Tuesday, 1 May 2018

TARIHIN KABILAR BABUR DAYADDA DABIUNSU NA AURE SUKE

BABUR MARRIAGE CULTURE AND RITUALS

TARIHIN KABILAR BABUR DA AL'ADUNTA NA AURATAYYA

DAGA SADIQ TUKUR GWARZO, RN

Kabilar Babur tana danganta asalinta ne da Mutanen Yamen, don haka aka ruwaito cewa rundunar wasu mutane ne sukaƴi hijira daga Yemen a wajajen shekara ta 600 miladiyya suka riski Kasar Sudan, sannan suka shigo cikin sahara tare da sauka a yankin da Kabilar Babur ke rayuwa a yanzu cikin kasar Borno.
   Ba iya kabilar Babur ba, har kabilun Kanuri da Luguda da wasunsu dake rayuwa a wannan yankin suna ikirarin asalin kakanninsu daga Yemen suke. Gusawar zamani ne kurum ya sanya takamaimen tarihinsu ya sauya.
   Zuwa yanzu dai, ana samun kabilar Babur ne a Jihohin Borno da Adamawa.
  A jihar Borno, akwai kabilar Babur a garuruwan Biu, Hawul, Kwaya kusar, Shani, Kwajaffa, Sakwa, Marama, Shaffa, Wandali, Kida, Miringa, Buratai, Zuwa, Yimirshika ,Hyera ,Dayar, Fumwa, Azare, Gwaski, Diragina, Yimana, Gwallam, Tiraku, Shindiffu, Goski, Pela Birni, Wangdang, Bula tawewe, Kogu Tashan Alade, Kida, da hang shang  da kuma Bayo, amma a jihar Adamawa kabilar Babur sunfi yawa a garin Garkida cikin karamar hukumar Gombi.
  Dukkan waɗannan garuruwa da Kabilar Babur ke zaune ciki nada nasu tarihin.
  Misali, ance jarumin daya kafa daular mulki ta Biyu mai suna Yamta, ɗane ga wata mace 'yar kabilar Mandara.
  Wai Tun tana da cikinsa aka ɗauke ta zuwa gidan Sarkin Borno, don haka acan aka haifeshi kuma acan ya taso da tarbiyar kanuri.
  Amma da Yamta ya girma, sai ya tumbatsa wajen jarumta. Shine fa harbya karɓe ikon yankin da Biu take ayau tare da kafa masarauta.
   Ana ganin ya fara kafa mazaunin masarautar sane a wani wuri mai suna 'Limbur' tsakanin chikorkur da Mandagarau. Har zuwa yanzu kuma ance kabarinsa yana nan a Limbur ɗin.
  Kabilar Babur, sune keda rinjaye a garin Biu da wasu garuruwan makwabta, amma akwai kuma kabilar Bura wadda ke zaune a makwabciyar kasar Babur ɗin, mai suna 'Babur Bura'. Dukkansu kusan da yare ɗaya suke amfani, kuma yaren yana da kamanceceniya dana garuruwan Chibok, Marghi, Higgi , Kilba and Bazza.
 Anfi samun kabilar 'Babur Bura' a jihohin gabashin Nigeria, watau Borno, Adamawa, Gombe da Yobe.
  AL'ADUN AURE
Mafi yawan kabilun Borno musamman Kanuri, Shuwa Arab da Babur nada kamanceceniya wajen al'adun auratayya. Watakila hakan ya faru ne saboda jimawar kabilun wajen zaman tare ko kuma ana iya cewa kakanninsu ne ɗaya, don haka daga garesu sukayo gadon ɗabi'un.
  Bisa al'ada ta Kabilar Babir, Idan namiji yaga mace yana so, to bazai sanar mata ba, sai dai ya nemeta da abota.
  A wannan abotar ne zai rinka bincikar halayyarta dana magabatanta, ba tare da ta sani ba, daga bisani kuma sai ya samu wani dattijo a danginsa ya ɗora masa alhakin kammala masa bincike akan yarinyar da zuriyarta duka.
  Daga wannan matakin kuma sai mai neman auren ya zaɓi maza uku da mata biyu akalla, daga danginsa su rakashi gidan su yarinya.
   Anan ne zasu haɗu da iyayenta ko 'yanuwanta, har kuma a tambayeta abinda ke tsakaninsu da wannan mai neman auren nata, da kuma muradinta akansa da sauransu.
  Idan an aminta a kulla auratayya, to daga nan ne za'a sanya ranar yin Baye, suna kiranta 'Yuyma'.
  Idan ranar tazo, dangi zasu haɗu daga ɓangaren namiji da mace maza da mata a gabatar da kayan ci dana sha, sanna a sanya ranar aure, watau “Mbwa Nyika”.
  Dangane da batun kuɗin aure ko sadaki, namiji na iya bayar da dukkan abinda ya samu gareshi ga iyayen wadda yake so ya aura, sukuma zasu ciri wani abu kaɗan su mayar masa da ragowar, (wasu ma ance basa cirar kome), to amma za'a gabatar masa da sunayen wasu abubuwa da akeso ya siya mata.
  A hakan ma, ba dole bane ya siyi dukkan komai ba, kawai dai yana iya zaɓar abinda yake da iko ne ya siya.
  Idan namiji ya haɗa kayan, sai ya tashi yan uwansa su tafi sukai gidan su yarinya. Daga nan kuma za'a saurarar ranar ɗaura aure.
  Daura aure kuwa ya danganta da addinin da mutum yakebi, kasancewar addini yayi tasiri cikin kabilar Babur, don haka kiristocin cikinsu sukanje chochi ne domin ɗaura aure, yayin da musulman cikinsu kan ɗaura aure a Masallatai ko gidaje, tare da aiwatar da al'adun aure kalar wanda musulunci ya halatta

