Wednesday, 6 December 2017

HIKAYAR MALLAM DILA WANDA YAJE LAHIRA YA DAWO

HIKAYAR SARKIN BIRAM DA BAFADENSA MALLAM DILA WANDA YAJE LAHIRA YA DAWO.
  (Hassada ga mai rabo Taki ce)

Sadiq Tukur Gwarzo, RN.

Lokaci mai tsawo daya gabata, a wani kauye anyi wani yaro mai wayo da hikima, sunan sa Ishaka, amma anfi masa lakabi da Mallam Dila saboda tsagwaron wayon sa.
   Mallam Dila yaro ne da bai wuce shekaru goma sha biyar da haihuwa ba, amma a bisa karan kansa ya kanyi tunanin abinda iyayensa suke da bukata, sannan da wurwuri yakan je ya samar musu dashi. Haka kuma gashi gwanin barkwanci da iya bada dariya.
   Wannan yasa duk mutanen kauyensu suke kaunar sa.
 Takanas wasu kanzo gida domin fira dashi abisa mararin samun nishaɗi.
    Rannan Mallam Dila ya tafi bayan gari yin itace wanda zai kawowa gyatumarsa don yin girki, sai kamar daga sama yaji kira..
  "Kai yaro, kai yaro dakata"
Abin da yaji ana cewa kenan.
 Sannan kafin ya ankara sai ganin mutane bakwai yayi a gabansa kowannensu akan doki.
  "Yaro, muna gama ka da girman Allah, a ina zamu samu rijiya ko tafki wanda zamu samu ruwa mu jika makoshin mu? Ka ganmu mun kwaso rana da kishirwa, har ma mun sauka daga turbar garin mu wajen neman ruwa" ɗaya daga cikinsu ya faɗa.
  Mallam Dila ya kalle su sama da kasa, "lallai da alamun waɗannan matafiya ne kuma attajirai", ya raya a zuciyarsa bayan ya kalli tufafin jikkunansu.
  "Ayya, naji tausayinku kwarrai. Sai dai ban san inda zaku samu ruwa anan kusa ba, amma kuna iya samunsa idan har zaku bini zuwa talautaccen gidan mu" inji Mallam Dila.
  Suka yi kallon-kallo a tsakaninsu, sannan ɗayansu ya umarci Mallam Dila yazo yahau gaban dokinsa, yayinda ɗaya daga cikinsu kuma ya karɓi itacen dake kansa, sannan suka nemi yai musu jagoranci izuwa inda gidan nasu yake.
  Da suka isa gidan, mallam Dila ya ya sauko daga doki, ya karɓi itacensa ya kaiwa mahaifiyarsa, sannan ya shiga jigilar samarwa da bakin sa ruwa isasshe da zasu sha, su kuma baiwa dabbobinsu.
   Bayan sun sha sun koshi, sai babban cikinsu wanda yafi dukkan sauran ado da kyakkyawar sura, ya dubi mallam dila yace "Yaro, shin kana da suna ne?"
   Mallam Dila ga girgiza kansa daga hagu zuwa dama, sannan yace "ko kana da wanda zaka bani ne?"
   Mutumin nan ya kalli yaro dakyau ya gyaɗa kansa sama sannan yace "Ko kasan wanene ni?"
   Nan ma Mallam Dila ya sake girgiza kansa, sannan yace "Ko kasan malami na a kauyen nan?"
    Wannan mutum ya cika da mamakin wannan yaro, domin wani bai taɓa masa irin wannan maganar ba, ya tambaye shi wani abu shima yayi masa tambaya da wani abu, amma yasan yaron bai san dawa yake magana ba.
  Don haka sai ya ciro zobe a hannunsa ya mikawa yaro, yace karɓi wannan zai nuna maka koni wanene"
  Sanan ya umarci abokan tafiyarsa dasu hau dawakansu su tafi.
