, amma waɗansu na cewa asalinsu Mallawa ne daga Mali suke.

Da akwai mabanbantan Ra'ayoyi dangane da ASALIN inda aka samo Sunan  KATSINA

1. Ra'ayi na farko na cewa, an samo sunan ne a zamanin Sarki MUHAMMADU Korao, a lokacin da ya Sanya wani makusancinsa mai suna Katsina ya ringa duba yadda ake Gina ganuwar Birnin a madadinsa. 

2.  Ra'ayi na biyu: Akace sunan Katsina ya samo asali ne daga Sunan wata mace mai suna matar sarki Mai suna KATSI wadda ta fito daga  Durbawa, mazaunan birnin na farko. Ance ta bar tsohon garin Katsina ne zuwa inda sabon birnin yake, a lokacin Yana matsayin karamin kauye, ba tare da an sani ba, da aka bazama nemanta sai aka risketa, shine mazaunan garin suke cewa 'Ai KATSI NA NAN'.

3. Ra'ayi na uku na cewa Sunan Katsina  ya samo ne daga wani Sarki da aka taba yi Mai suna Katsina Dan Bawo. Amma marubuci Tijjani Lawal Ingawa yace Sarki Katsina dan Kumayo ne a wani rubutunsa.

Monday, 1 May 2023

BONONO WAI RUFE ƊAKI DA ƁARAWO

 BONONO

SADIQ TUKUR GWARZO

Kamal Iyantama ne ya ja hankali na a wani rubutunsa mai nuni da yadda wata Marubuciya ta halarci wani taro sanye da tufafi mai nuna tsiraicin jikinta.

   Don haka sa'ar da na halarci taron Marubuta, tunda ina da wancan ilimin a ƙwaƙwalwata, na zuba ido naga wacce zata kwata irin wancan abin da ya faru. Kwatsam sai kuwa na hango ta.

   Shahararriyar marubuciya ce fa, ina girmama ta, tana shiga sha'aninmu sosai. Tufafin da ta sa ƙasaitacce ne. Irin wanda ake cewa ɗan ubansu! Daga kallonsa na san mai tsada ne wanda sai hamshaƙan mata ke ɗaurawa.. aibunsa kaɗai shine rashin rufe tsiraici. Wannan ne yasa na tuno da wata shahararriyar Hikayar Amurka mai suna 'The Emperor has No Clothes'. Bari na sanar daku wannan hikaya a taƙaice.

Wani Sarki aka taɓa yi mai son ƙawa a ƙasar Turai. Sai rannan wani maɗinki yace masa zai ɗinka masa tufafin da babu tamkarsa da wani zare na musamman. Sarki ya ɗauki tarin dukiya ya bashi. 

Tun Kafin Maɗinkin ya gama aiki har Sarki ya sa anyi shela cewa za  a ɗinka masa tufafin da babu tamkarsa, don haka yana son jama'ar gari suzo kallo a ranar da zai sanya shi.

Da Maɗinki ya kawo tufafi, sai Sarki baiga komai ba. Maɗinki ya gamsar da Sarki cewa zaren da aka ɗinka kayan idanuwa basa iya ganinsa. Don haka akayi dabaru, aka sanyawa Sarki wannan tufafi. Sarki ya fito gaban jama'a yana ƙwambo a matsayin wanda ya sanya mafi ƙawan tufafi na zamani.

Ko da fitowar Sarki, sai jama'a duk suka razana, domin a zahirance Sarkin tsirara yake, to amma tun kafin fitowarsa an sanar dasu cewa zaren tufafin sarki ba kowanne ido ke iya kallo ba. Don haka ba tsiraicin suke kallo ba, tufafin suke kokarin ganowa.

A haka, sai wani yaro ya kasa dannewa, ya ɗaga murya yana mai cewa "The emperor has no clothes". Watau, Sarki fa a tsirara yake! Daga nan kuwa sai hankalin jama'a ya dawo jikinsu cewa wannan fa rainin hankali ne, Sarki tsirara yake babu komai a jikinsa! Daga nan mutane suka watse cikin takaici. Sarki kuwa yayi turus, kunya duk ta lulluɓe shi.. ƙarshen mulkinsa kenan!