Friday, 20 April 2018

HIKAYAR WASU KWARTAYE

HIKAYAR WANI BAKO GA SARKI MAI SUNA 'DUNIYA'

Tare da SADIQ TUKUR GWARZO

Akwai wani Babban bafaden Sarki a wani garin Hausawa, yana da wata mata kyakkyawar gaske, wadda ake yawan sanar dashi cewa tana tara maza a gidansa, amma sam baya yadda.
Watarana sai wata Tsohuwa ta kirawo bafaden nan, tace masa "kullum idan ka tafi fada, matarka maza take tarawa. Amma idan kanason ka gane hakan, sai kace mata zakaje unguwa kauye, acan zaka kwana, inyaso sai ka dawo kafin lokacin don ka ganewa kanka abinda ke faruwa".
  Sai kuwa bafade yace da tsohuwa, "haka nan za'ayi". Daga nan ya tafi ya samu mai ɗakinsa ya sheda mata cewa zai tafi unguwa sarki ya aikeshi kauye, bazai dawo ba sai gobe.
Bafade yahau dokin sa, ya bar gida abinsa.
Matar gida kuwa ta samu abinda takeso.
 Mai gida ya tafi bazai dawo ba, don haka ta yanke shawarar aikewa masu nemanta cewa yau gida a buɗe yake.
Daga cikin waɗanda ta aikewa akwai Wazirin gari, da Galadiman gari, da kuma wani babban bako na Sarki mai suna Duniya, dukkansu suna nemanta.
Nan da nan waziri ya aiko da kaɓakai na nama da shinkafa, yace wa matar gida ta gyarasu yana nan tafe zuwa dare.
Dare nayi kuwa sai ga waziri fagan-fagan, ya karaso gidan bafade. Matar bafade ta taryeshi da abinci da nama wanda ya aiko dasu.
Ya zauna yana ci kenan, sai ya jiyo sawun takalma, nan fa hankalinsa ya tashi, tsammaninsa Maigida ne yake zuwa. Sai yayi wuf ya shige karkashin gado.
Ashe galadima ne ya samu karasowa.
  Nan ma sai matar gida ta tarbeshi da kissa, ta gabatar masa da abincin da waziri ya bari. Galadima ya zauna ya fara cin abinci ana fira, sai shima ya jiwo sawun takalma.
Hankalinsa ya tashi, tsammaninsa Maigida ne, ya tambayi matar gida ina mafita, ita kuma sai ta nuna masa karkashin gado, inda waziri yake, nan take kuwa yayi wuf ya auka. Ashe bakon sarki mai suna Duniya ne ya shigo.
 Koda Galadima ya shiga karkashin gado, sai ya fahimci akwai wani bayan shi aciki. Daya duba sosai sai ya gane ai waziri ne.
  Galadima yace Waziri me kakeyi anan? Waziri yace Kaga Galadima, abinda ya kawoka shi ya kawo ni, saboda haka mu rufawa kanmu asiri.
Galadima yace aikuwa haka nan ne.
Suna nan suka jiyo muryar Duniya da matar gida suna taɗi, shima an bashi abinci kamar yadda aka basu. Daga nan su waziri suka gane ashe ba Maigida bane, Duniya ne.
Ba'a jima ba sai suka jiwo karar kofatan dawaki, alamar Maigida ya dawo kenan. Nan da nan Duniya yayi wurgi da kwanon abinci, ya tashi tsaye yana dube-duben mafita, can ya hango karkashin gado, sai kuwa yayi wuf ya auka.
Da shigar sa shima sai yayi arba da mutane biyu a ciki. Ya kalle su a tsanaki ya ganesu, yace Waziri!! Galadima!! Me ya kawo ku nan? Sukace muna gama ka da Allah mu rufawa juna asiri. Duniya yace to shikenan. Sai kowa cikin su yayi tsit kamar ruwa yaci su.
Maigida ya sauko daga kan dokinsa sannan ya daure shi, yace mai ɗakinsa ta bashi ruwa ya wanke jikinsa, da ta kawo masa ya gama kimtsawa, suka suka shiga cikin ɗakin tare, ya zauna a gefen gado.
Maigida yana cike da mamakin Kazafin da ake yiwa matarsa, tunda ance idan yayi haka zai kama matarsa da maza, gashi kuma yayi bai kama ta ɗin ba. Shine yake fadin "duniya.. duniya,, duniya"
Matar gida tace "Maigida me ya faru ne kake kiran duniya?"
Maigida yaci gaba da cewa "Duniya, duniya, duniya ba gaskiya"
Shikuma Duniya dake karkashin gado sai hankalin sa ya tashi, abinka da bako, tsammanin sa Maigida sunan sa yake kira. Sai yayi wuf ya ce "Haba maigida, yanzu sunana kaɗai kake kira alhali ga Waziri ga kuma Galadima?"
 Maigida ya tashi zumbur, yana fafutikar neman madoki, kafin kace haka tuni galadima da waziri da Duniya sun fara kacaniyar fitowa daga karkashin gado domin arcewa a na kare...