   Bayan mutumin ya hau dokin nasa ne, ya ja linzamin dokin kaɗan gami da bugar matsematsin dokin da dunduniyarsa, sai kuwa dokin ya ɗanyi rimi sama yana karkaɗa kafafuwansa na gaba tare da haniniya, sannan mutumin yace "Dakyau yaro, kayi girma sosai, sai na ganka a Fadata ta Biram!! Kajiko?"
  Daga nan suka saki linzaman dawakansu, suka arce da gudu.
  Mallam Dila na tsaye a kofar gida yana ta faman jujjuya wannan zobe, sai daga baya ya lura da tambarin sarkin biram a jikinsa.
 " Wayyo!!!" ya faɗa cikin da-na-sani.
 " Ashe babban sarki Maje ne ke tambayar sunana naki faɗa masa".
  Ya ɗaga kansa yaga ko basuyi nisa ba, amma ina, ko kurar su ma baya iya hangowa.
  Kurum sai ya saduda, ya shiga gida tare da sanarwa iyayensa da kakansa wanda shine malamin sa, abinda ya faru.
  Bayan kwana biyu da faruwar haka, sai mutanen wannan kauye suka ce lallai ya kamata ya shirya ya tafi Biram don ziyartar sarki Maje kamar yadda ya jaddada masa a haɗuwarsu, watakila alheri ke jiransa.
 Haka kuwa akayi, Mallam Dila ya haɗa 'yan komatsansa, sannan ya nufi Biram shi kaɗai, ko ɗan rakiya ma babu.
  Biram babban birni ne mai cike da gine-gine na zamani da kuma manyan mayaka.
  Ana mata kirari da "Biram ta Hammaruwa, maida ɗan wani naki" saboda shaharar ta a zamanin tsohon sarki Hammaruwa.
Don haka, kasancewarsa bakauye tun daga farkon gari yake ta mamakin yadda kyawun garin da yanayin ɗabi'un mutanen suke. Kowa kagani tsaf-tsaf abinsa sai kace ranar bikin sallah.
  Da isar sa fada, sai ya tarar fadar wani babban zaure ne yalwatacce mai cike da mazaunai masu taushi, sai kuma sarki Maje wanda yake cikin kyawawan manyan tufafi, ya ɗaure saman kansa da rawani mai walwali, yana zaune daga can k'urya akan wani gado kasaitacce ana masa fadanci.
  Ga fadawa hagu da damansa suna masa ban-iska, ga wasu kuma zaune fululu sanye da tufafin askarawan sarki.
  Can daga gefe kuma mutan gari ne zazzaune, da alamar suna son suyi magana dashi ne bisa wata bukata.
  Don haka, sai aka nunawa Mallam Dila wuri cikin mutan gari akace ya zaune kafin layi ya iso kansa.
  Da yake sarkin mai raha da barkwanci ne, suna magana kus-kus da wani mutum wanda ya zube a gabansa, sai akaga ya ɗago kansa sama yana magana da murya sanyi sanyi cikin mulki, yace "Wacce kyauta ce tafi kamata mu bayar akai ga abin kaunar mu dake birnin Njimi.?"
  Nan fa fadawa sukai ta kawo son ransu, amma bai gamsar da sarki ba.
  Wani yace a tura farin doki kasaitacce, wani yace a samu kyakkyawar baiwa a tura, wani yace zinare ya kamata a aike dashi da dai sauran su.
  Ana haka sai mallam Dila ya ɗaga muryarsa yace "Ranka ya daɗe, a ra'ayi na gishiri yafi kamata a tura kyauta izuwa Njimi"
  Take, fada ta ruɗe da dariyar mutane, sunji zance na shirme daga bakin yaro, saboda gishiri abune maras daraja a biram sabili da yawan fataken dake kawo shi a koda yaushe.