A irin rayuwar da muke ciki fa kenan (Fake life), mun fi yin abu don burga da burge mutane sama da cimma buƙatu na zahiri. Abinda ke faruwa a zahirin rayuwa daban, abinda muke kallo daban, sannan abinda muke muradi ma daban.. Wohoho!

 Don haka, manufar tufafi ga ɗan adam shine rufe tsiraici. 

Ko nawa ka kashe wajen siyen tufa, matsawar bata rufe tsiraici ba to anyi abinda ake kira BONONO.

Yin Bononon tsiraici kuwa, yana jan hankalin shaiɗanu ga mata, sannan ga uwa uba tsinuwar mala'iku.

Fatana, Allah ya sa ƴanuwana mata su faɗaka!

ALAƘAR TARA DUKIYA DA SHEKARU

 ALAƘAR TARA DUKIYA DA SHEKARU



SADIQ TUKUR GWARZO


Kafar ƙididdigar manyan lamurorin duniya mai suna 'World of statistics' ta yi bajekolin sunayen manyan Attajiran duniya tare da shekarunsu a lokacin da suka soma kasuwanci.

   Wannan bayani gagarumi ne a garemu, dube da muhimman abubuwan da zamu iya zakulowa daga gareshi musamman alaƙar dake tsakanin tara dukiya da kuma shekarun ɗan adam. 

 Ga kaɗan daga abinda binciken ya ƙunsa;-

1. Jadawalin sunayen na ƙunshe ne da Attajirai guda 38, 27 Amurkawa ne, guda 3 Indiyawa, sai saura daga sauran ƙasashe.

2. Mutanen da suka soma kasuwanci har suka zama Manyan Attajiran Duniya daga shekarun haihuwa 0- zuwa shekara 19 guda 2 ne kachal,

 sai shekaru 20-29 guda 9, 

30-39 guda 5,

 40 - 49 guda 12, 50-59 guda 7,

 sai 60+ guda 3.

3. Binciken na nufin tara arzikin kasuwanci ba a daɗewar soma kasuwanci take ba, yafi ga manyantakar shekaru wajen soma kasuwancin, domin idan aka lura za a ga cewa ɗan adam ya kan samu cikar hankalinsa daga shekaru 40, kuma attajirai 27 ne suka zama shahararru waɗanda suka soma kasuwanci bayan sun cika shekaru 40 daga cikin 38 na mafi shaharar attajiran duniya. 

4. Binciken na nufin masu shekaru (40+) sunfi gam-da-katarin dacewa da samun arzikin kasuwanci sama da matasa (matasa ƴan ƙasa da shekaru 30 guda 11 ne kachal a jerin sunayen)

5. Idan har yawaitar shekarun ɗan adam a duniya  na nufin yawaitar ilimi gami da gogewar mu'amala da mutane da samar da sabbin abubuwan da zasu amfane su, to muna iya cewa babu matashin da zai cimma gagarumar nasarar kasuwancinsa har sai ya koyi darussa daga attajirai masu shekaru sannan ya labbaƙa irin ɗabi'o'insu.

6. Binciken na tabbatar mana da cewa dukiya tafi son zama kusa da masu shekaru, wataƙila saboda ɗabi'unsu na sarrafa dukiya yafi tafiya dai-dai da wanda takeso. A kwanakin baya Mawaƙi Davido ya shaidawa duniya cewa a duk sa'ar da ya haɗu da attajiri na ɗaya a Afirka, Aliko Ɗangote, abinda yake faɗa masa shine "Ka tattala dukiyar ka". Don haka, kasancewar 'tattala dukiya' wani lamari ne da yake buƙatar tsawon lokaci kafin a samu ƙwarewa akansa, tana iya yiwuwa shine dalilin da ya sanya masu tarin shekaru (40+) suka fi dacewa sama da matasa.