Thursday, 19 April 2018

TARIHIN BIRNIN LALLE DA SARKIN SU KUTTURU

Tarihin Birnin Lalle da sarkin mutum-mutumi, MAI SUNA Sarki Kututturu.

Sadiq tukur gwarzo, rn.
 
Daga abinda marubuci Dan Zubairu ya ruwaito, masarautar Birnin Lalle dake can a yankin Dakoro na Jahar Maraɗin Jamhuriyar Nijar, shahararra ce wadda ambatonta ba zai yanke ba.
  Kasancewar Birnin Lalle ɗaya ne daga tsoffin cibiyoyi ga Masarautar Gobir, ana ganin Gobirawa ne suka kafa garin. Amma kuma akwai alamu dake nuna cewar tun da jimawa Birnin Lalle ya kafu, kawai dai gobirawa  sun shigo cikinsa ne tare da kwace ikon sa.
   Birnin ya samo sunansa ne daga yawaitan bishiyoyin Lalle (wanda mata ke kunshi da kuma wanka dashi a baya) dake cikinsa.
   Birnin lalle shine birni na gaba da Gobirawa suka sauka tun bayan barowarsu daga Birnin Marandat da Birnin Toro. Da yake daman ance asalinsu daga Baghaza suke, suka shiga duniya, har kuma a hankali suka rinka sauka a garuruwa suna auratayya da yake-yake.. A haka har suka riski birnin Lalle.
   Masu cewa gobirawa ne suka kafa wannan birni na Lalle ɗaruruwan shekaru da suka gabata, sun faɗi cewar Gobirawa sun riski wajen ne yana fili sa'ar da suke neman gulbi ko tabki a wannan yanki domin su rinka gudanar da ayukkansu na noma, kasancewarsu daman bayan yake-yake, sukan jarraba noma tun tale-tale.
   Don haka ake ganin da isowar su bakin tabkin sai suka ga bishiyoyin Lalle burjik a zagaye dashi, shine sai suka baiwa wurin suna da cewa “Wannan wuri Birnin lalle kenan!”. Daga nan kuma suka yanke shawarar zama acikin sa.
    Amma dai wasu masanan tarihi sun tafi akan cewa Birnin lalle ya kafu ne tun kimanin shekaru 2000 da suka gabata. Sai dai kuma babu takamaimen sunan kabila ko mutanen da suka birnin.
   Haka kuma, ana ganin garin ya tumbatsa matuka a wani lokaci can a baya, amma ɓarkewar yunwa a wannan birni ce tayi sanadiyyar da Gobirawan suka tashi daga gareshi izuwa birnin Alkalawa dake tsohuwar masarautar Zamfara (wajajen karni na goma sha shidda).
   Sai dai duk da haka, ance garin ya sake haɓaka a wajajen karni na goma sha bakwai ta yadda fatake ke isa gareshi fatauci tun daga kano, lokacin ma garin maraɗi na karamin kauye, ko kuma ace sam bai kafu ba.
Ance Sarauniya Tahoua tayi mulkinta a birnin Lalle, ita kuwa itace sarauniya mace ta farko da aka yi a Gobir, kuma itace uwa ga waɗanda suka kafa Biranen konni dake cikin Jihar Tahoua a Jamhoriyar Nijar da kuma Argungu na jahar Kebbin Nijeriya.
   Sarki Kanni da Sarki Hammadin shine sunayen 'ya'yayen Sarauniya Tahwa, kuma sun tsira da rayukan sune bayan da suka gudu daga garin da dare, kamar yadda suka shawarta a tsakanin su.
  Dalilin hakan kuwa shine, an tilasta musu hawa kan gadon sarautar birnin ne alhali kuwa basu so.
   Kanni aka fara naɗawa sarki, dare nayi ya hau sirdi ya ɓace ba’a san inda ya dosa ba. Kashe gari aka naɗa kanin sa Hammadin, shima kuwa cikin dare ya bi ɗanuwan shi ya gudu.
  Ance Hammadin ya ɗan zauna tare da ɗan uwan shi Kanni a birnin Konni tsawon shekaru, daga bisani ya tashi bai sauka ba sai a Argungu.
  Mawakin gargajiya kuma masanin tarihi, Marigayi Alhaji Maidaji Sabon Birni ya faɗa a wani baiti cewar duk sa'ar da mahaifiyar Kanni da Hammadin watau Sarauniya Tahwa ta tuno yadda ta rasa 'ya'ayenta, sai ta dugunzuma cikin ɓacin rai, tace “Gobirawa haka kuka kai ni, bani ga Kanni, bani ga Hammadin?”
 Amma daga baya ance ta samu haɗuwa dasu bayan an gano mata inda suke. Shine ma akace an kaiwa Sarki Kanni matar shi mai ciki wadda ya gudu ya barta a Birnin Lalle, wasu masoyan sa kuma sukayi dandazo suka tafi gareshi domin zama tare dashi.
  Ance  Sarki Kanni da kanin sa Sarki Hammadi suna da tsagen Gobirawa guda shidda (6) a kuncinsu na tsagin hagu, da kuma guda bakwai (7) a tsagin dama,  amma da suka haihu sai suka yanke shawarar yiwa kowane ɗa  tsagu goma (10) a hagu da goma sha-biyu (12) a dama domin  bambamta su daga sauran 'yanuwansu Gobirawa.
      Game da Sarkin birnin Lalle Kutturu, wanda akan kira shi da suna Sarki Dalla Gungume, ya samu shiga cikin jerin sunayen da suka mulki wannan birni duk da kasancewar sa gungumen itace, watau sahun sarakuna irinsu Sarki Barankame, Sarki Kanni, Sarki Bartakeskes, Sarki Hammadin, Sarki Bartuwatuwa da wasunsu kimanin ɗari uku da tamanin (380).
  Asalin naɗa shi shine, ance akwai wani lokaci a baya, da husumar hawa mulkin Birnin Lalle tayi tsamari a tsakanin Gobirawa dake da iko da garin, ya zamana duk wanda aka ɗora sarki sai masu adawa dashi sunbi dare sun halaka shi komai tsarin sa, don haka sai dabarar sassaka gungumen itace a matsayin mutum-mutumi tare da sanya shi cikin ado gami da ɗora shi akan karagar mulki ya faɗo a zukatan manyan fadawan wannan masarauta.
 Bayan an yi bikin naɗin Sarki kututturu bisa karagar mulki, rannan sai waɗanda basu so suka sake yin yunkurin kawarda sarkin, kamar yadda suka saba yi ga duk wanda aka naɗa bisa wannan karaga, suka biyo dare ɗauke da makamai, amman sai suka tarar da Sarkin ɗangalgal bisa karagar shi.
    Da yake basu san shirin da akayi ba, sai kurum tunanin su ya basu cewa lallai wannan sarki hatsabibi ne, domin basu san adadin layu ko kahunan da ya tanada ba ta yadda ko gezau bai yiba a lokacin da suke fuskantar sa don su halaka shi, sai kurum suka rantaya da gudu.
  Tun daga nan kuma aka samu sauki, har kuma aka cigaba da naɗa mutane bisa mulkin Birnin Lalle.
   A ɗan lokacin da Sarki Kututturu yayi bisa mulki, waɗanda suka naɗa shine ke gudanar da harkokin mulki gami da zartar da duk wasu lamurori. Har ma an samu cewa idan mutane sunzo yin gaisuwar fada, sai fadawan su amsa da cewa “Sarki ya gaisheka”, don haka ake ganin watakila wannan ne mafarin irin wannan amshin gaisuwa a tsarin Shugabancin Hausawa.