   Mallam Dila baiyi kasa a guiwa ba yaci gaba da zancensa yana mai cewa "ita kyauta ga mutum kana bada ita ne ga abinda yafi darajantawa ba abinda kai mai bada kyautar kake darajantawa ba. Idan kuwa an lura, gishiri yafi komi tsada da karanci a Njimi, tun bayan yakin kabilun Zurami da yasa fatake suka k'auracewa wannan hanya"
   Sarki yayi shiru na ɗan wani lokaci yana mai cika da mamakin wannan batu na hikima daga yaro mai kananun shekaru haka. Sai daga baya ne sarkin ya gane ashe wannan yaron shine wanda ya taimakesu da ruwa kwanaki a sanda ya fita rangadi.
   "Hakika wannan zance na cike da hikima. Matso gareni yaro, daga yau na naɗa ka mukamin Birbal, zaka kasance tare dani cikin farin ciki da annushuwa".
  Sarkin ya faɗa yana mai cike da murmishi.
   Tun daga wannan rana ya zamo Mallam Dila ke rike da sarautar Birbal a birnin Biram, aikinsa kullum yana gefen sarki, kuma yana da ikon tsoma baki a duk wani lamari da yazo ga sarki.
  Kasancewar sarki Maje ba mai ilimi bane matuka, amma yana girmama ma'abota hikimomi da ilimai. Don haka yayiwa mallam dila wannan karramawa.
  Sai dai kuma hakan sai ya sanya tsana da kishin Mallam Dila a zukatan manyan fadawansa.
  Watarana wani bafade ke sanar wa sarki irin yadda fadawa keji a ransu bisa karramawar da yake baiwa sabon Birbal, watau mallam Dila. Sai kuwa sarki yace rabu dasu, gobe a fada zan nuna musu irin baiwar dake gareshi.
   Kashe gari, sarki da fadawa suna zaune a fada, sai sarkin yace "inada da tambaya a gareku da nake so ku amsa min ita da gaggawa".
  Fadawa suka amsa duka da cewa "muna sauraron ka sarkin Biram mai duniya".
  Sarki Maje yace "ku sanar dani adadin dawakan dake wannan birni ayau".
  Daga nan fa kowa yayi jugum-jugum yana tunani.
  Ana haka Birbal ya shigo, sai sarki ya jefa masa tambayar kamar yadda yayi ga fadawansa.
 Cikin hanzari Birbal yace "ya mai duniya, dawakai ɗari bakwai ne kachal suka rage a garin nan".
  Sarki yace "yaya akai kasan haka?'
  Birbal ya sunkuyar da kansa kasa cikin girmamawa yace "ranka ya daɗe, kwanaki biyu da suka wuce kasa ayi shelar cewa duk wanda keda doki a garin nan yazo tare dashi don yin rakiya ga Amininka sarkin Njimi da ya ziyarceka izuwa iyakar kasarka. A jiya ne ka tura waccan tawaga gagarumaa izuwa rakiyar sarkin, amma kace dakaru ɗari bakwai su zauna tsaron kasa, na tabbata kuwa dukkansu da dawakansu suke tare"
   Sarki ya tuntsire da dariya yace ''Haka nakeso Birbal, lalle ka cika yaro mai kiyaye abu da hazaka kuma"
  Wannan abu da akai sai tasa sarki ya kara sanya kauna da yardarsa ga Birbal, yayinda fadawa suka ɗora masa karan tsana matuka.
  Rannan a fada sai dukkansu suka duk'a gaba gareshi, sukace sam basa jin daɗin yadda yake yawan amfani da maganganun yaro karami yana barin tasu, hakika hakan zai iya jawowa masarautar Biram abin kunya da dariya daga sauran sarakunan birane.
  Sarki maje yace "kuyi sani, hikima da wayon wannan yaro Birbal ta ninka taku, amma idan baku yadda ba, zan nuna muku idan ya shigo fada".
  Daga nan sai aka cigaba da harkokin mulki, sarki na ganawa da jama'arsa yana jin koke-kokensu.
  Ana haka sai Birbal ya shigo, ya zube a kasa yayi gaisuwa ga sarki, sannan ya koma gefe ɗaya ya zauna.
  Sarki yace "Au, daman kuwa ina neman shawarar ku mutanen wannan fada, yau da safe wani yasa kafarsa ya hamɓari kirjina, wanne hukunci ya kamata nayi akan haka?"