(Masha Allahu Rabbi, amma dai Allah ke bayar da arziƙinsa wanda yaso kuma a sa'ar da yaso)


Ga jerin sunayen da kafar ƙididdigar ta saki:-

🇺🇸 Bill Gates (Microsoft) - 19

🇺🇸 Mark Zuckerberg (Facebook) - 19 

🇺🇸 Walt Disney (Disney) - 21 

🇺🇸 Steve Jobs (Apple) - 21

🇮🇳 Ritesh Agarwal (OYO) - 22

🇺🇸 Bill Clerico (WePay) - 22

🇺🇸 Jack Dorsey (Twitter) - 23

🇺🇸 Larry Page (Google) - 25

🇺🇸 Sergey Brin (Google) - 25

🇮🇳 Dhirajlal Ambani (Reliance) - 25

🇨🇳 Jack Ma (Alibaba) - 29

🇺🇸 Elon Musk (SpaceX) - 30

🇺🇸 Jeff Bezos (Amazon) - 30

🇺🇸 Oprah Winfrey (Harpo) - 32

🇺🇸 Estée Lauder (Estée Lauder) - 38 

🇺🇸 Henry Ford (Ford) - 39 

🇺🇸 Vera Wang (Vera Wang) - 40 

🇺🇸 Jeffrey Brotman (Costco) - 40

🇺🇸 Robert Noyce (Intel) - 41

🇫🇷 Christian Dior (Dior) - 41

🇺🇸 John Warnock (Adobe) - 42

🇺🇸 Ralph Roberts (Comcast) - 43

🇺🇸 Donald Fisher (The Gap) - 44

🇺🇸 Sam Walton (Walmart) - 44 

🇺🇸 Bob Parsons (GoDaddy) - 47

🇯🇵 Yoshisuke Aikawa (Nissan) - 48

🇮🇪 Tony Ryan (Ryanair) - 48

🇺🇸 Bernie Marcus (Home Depot) - 49

🇺🇸 Gary Burrell (Garmin) - 52

🇨🇭 Henri Nestlé (Nestle) - 52

🇺🇸 Ray Kroc (McDonalds) - 52

🇮🇳 J. C. Mahindra (Mahindra) - 53

🇹🇭 Chaleo Yoovidhya (Red Bull) - 53

🇺🇸 John Pemberton (Coca-Cola) - 54

🇯🇵 Kawasaki Shozo (Kawasaki) - 59

🇺🇸 Charles Flint (IBM) - 61

🇺🇸 Bill Porter (E-trade) - 63

🇺🇸 Colonel Sanders (KFC) - 65

Wednesday, 1 February 2023

ABUBUWA TARA GAME DA FASAHAR CHATGPT

Abubuwa tara muhimmai game da FASAHAR ChatGPT


Sadiq Tukur Gwarzo

(A.A Gwarzo Learning Institute @AAGHOLI)


-Kamfanin Amurka mai suna OpenAI mai bincike akan fasahar AI (Artificial Intelligence) ne ya samar da wannan fasaha a watan Nuwambar 2022, attajiri na ɗaya a duniya Elon Musk na daga waɗanda suka assassa kamfanin OpenAI a 2015

-An gina Fasahar AI (Artificial Intelligence) bisa sigar koyar da Na'ura mai ƙwaƙwalkwa wajen tattaro bayanai daga mabanbantan wurare tare da yanke hukunci gwargwadon abinda ta iya riska tamkar dai yadda ɗan Adam yake iya yi. Misalin fasahar AI shine shafin writesonic.com inda mutum zai iya umartar Na'ura ta samar masa da gamsasshen bayani daga ƙaramar saɗara.

-Fasahar ChatGPT (Chat Generative Pre-trained Transformer) na nufin wani ɗan mutum-mutumin (mai amfani da fasahar AI) na'ura mai ƙwaƙwalwa wanda mutum zai iya tuntuɓa domin zartar masa da wani aiki babba ko ƙarami a sigar mutum tamkar yadda ake sadarwa tsakanin mutum da mutum.