Sunday, 15 April 2018

TARIHIN DAULAR KATSINA

TARIHIN DAULAR KATSINA

DAGA SADIQ TUKUR GWARZO

Maruwaitan tarihi sunyi ruwaya mabanbanta dangane da tarihin Katsina.
   Daya daga ciki itace mai cewa an kafa Daular Katsina ne a wajajen karni na goma sha uku, kuma wata zuria mai suna Ambutai ne suka fara mulkin birnin katsina a inda yake a yanzu,
  Wata ruwayar kuma tace Sunan sarkin Katsina na farko shine Kumayau, kuma shi jikan Bayajidda ne, ance shine wanda  ya kwace ikon masarautar Durɓi, daga nan ya haɗe masarautar tare da kafa cibiyar mulki a birnin Katsina.
  Wata ruwayar kuma ta tafi akan cewa Katsina ta kafu ne tun a shekarar 950 miladiyya, daga kabilar Nufawa wangarawa.
   Sai dai, watakila zance mafi inganci shine wanda maigirma Walin Katsina ya faɗa cewar asalin birnin Katsina karamin kauye ne, sai wata gimbiyar tsohon birnin Durɓi ta kusheyi mai suna Katsi ta gudo daga garin izuwa nan saboda wani dalili. Aka shiga nema ba'a gantaba, sai daga baya aka same ta a wannan ɗan kauye. Shine ake cewa Katsi-na-nan.. Daga nan sunan 'Katsina' ya samo asali har kuma a hankali cibiyar masarauta ta baro Durɓi izuwa nan, wanda yayi sanadin bunkasar garin.
  Dangane da tarihin asalin mutanen Durɓi, wasu sun tafi akan cewa asalinsu mutanen Mali ne masu fatauci suka kafa garin, yayin da wasu ke ganin dube da aiyukan maguzanci da suka auku a Durɓi, da bautar Magiro a Kwatarkwashi, sai ake ganin mutanen garin sunfi kamantuwa da zamowa jikoki ga mutanen tsohuwar daular 'Katsina Ala' data taɓa wanzuwa a ɗaukacin yankin.
   Kusan dukkan masu ruwaito tarihi sun yadda da cewa Kumayau shine wanda ya kafa Katsina tun farko, shine kuma shugabanta na farko, sai dai kuma akwai saɓani dangane da yadda tarihi ya nuna cewar a zamanin da ana zaɓen sarki a wannan masarauta.
  Wasu sun tafi akan cewar ta hanyar jifan mashi ake zama sarkin Katsina, watau duk wanda jifansa ya kerewa saura shine zai zama sarki.
  Yayin da wasu ke ganin ta hanyar kokawa ake zama sarkin Katsina, watau wanda ya kayar da wani shine sarki.
    Ance anyi sarakuna masu suna Ramba, Taryau, da Jatinnati a iya tsawon shekaru kimanin ɗari bayan kafuwar Katsina,  sannan Muhammadu Korau yazo daga wani gari mai suna 'Yandoto yaci nasara a gasar zamowa sarki.
  Wasu sunyi maganganu akan cewar sai da Korau ya haɗa kai da matar sarki Sanau tare da karya asirin sa sannan yaci galaba a gasar da aka shirya musu ta kokawa don zamowa sarki. Daga baya ya samu nasarar kayar da Sarki Sanau tare da  yanka shi da wata wuka mai suna 'Gajere', sannan kuma ya halaka matar tasa.
Wasu kuma na ganin sa'a kurum ya samu akansa.
   Ana ganin Sarki Muhammadu Korau yayi mulki ne a wajajen shekara ta 1445 miladiyya zuwa 1495, amma dai ana ganin shine sarki Musulmi na farko a daular Katsina, sannan shine sarkin daya mayar da cibiyarsa izuwa birnin katsina na yanzu da zama, haka kuma a zamanin mulkin sane shahararren malamin addinin musulunci mai suna Muhammad Abdulkarim al-maghili yazo birnin katsina tare da soma  karantaswa. A lokacin ne kuma aka gina tsangayu da masallatai manya, ciki kuwa harda hasumiyar Gobarau wadda har yau tananan cikin birnin katsina.