   Fada tayi shiru kowa na tunani.
  Can, sai mutane suka soma bada ra'ayinsu.
  Wani yace "kamata yayi a gutsire karmfar, wani yace kamata yayi a tsire mutumin a kasuwa', wani yace "zaifi kyau a datse masa hannaye da kafafuwa", wani yace "ai kurum a sare kansa kowa ya huta.." Da dai sauransu.
  Birbal ne kurum baice wani abu ba.
   Sarki ya juya gareshi yana murmushi, yace "menene ra'ayinka Birbal?"
  Sai Birbal yace "ranka ya daɗe nafi ganin kamata yayi kasa ayiwa kafar wanda yayi wannan aiki takalmi na zinariya".
  Nan fa fada ta sake ruɗewa da dariya, saboda anji zance na wauta daga wurin yaro maras hankali.
   Sarki Maje yace "me yasa kace haka Birbal?"
   Birbal yace "ya mai duniya, abisa yadda ka bada labarin an dakeka a kirji alhali da walwala a fuskarka, ya tabbatar min da cewa wanda yayi aikin ba wani ne daga makiya ba. Don haka nayi hasashen ɗanka ko jikanka ka ɗauka kana masa wasa shikuma ya sanya k'afarsa akan kirjinka.
  Idan kuwa hakane, babu abinda yafi kamantuwa dashi sai a k'awata kafarsa da takalma na zinariya".
   Sarki Maje ya tuntsure da dariya cikin farin ciki, yace "Kwarrai kuwa haka ne, kunji abinda nake faɗa muku ko? Wannan ne dalilin dayasa nake bawa wannan yaro aminci da kulawa mai yawa".
    Da fadawa sukaga korafinsu ga sarki ba zai warware matsalar suba, ga kigayyar Birbal kullum sai karuwa take a zukatansu, sai suka soma shirin halaka shi domin maido da martabar su ga sarki.
   Akwai wani wanzami wanda aikinsa kurum yiwa sarki aski da kuma gyaran gemu idan bukata ta taso. Sai ya kasance watanni  biyu baizo fada sarki ya ganshi ba.
  A wata na uku sai gashi yazo don ya gaishe da sarki.
   Sarki ya tambayeshi shin lafiya watanninsa biyu baizo fada ba?   Sai wanzami yace "rakiya nayi ne ranka ya daɗe".
   "Rakiya zuwa ina haka"
Inji sarki.
  "Kaka nane ya rasu a kauye, don haka dana je an riga an kaishi kushewa, shine sai na bishi na raka shi lahira kurum".
Inji wanzam.
  Sarki ya kame na ɗan wani lokaci saboda kaɗuwar wannan zance. "Kai kuwa ina ka taɓa ganin anje lahira ba'a mutu ba kuma an dawo" inji sarki.
  "Ranka ya daɗe hakika gaskiya nake faɗa maka, naje lahira naga mahaifinka sarki Hammaruwa, naga kakanka sarki Birnima, dukkansu suna cikin wallwala da farin ciki".
  Sai anan ne sarki ya soma tunanin watakila wanzami ya samu taɓin hankali ne.. To amma sai wanzam ya hakikance da gaskiyar abinda yake faɗawa sarki.
  "Wannan abu da mamaki yake, to amma tayaya suka barka ka dawo" Inji sarki Maje.
  "Ranka ya daɗe ai lahira sauki gareta, matsawar kaje alhali baka kammala ayyukanka na duniya ba, tilas su dawo dakai ka karasa sannan ka koma". Wanzami ya bada amsa.
   "To yaya akai ka isa lahira kai kuwa?" Sarki ya kara tambaya.
 "A lokacin dana isa kabarin kakana, sai nasa aka buɗeshi na kwanta a gefensa na rufe ido ina ambatar sunayen ubangiji, mutane kuma suka rufeni da kasa, sai kurum ganina nayi a lahira". Wanzami ya baiwa sarki amsa da haka.