-Wannan fasaha ta ChatGPT ta kafa tarihi wajen samun karɓuwa sama da kusan ɗaukacin fasohohin da ake samarwa a duniya; a tsawon kwanaki biyar kacal da fara ta sai da mutane miliyan ɗaya sukayi rajista da ita, zuwa yanzu kuwa fasahar ta samu karɓuwa a wajen kimanin mutane miliyan 500.

-Mutum-mutumin ChatGpT na da basira matuƙa kamar ɗan adam, don haka akan iya umartarsa yayi rubutu akan wani lamari na ilimi, kuma zai iya yin hamshaƙin rubutu tamkar yadda ƙwararre a fannin zai iya yi, misalin; fayyace ma'anar wani abu, ko rubuta waƙa, ko yin zane, ko warware wata daga matsalar lissafi, ko kuma uwa uba rubuta kundin masarrafa mai ƙwaƙwalwa. 

-Attajiri Bill Gates, mutumin da ya kafa kamfanin Microsoft, yayi gargaɗin cewa anan gaba fasahar ChatGpt na iya kawwame ɗumbin mutane daga samun ayyukan yi bisa ganin yadda fasahar take iya yin ayyukan da ƙwararru ke gabatarwa cikin ƙanƙanen lokaci.

-Tagomashi: Ana iya umartar fasahar da bayar da bayanai muhimmai game da abubuwan da ake da buƙata, misali;

"Explain quantum computing in simple terms" →

"Got any creative ideas for a 10 year old’s birthday?" →

"How do I make an HTTP request in Javascript?" 

-Ƙalubale: Har yanzu fasahar jaririya ce, tana iya bayar da raunanan bayanai gaɓe da abinda aka tambayeta, ko ta bayar da bayanai masu hatsari ga lafiya a matsayin amsar wata tambayar da aka yi mata, sannan an haƙƙaƙe cewar tana da ƙarancin sani game da muhimman abubuwan da suka faru ƙasa da shekarar 2021.  


- Akwai masarrafai da dama da mutum ke iya saukewa don amfanuwa da wannan fasaha, sai dai da yawansu na kuɗi ne. Hatta a zauren whatsapp ana iya shigar dashi ta yadda zai zamo tamkar abokinka da zaka rinƙa tambaya abubuwa ko ka sanya shi yayi maka rubutun zube, ko rubutun waƙa, ko zane, da makamantansu, amma dai babban shafin ChatGPT shine https://chat.openai.com 

Monday, 23 January 2023

Matsalar kuɗi

 Matsalar kuɗi


 (Money Problem)

Sadiq Tukur Gwarzo

Zuwa yanzu, abinda zantukan ilimi suka tabbatar shine, kowanne mahaluki a wannan duniyar yana da matsalar kuɗi, walau Attajiri ko Faƙiri, babban abinda ke rarrabewa a tsakani shine hanyar da kowanne mutum ke bi wajen warware matsalar kuɗin da ta fuskance shi, don haka wannan ɗan rubutu zai kalli waɗannan matsaloli da hanyar fita daga garesu.

Kuɗi wasu kawwamammun abubuwa ne masu ƙayyadajjiyar daraja wadda kowa ya yarda dasu, walau su kasance na takarda ko sulalla, ko na ma'adinai, ko su kasance taskantattu a wani muhimmin wuri wanda kuma ake amfani dasu wajen mallakar darajoji.

   Da yawan mutane sun ƙwallafa a ransu cewa basu da wata matsala sama da matsalar ƙarancin kuɗi, saboda sun lura da cewa wanda ya tara kuɗi yana da ikon warware yawa-yawan matsaloli, don haka babban burinsu shine su tara mamakon kuɗaɗe.

Akwai zantuka biyu masu cin karo da juna dake tattare da kuɗi gami da alaƙar kuɗin wajen tunzura aikata ayyuka musamman munana a wannan duniyar. 

Zance na ɗaya yana cewa "Son kuɗi shine tushen aikata duk wani laifi", yayin da zance na biyu ke cewa "Rashin kuɗi ne silar dukkan wasu munanan ɗabiu".