  Ance sarki Maje shine ya ɗora akan inda sarki Korau ya tsaya ta fannin yiwa addinin musulunci hidima. Ya wanzar da shari'ar musulunci, ya zama mai umarni da yin sallah akan kari, tare da tursasawa tuzurai yin aure.
 A shekarar 1513 akace Sarkin Songhai Muhammadu Askiya ya aiko dakaru kasar Hausa, har suka karɓe ikon Katsina.
   Ance a wajajen shekarar 1554 Katsinawa suka 'yantar da kansu daga masarautar Songhai, sannan a wajajen shekara ta 1570, suka samu nasarar yaki akan masarautar Kano, wadda take hamayya dasu a wancan lokaci. Amma babu jimawa sai akace daular Borno ta samu iko da ita na tsawon wani lokaci.
    Zuwa karshen karni na goma sha shidda birnin katsina ya zama cibiyar karantarwar addinin musulunci kwatankwacin Timbuktu, musamman saboda cikar garin da manyan malumma masu karantarwa.
 Daga cikin malaman akwai Muhammed Bin Masani al Barwani al Katsinawi (Dan Masani) wanda akace asalinsa daga Borno yake. Da kuma  Muhammad al-Katsinawi Ibn Sabbag (Dan Marina). Sai kuma Muhammad al-Fulani al Katsinawi.
  Shi Muhammad al Fulani shashararre ne a fagen ilimai na addini dana kimiyya dana falsafanci.  Ance bayan ya koyi karatu a katsina sai ya ɗauki haramar tafiya Makkah don yin aikin Hajji. Akan hanyarsa ta komowa ya sauka a Cairo yana karantarwa, har kuma ajali ya riskeshi a shekarar 1734. Amma an samu cewar yayi wallafe-wallafe na ilimi da dama, aciki har da wani littafi mai suna ‘al-Durr al-Manzum wa Khulasat al Sirr al Maktum fi Ilmi al-talasim wal Nujum’.
  Zuwa karshen karni na goma sha takwas aka samu cewar adawa gagaruma ta shiga tsakanin daular katsina da masarautar Gobir. Ance rigimar ta samo asali ne a lokacin da dakarun Gobir suka karɓe iko da birnin Maraɗi, daga nan suka fara turawa izuwa  Birnin Katsina.
  Sarkin Katsina na lokacin mai suna Agwaragi (1778-1799) ya tara rundunar mayaka domin yakar Gobirawa, amma cikin rashin nasara Gobirawa suka yiwa dakarunsa sukuwar sallah tare da tarwatsa su.
  Tun daga nan sai rikici ya cigaba tsakanin masarautun biyu, ya zamana ana gwabzawa lokaci bayan lokaci, har izuwa zamanin Sarkin Gobir Yakubu (1788 – 1795) wanda akace ya halaka wani shahararren makeri Bakatsine tare da kai farmaki garin Ruma wanda yake cikin kasar Katsina.
Daga karshe dai katsinawa suka gwabza da Gobirawa tare da halaka sarkin su Yakubu, suka sare wuyansa, suka tafi da kansa birnin katsina.
 Ance tun daga nan yaki ya kare tsakanin su.
  Haka nan masarautar Katsina ta rinka faɗaɗa a hankali, inda ta zamo giwa mai makwabtaka da masarautar kano a Gabas, Zaria a kudu, Zamfara a yamma, Daura da Damagaran a ɓangaren arewa maso gabashi.
  Manyan biranen tsohuwar masarautar katsina sune:- ‘Yandoto, Gozaki, Maska, Tasawa, Gazawa, Ingawa, Matazu, Ruma, Kwatarkwashi, Birnin Bakane, Karofi, Maraɗi, Gwiwa, Kanen Bakashe, da suransu.