   Sarki yasa masu leken asirinsa suje su binciki wannan labari na wanzami.
 Kai tsaye kuwa suka je gidansa da tambaya, kuma akace tabbas watanni biyu kenan wanzam baya gida, kuma daya dawo yana ta rabon dukiyarsa yace wai kakansa ne ya bashi umarnin yayi haka a sanda ya riskeshi a lahira.
   Da sarki yaji wannan almara, sai ya yarda, harma yace yana so zaije lahira yaga yadda mahaifinsa da kakansa suke acan.
   Fadawa sukace "haba ranka ya daɗe, ina zamusa kanmu idan kayi watanni baka tare damu alhali makiya na iya amfani da damar su kawo hari garemu, gaskiya kar ka soma wannan tafiya".
   Abu kamar wasa fa sarki ya dage zaije lahira, amma da yaji babu goyon baya gareshi na tafiya lahira daga fadawansa, sai yace "to nifa a gaskiya inason sanin halin da iyayena suke ciki a lahira, don haka yaya za'ayi kena ?
  Sai wani yace "ai hakuri zakayi ka tura wani ya gano maka, idan da sako sai ka bashi yakai garesu".
   Sarki yace "to wa zan tura?"
  Nan take wani yayi caraf yace "sai a tura Birbal, domin shi keda hikima sama damu, zuwansa zaifi namu alfanu".
   Sarki ya dubi Birbal wanda tuntuni ya kasa magana saboda mamakin irin rainin hankalin da aka zowa sarki dashi, yace "Birbal, zaka iya yin wannan tafiya kuwa?"
  ƁCikin ladabi Birbal yace "ranka ya daɗe, zan iya yi domin cika umarninka". A zuciyarsa yasan gadar zare ake shirin kulla masa.
  Sarki ya cika da murna, sannan yace yana so yaje yayi shiri zai aike shi lahira wurin iyayensa.
  Birbal yace yaji ya gani zaiyi wannan tafiya bisa umarnin sarki, to amma yana so a bashi watanni uku ya gama shiri don yaje kauye yayi sallama da iyaye sannan yazo ya tafi.
  Sarki yace an yardam nasa.
 A cikin waɗannan watanni ukun, Birbal ya sanya wasu amintattun bayinsa suka haka masa wawakeken rami a makabarta da dare, sannan suka rufe shi daga sama da sigar kabari, suka fidda taga karama daga sama, sannan suka samu wata gawa suka binne a ciki.
  Anyi haka da kwana ɗaya sai Birbal yaje ga sarki yace ya gama shirinsa zai tafi.
  Sarki ya zaunar dashi ya zayyana masa sakwannin da yakeso ya isar ga kowanne mamaci daga magabatansa daya rasu, sannan dashi da mutanensa suka taru suka rakashi makabarta.
  Tun kafin su isa ma, waɗannan bayi na Birbal sunyi shiri a cikin tawagar 'yan rakiya, don haka ana isa makabarta sai suka nuna wannan sabon kabari tare da cewa shi yakamata a buɗe, tunda sabo ne, "da alamun mamacin bai riga ya riski lahirar ba zuwa yanzu" inji su.
  Nan take suka sa kayan hak'a suka soma buɗe kabarin.
   Da suka gama sai Birbal ya shiga ya kwanta, suka kawo ganyayyaki da tufafi suka yayyaɓeshi, sannan suka sanya turɓaya a samansa suka rufe.
  Daga nan fa fadawan sarki suka cika da murna, tsammanin su sun hak'awa Birbal ramin mutuwa, har da cewa "yayi tafiyar da bazai taɓa dawowa ba", to amma abinda basu sani ba shine ana gama rufe kasa, sai Birbal ya buɗe kofar wawakeken ramin da barorinsa sukayi ya shige. Da dare kuma amintattun bayin nasa suka zo suka fiddashi, sannan suka kaishi can wani kauye wurin wata 'yaruwansa ya ɓoye kansa acan.
  Bayan watanni biyu, rannan ana fadanci kwatsam sai ga Birbal ya shigo fada.