Sau tari da zarar an ambaci matsalar kuɗi, abinda ke zuwa a zukatan mutane shine 'ƙarancin kuɗi'. Yawa-yawan mutane ita suka sani, saboda ita tafi yawa, kuma ita akafi sani a matsayin matsalar kuɗi, amma a zahiri, abin ya haura haka.

 Ga abinda nazari ya nuna game da kuɗi da masu kuɗi:-

-Daga cikin mutanen duniya balagaggu sama da biliyan biyar, mutane miliyan sittin da biyu da rabi ne suka mallaki kashi 47.8 na arzikin duniya (1%). 

-Rahoton Oxfam na 2021 ya nuna cewar mutane goman da suka fi kowa kuɗi sun mallaki arziƙin da ya haura abinda mutane biliyan uku da miliyan ɗari ɗaya suka mallaka.

-Kashi 27 na attajirai sun faro ne daga tsatson talauci (Bank of America)

-Kashi 46 na attajirai sun samu arziƙi daga kyakkyawar tarbiyar sarrafa dukiya gami da gadon jari ko na kasuwanci  (Bank of America).

Saboda haka a taƙaice, matsaloli biyu ne ke tattare da kuɗi

1. Matsalar Ƙarancin kuɗi

2. Matsalar Yawaitar kuɗi

Kowacce babbar matsala ce wadda idan baka san yadda zaka yi da ita ba haƙiƙa zaka kasance cikin gagarumar matsala.

Attajiri na ɗaya a Afirka, Aliko Ɗangote, ya haɗu da matsalar ƙarancin kuɗi a shekarun baya, lokacin da yake ƙoƙarin gina gagarumar matatar man fetur ta afirka, amma saboda shi gwani ne a wajen warware matsalar ƙarancin kuɗi, ya jima da warware matsalarsa ba tare da kowa ya sani ba.

  Ɗangote yana sahun kaso 46 na daga ƙididdigar bankin Amurka, watau sahun attajiran da suka samu arziƙi daga kyakkyawar tarbiyar kasuwanci gami da jalin soma kasuwancin. Don haka tun da jimawa, ya gina ɗabi'unsa akan tarbiyar sarrafa dukiya, maimakon burga da burgewa. Wannan ya sa kuɗi da kansa yana son zama a tare dashi.

Matsalar ƙarancin kuɗi ita yawa-yawan mutane ke fama da ita, tunda ga abinda rahoton Bankin Amurka ya nuna can a sama, don haka da yawan mutane ke ɗaukar kuɗi shine jindaɗin rayuwa.

A zahiri, matsalar ƙarancin kuɗi abu ne mai muhimmanci ga duk wanda ya fahimce ta, domin ita ke tunkuɗaka yin tunani da ayyuka waɗanda zasu sauya rayuwarka daga talauci zuwa arziƙi, waɗanda kuma zasu hana ka wawanci idan ka shiga sahu na gaba, watau kashi ɗaya bisa ɗari na Attajirai a duniya.

Wannan yasa koda attajiri ya tsiyace, ake kiran yanayin da ya shiga da suna 'Broke', saboda yanayi ne wanda ba tabbatacce ba, yanayine tamkar makaranta wadda zata ta ƙara masa haske da karsashin sake ginawa kansa arziƙin da zai fi abinda ya mallaka a baya. Amma shi talaka, saboda ɗabi'unsa na rashin tafiyar da dukiya yadda ya kamata, ko nawa ya samu na ɗan lokaci ne, sai aga kuɗaɗen sun gudu sun barshi, don haka ake yiwa nasa laƙabin da suna 'poverty'.

Matsalar yawaitar kuɗi tana sanya mutum ya zama rago, shashasha kuma wawa musamman a harkar rayuwa ko ta kasuwanci matsawar bai ɗauki darussan dake cikin yanayin ƙarancin kuɗi ba. Sannan wannan matsala, ta kanyi silar mutum ya mutu cikin ɓacin zuciya.

   Mun  ga haka a rayuwar Mashahurin mai Kuɗin nan Pablo Escobar ɗan ƙasar Columbia, wanda ake zargin ya tara dukiya daga dillancin miyagun ƙwayoyi.

 Pablo ne wanda ya taɓa zuba zunzurutun kuɗi kusan dalar amurka miliyan biyu a wuta domin ta ruru, ta samar da ɗumi wanda zai sa ƴarsa ta daina kyarmar sanyi.. a lokacin da ya tserewa kamun jami'an tsaro.

Pablo ya bi miyagun hanyoyi wajen tara kuɗi, ya kuma yi amfani da kuɗin wajen cimma muradunsa, ya sa an kashe mutane da yawa waɗanda suka ɗaga masa yatsa, ya gina gagarumar daula. D

A lokacin da gwamnati ta kama shi ta tsare a kurkuku sai da ya siye kafatanin jami'an jarun ɗin ya tsere, daga bisani aka sake kamo shi, inda aka bashi dama ya gina Fursuna tashi ta kansa, wadda ya cikata da kayan alatu, da ɗumbin kayayyakin more rayuwa, amma dai a ƙarshe, ana zargin ya kashe kansa da kansa saboda gudun kamun jami'an tsaro.. kuɗin ba suyi masa rana ba.

Wani rahoto na kafar Business Insider ta Amurka ya nuna cewa ko ɗa gareka idan yana samun duk abinda yake nema a wurinka, karsashinsa na yiwa kansa abinda ya kamata yayi raguwa yake yi matuƙa.

Wannan yasa daga rahoton sama, kashi 27 kaɗai na talakawa ke iya jure fafutikar gina dukiya daga ƙuncin ƙarancin kuɗi.. saboda kiran dukiya yana buƙatar waɗansu ɗabi'u waɗanda dole sai mutum ya soma aikatasu na tsawon lokuta kamar yadda marubuci Tom Corley ya kawo a littafinsa 'Rich Habits'  bayan ya shafe shekaru yana nazartar rayuwar attajirai.

Haka kuma dalili kenan da yawa-yawan attajirai (kashi 46 daga rahoton Bank of America) suka samu tarbiyar kafa kasuwanci da kuma jarin soma kasuwanci, saboda sun samu abinda yawa-yawan mutane basu dashi, don haka sunfi zarafin zamowa attajirai.

  Talakawa da yawa basu gane haka ba. Akwai ɗabi'u da ayyuka na mutane waɗanda ke ƙara cusa su cikin talauci, a tsammanin wasu, gwamnati zata rage musu raɗaɗi, amma akasari duk abubuwan da gwamnatoci ke yi suna ƙara dankwafar da talaka cikin talauci ne da ƙara arziƙa mai arziƙi, saboda a duk sa'ar da kace zaka yiwa mutum abinda ya kamata ya yiwa kansa, a zahiri cutar dashi kayi ba taimakonsa ba.

A taƙaice, Wajibi ne mutum ya koyi rayuwa da ƙarancin kuɗi matsawar yana so kada kuɗin su tunzura shi aikata shiririta a yayin da ya tsallaka fagen attajirai masu matsalar yawan kuɗi.

 Ga duk inda matsala ra samu, akwai wani darasi dake rattare da ita. Fahimtar wannan darasin da aiki dashi sune abubuwanda zasu ƙara maka daraja a ayyukanka na gaba.

 Sannan yana da kyau a sani cewa ba kuɗi ne mafi muhimmanci a kasuwanci ko a rayuwa ba, duk abinda zaka mallaka, matsawar ka rasa farin ciki, ai kuwa sam ba suyi maka rana ba. Haka nan, duk abinda ka rasa na dukiya, matsawar ka samu farin ciki, ai kuwa ka mallaki abinda ya fisu.

Saboda haka, idan kana da matsalar ƙarancin kuɗi, ya kamata ka soma koyon ilimin nema da sarrafa dukiya.

 Sannan idan har ka iya kafa kafar warwarewa mutane matsalolin dake damunsu, tabbas da sannu zasu kawo kuɗin da suka mallaka zuwa gareka.

Haka kuma, yana da kyau ka koyi dabarar farantawa na kusa da kai domin samun dacewa da farin ciki daga mahalicci..