Saturday, 31 March 2018

HIKAYAR WASU TSUNTSAYE

HIKAYAR MACIJI DA TSUNTSAYE

Sadiq Tukur Gwarzo, RN.

Wannan hikayar shahararra ce acikin littafin hikayoyi na 'Kalila wa Dhimma', musamman yadda aka rinka amfani da ita wajen koyar da yara masu jiran sarauta hikimomin kuɓuta daga zaluncin duk wani azzalumi.
  Hikayar tace:-
  A saman wata babbar bishiyar Kuka, anyi wasu tsuntsaye guda biyu waɗanda ke rayuwa acikin shekarsu dake saman wannan bishiya.
  Sai dai kuma akwai wata damuwa tattare da waɗannan tsuntsaye.
  Damuwar itace, duk sanda suka kyankyashe kwayayensu sai wani maciji ya zo ya shanyesu, shikuwa a kasan bishiyar yake rayuwa cikin  wani kogo.
  Kullum haka, kullum haka.
  Rannan sai sukayi shawarar suje su sanar da Mallam Dila domin ya basu shawarar hanyar kuɓuta daga wannan kunchi da suke ciki.
  Bayan sun same shi suke shaida masa irin zaluncin da maciji keyi musu gashi sun rasa yadda zasuyi.
  Dila yayi ajiyar zuciya, sannan yace "kada ku damu, komai karfin azzalumi, kaskantaccen abu yana iya cin galaba akansa cikin hikima"
  Yaci gaba da cewa "saboda haka, shawara ɗaya dazan baku shine, ku shiga cikin gari kuyi duba ga gidan dayafi kowanne arziki da kuma dakaru, sannan ku lura da abu mafi daraja wanda akayi sakaci dashi, sai ku ɗauko shi kurinka tafiya a hankali a hankali, da kunzo bakin kogon maciji sai ku wurgar dashi kuyi naku wuri.
  Tsuntsaye sukayi godiya sannan suka tashi firrr! zuwa cikin gari domin aiwatar da shawarar mallam Dila.
   Ai kuwa suna ta zagaya gari, sai suka hango 'yar sarkin garin tana wanka a cikin wani karamin tafki, ga abin wuyanta yana ta walwali ta ajiyeshi a gefe saman kayan sanyawarta, sai kuma dakaru suna ta shige da fice.
  Kwatsam sai gani akayi tsuntsuwa ɗaya tayi kasa-kasa tare da wuftar wannan abin wuya da bakinta, sannan ta tashi sama a hankali tana mai karkaɗa fuka-fukanta.
   Koda faruwar haka sai hankalin 'yar sarki da dakaru yakai gareta. Yar sarki ta daka musu tsawa da cewar subi bayanta su karɓo mata abin wuyanta.
  Ai kuwa a haka tsuntsuwar nan ta rinka janyo dakaru, ta sauka acan, da zarar sun runtumo gareta sai ta tashi, ta sake sauka a wani wurin, a haka har tazo bakin kogo sannan ta wurgar dashi.
  A wannan lokaci maciji nata sharar bacci abinsa, yaci abinci yayi hani'an, jira yakeyi dare yayi yahau sama don kara farauto kwan tsuntsaye kamar yadda ya saba.
   Karar wurgar da abin wuya kuwa sai ya tashe shi.
  Koda ya hango abu mai walwali sai yayi sha'awar zuwa don ganin ko menene.
  Yana daf da fitowa dakaru suka iso wurin suna ta haki, ɗaya daga cikinsu ya mika hannu zai ɗauki abin wuya amma sai ya jiyo motsi, dubawarsa keda wuya sai yaga maciji na fitowa gareshi.
  Nan take kuwa waɗannan dakaru suka rufar masa da duka da sanduna har sai da suka halaka shi, sannan suka ɗauki abin wuyan gimbiya suka tafi abinsu.
  Tun daga wannan rana tsuntsaye suka samu kwanciyar hankali, domin babu mai hanasu sakewa.

HIKAYAR SARKIN HINDU BHOJ

GA KOWANNE MA'ABOCIN ILIMI, AKWAI NAGABA DASHI: HIKAYAR SARKI BHOJ NA HINDU

DAGA SADIQ TUKUR GWARZO, RN.

Kasar Indiya nada mutane masu karancin ilimi matuka a yanzu. Wannan ne yasa 'yan siyasa da sauran masu kumbar susa suke abinda suke so, saboda yawan mabiyansu basu san abinda doka tayi tanaji akan hakkokin su na 'yan kasa ba.
   Sai dai kuma, an taɓa yin wani lokaci da jimawa a tarihin kasar Indiya wanda sai an sha matukar wahalar bincike kafin a samu mutum kwalli ɗaya wanda bai iya rubutu da karatu ba, bai kuma kiyaye hikimomi a kirjin saba.
   Anyi wannan zamanin ne a lokacin mulkin sarki Bhoj na daular Malwa dake tsakiyar Indiya a wuraren shekara ta 1010-1055 miladiyya.
   Ance a wancan lokaci, duk talaucin mutum, zaka sameshi yana iya karanta littafin addininsu mai sun Sanskrit.
   Sarki Bhoj ya kasance mai bauta ne ga ubangiji Saraswati, kuma shi mutum ne mai matukar ilimi, da kuma son ilimi.
 Shi gwanin karance-karance ne, da rubuce-rubuce, musamman a fannonin falsafanci, kimiyya, fasaha, wake-wake, tarihi da sauransu.
  Sarki Bhoj ya wallafa littatafai kimanin 35 waɗanda har zuwa yau ana amfani dasu a kasar ta Indiya. A ciki akwai misalin 'Champu Ramayan' wanda yake kunshe da tarihi cikin wake, da kuma Rajniti Shastra mai ɗauke da ilimin kere-kere da Shringar Prakash mai ɗauke da kayatattun wakoki..
   Wata rana sai wani mai ilimi yazo ziyara ga Sarki Bhoj a fadarsa dake birnin Dhar, to amma kamar yadda kasar hausa ta kasance abaya, babu otal na saukar baki, don haka sai sarkin ya umarci wani bafadensa mai suna Amatya akan ya zagaya cikin gari ya nemi mutum jahili ya umarceshi daya fita daga gidansa dashi da iyalinsa domin baiwa wannan bako masauki.
   Amatya ya shiga gari yana ta lalube, kwatsam sai gashi gaban wani mutum masaki, yana ta saka a kofar gidansa.
  "da ganin wannan bagidaje ne", Amatya ya raya a ransa. Sannan ya gabata gareshi yana muzurai tare da faɗa masa umarnin sarki Bhoj.
  Koda wannan masaki yaji haka, sai baicewa ɗan aike uffan ba, ya kamo hanya zuwa fada.
 Da zuwansa ya faɗi gaban sarki yayi gaisuwa sannan ya fara rero wasu baitoci daya haddace a cikin littafin addininsu Sanskrit.
  Bayan ya gama, sai kuma ya shiga rera wata wakar, yana mai cewa:-
  Ya Sarki! ni kaina na wallafa wakoki, amma basu yi kyawu ba.
  Na tabbata, da himmatuwata, sam bazan rasa baiti ba.
  Ya kai Shugaba, takalman wanene aka yiwa ado da kambun tsoffin sarakuna?
  Ina mai jiran umarninka, shin rubutun wakoki ne ya zamar mini wajibi, ko saka tufafi, ko kuwa barin gidana da masarautar ka baki ɗaya..?
  Sarki da duk wanda ke wannan fada ya tsinkayu da hikimar wannan mutumi, musamman duba da cewar sigar dake gareshi ta kidahuman mutane ne marasa ilimi. Don haka sarki ya sauya shawara akan saukar bakonsa, yasa a nema masa wuri acikin gidansa ya kwana, masaki kuma yayi masa kyauta ya sallame shi.
(Ana lissafa wannan a matsayin yadda indiyawa ke fafutikar kwatar 'yancinsu tun a karni na goma sha ɗaya, da kuma yadda sarakuna ke baiwa mabiyansu damar shigar da koke a kodayaushe).
  Rannan kuma har ila yau, sarki Bhoj ya sake yin wani bakon mai Ilimi daga wata masarauta, sai suka fita kilisa bisa dokuna suna masu tattauna mas'alolin ilimi, basu ankara ba har sukayi nisa da gida.
  Don haka sai suka juyo da nufin komowa gida, amma sai hanyar da sukabi tun da fari ta ɓace musu.
  Suna dai ta tafiya basu san inda suke dosa ba, sai gasu kusa da wani ɗan kauye.
  Tun kafin su shiga ciki sukaci karo da wata tsohuwa, da alama tana cikin matalautan mutane duba da tufafin jikinta.
  Sai suka tsayar da ita suka tambayeta da cewa "Ya wannan tsohuwa, shin ina wannan hanyar take tafiya ne?"
  Tsohuwa tace "Wannan hanyar babu inda take tafiya, anan wurin kurum take a kwance, amma mutanen da suke tafiya akanta sune ke riskar wani wuri. Don haka sai ku faɗa mini su wanene ku?"
  "Mu matafiya ne" inji sarki Bhoj cikin kaɗuwa.
  "Ai matafiya biyu ne kaɗai anan duniya, daga Rana sai wata" inji tsohuwa. "Shin su wanene ku aciki?"
  Abokin Sarki Bhoj yayi farat yace " 'yar uwa, mufa baki ne"
  Tsohuwa tace "baki guda biyu ne kachal a duniya. Na ɗaya sunansa dukiya, na biyunsa kuwa sunansa Samartaka"
  "To mu sarakuna ne" inji Sarki Bhoj.
  "Ai kuwa sarakuna biyu garemu a duniyar nan, daga sarkin sarakuna Indra, sai allan mutuwa Tama. Shin waɗanne ne ku daga ciki?" tsohuwa ta sake jefa musu tambaya.
  Sukayi shiru suna kallonta cikin mamaki, sannan sai sukace "mu.. Mutane kurum masu juriya"
   Tsohuwa tace "ai kuwa anan duniya abubuwa biyu ne kaɗai masu juriya, daga ita duniyar kanta, sai kuma mace. Ni kuwa ban ganku da lulluɓi ba"
  Sarki Bhoj yace "yar uwa, munan da kike ganin mu waliyyai ne"
  Tsohuwa tace "waliyyai biyu ne fa a duniya, daga mutumci sai hakuri."
   Sarki Bhoj da abokinsa sukayi shiru suna nazarin abinda zasu ce, domin sun ɗauki abin a matsayin farmaki ga iliminsu, don haka suka kudurci aniyar lallai sai sun kure tsohuwa.
  Abokin sarki Bhoj yace "yar uwa, mufa masu balaguro ne"
  Tsohuwa tace "sam bakuyi kama da masu balaguro ba" tana mai girgiza kanta alamar rashin amincewa.
  Sannan ta kara da cewa "ai ruhi da ganyen bishiya ne kaɗai masu yin balaguro.. Ko akwai ɗaya a cikinku?"
  "to munan mun kasance talakawa ne" inji sarki Bhoj.
  "matalauta biyu ne a duniya. Na ɗaya shine ɗan marakin da akayiwa reno yana jiran yanka, na biyunsu kuwa itace budurwar da aka sanya a lalle" inji tsohuwa.
   Abokin sarki Bhoj yace "Haka ne, amma a zahiri mu fasihai ne"
  Tsohuwa tace "ai fasihai biyu garemu duk duniya, daga Hatsi sai Ruwa, shin a wanne babin kuke?"
  Ran sarki Bhoj ya sosu, amma dai ya kanne, yace " to munji, kinyi nasara akanmu, mun kuma karɓi faɗuwa"
  Sai tsohuwa ta sake kada baki tace "mutanen da akayi nasara akansu biyu ne anan duniya. Na ɗaya shine wanda yayi rance, har ya zamana bashi yayi masa katutu. Na biyu kuwa shine mahaifin budurwa maras ɗa'a. Shin meya hanaku tun da fari ku sanar mini gaskiyar ko su wanene ku?"
  Sarki Bhoj da abokinsa sukace "to me kike son muce ne? Ai ya kasance kamar bamu san komai ba, kece mafi sanin mu duka"
  Tsohuwa tayi murmushi, sannan tace "dukkan ku na lura kuna takama da dukiya gami da ilimi, ni kuwa nayi muku haka ne domin na nuna muku akwai abubuwan da kuka rasa sani na daga ilimi, amma tunda fari na gane cewar wannan Sarki Bhoj ne, wannan kuma bakon sane.."
  Daga nan sai ta nuna musu hanyar da zata kaisu birnin Dhar.
  Sarki Bhoj da abokinsa sukayi godiya ga wannan tsohuwa mai ilimi bisa darasin data koya musu, lallai sun gamsu da cewar akwai mutanen da suke kallo a matsayin kaskantattu amma sun ɗarasu sanin hikimomi, don haka har suka isa gida firarta kurum sukeyi.
 
SUBHANAKA LA ILMA LANA ILLA MA ALLAMTANA..

Thursday, 15 March 2018

HIKAYAR SARKI BHOJ NA HINDU