   Sanye a jikinsa tufafi ne masu kyau na kasaita, yana ta faman fara'a abinsa.
  Sarki Maje ya tashi zumbur daga kan gadon mulkinsa a lokacin daya haɓgoshi, ya taho ya rungumeshi yana mai yi masa barka da dawowa.
   Amma fa, fadawa a rannan sun cika da mamakin ganinsa, ji sukai kamar su kashe kawunansu don tsananin ɓacin zuciya.
  "Yaya ka samu iyaye na?, ina fatan suna lafiya.. ka faɗa mini abinda suke cewa game da mulki na" inji sarjin Maje cikin zakuwa.
  Birbal yayi murmushi ga sarki yace "ya mai duniya, hakika na same su lafiya, suna cikin walwala tabbas, kuma sunce kana matukar kokari yadda kake tafiyar da wannan mulki naka, don haka baka bukatar wasu shawarwari, kurum kacigaba da abinda kake yi". Inji Birbal.
  "Ai kuwa naji daɗin haka". Sarkin  ya faɗa. Sannan ya cigaba da cewa "tabbas nayi kewar rashinka a wannan fada maigirma, to amma sanar mini wacce bukata suke da ita daga gareni...
  Shin akwai wani abu da sukeso wanda zai inganta musu jindaɗi daga gareni?"
  "Eh, kwarrai kuwa!", Birbal ya bashi amsa.
  Sannan yaci gaba da cewa "Kakanka sarki Hammaruwa gemanya tayi masa yawa a fuska, kuma wanzamai irin namu sunyi karanci a lahira. Don haka yace ka aika masa wanzamin ka kwararre yayi masa aski".
  "Laaa, ashe lahira babu kwararrun wanzamai da yawa?. Ai kuwa ba zan bar kakana da gemanya biya-biya a fuskar saba, tilas na aike da wanzamina yaje ya gyara kyakkawar fuskarsa" inji sarkin.
   Nan take ya juya ga wanzam, yace "kayi maza gida ka soma shiri, mako mai zuwa zaka tafi lahira kayiwa kakana aski acan".
 Koda wanzam yaji haka, sai fa ya cika da tsoro, yasan karshen rayuwarsa ce tazo.
  Da fari kamar zai iya jurewa, amma daya tuno haɗarin dazai shiga sai ya firgita ainun, ya durkusa gaban sarki yana kuka da neman afuwa.
  "Ranka ya daɗe kayi mini rai, kada kasa a binneni da raina, na rantse da girman rawaninka sanyani akayi nai maka karya.. Sam banje lahira na dawo ba" inji wanzami cikin sheshshekar kuka.
   "Daman karya ka shirya mini?" Inji sarkin. "To suwaye suka sanya ka wannan aiki".
  Da hanzari wanzam ya shiga nuna su ɗaya bayan ɗaya, sannan ya shaidawa sarkin cewa kuɗi suka bashi suka nemi ya gamsar da sarkin cewa lahira yaje ya dawo.
  Koda fadawan nan suka gane asirinsu ya tonu, sai suma suka gabata gaban sarki suna afi da neman yafiya. Suna masu cewa kishi ne ya tunkuɗasu suka kullawa Birbal wannan makirci amma ba niyyarsu suci zarafin sarki ba.
 Ran sarki ya ɓaci kwarrai, sannan yasa duk aka ɗaure fadawan nan a turu, shikuwa wanzam sarki yace yabar masa kasarsa baki ɗaya.
   Daga nan sarki Maje yasa dokar cewa duk wanda ya sake shiryawa Birbal makirci, to kuwa tabbas sai yasa an sare kansa a tsakiyar kasuwa.
  Kunji mafarin yadda Birbal ya samu lafiya, ya aika iyayensa suka zo gareshi da malaminsa, yacigaba da rayuwa cikin farin ciki abinsa. Sarki Maje kuwa dakansa ke hawa don ya rakashi kauyensu sada zumunci lokaci zuwa lokaci.
   

2 comments: