Wednesday, 6 December 2017

TARIHIN ATTAJIRI ALH ALIKO DANGOTE

TARIHIN ATTAJIRI NA DAYA A AFIRKA, ALH ALIKO DANGOTE


Daga Littafin Kano cibiyar Kasuwanci wanda Marigayi Maje Ahmad Gwangwazo (Allah yajiqansa) ya wallafa.

Daga Sadiq Tukur Gwarzo

Shine Aliko ɗan muhammadu Gote ɗan Aliyu, dukkaninsu fulanin Kura ne ta jihar kano.
  An haife shi a shekarar 1956 miladiyya a unguwar Kududdufawa ta cikin birnin kano, sannan Kakansa na wajen Uwa marigayi Alhaji Sunusi Dantata ne ya yaye shi, domin tunda ya ɗauko shi sai ya danka shi a hannun shakikiyar mahaifiyarsa mai suna Hajiya Ammami, ita ce ta raine shi har girmansa, wanda sai daga baya ne Alhaji Aliko ya gane cewar Hajiya Mariya ce mahaifiyarsa.
  Bayan ya soma karatun muhammadiya a gida, sai aka sanya shi a makarantar boko, inda daga bisani ya samu damar karatu a makarantar sakandare dake Birnin Kudu, sai dai kafin ya kammala sai kakansa Alh Sunusi ɗantata ya ɗaukeshi daga makarantar, yace kasuwanci ya kamata yayi ba karatun boko ba.
  A wannan lokaci, wani gidan bulo aka buɗe musu a Unguwar kurnar Asabe, suka rinka kula dashi, amma shi Alhaji Aliko, yafi son karatun boko a zuciyarsa.
  Ance ya taɓa samun yayansa mai suna Alh Ummaru Gote domin ya taimaka a faɗawa kakansa a maidashi makaranta, amma abin ya faskara a lokacin. Sai daga baya ya samu nasarar kammla sakandare tare da tafiya jamiar Azhar ta Misra don yin digiri.
   Sannu a hankali sai Alhaji Aliko ya shiga kasuwancin sai da kayayyakin keken hawa, sannan ya ya faɗaɗa harkar kasuwancinsa izuwa Kwangiloli.
  Ance wata makarantar primary ya fara ginawa a garin Takai, daga nan sai wasu makarantun a birnin kudu, sai wani ɓangane na gidan gajiyayyu a mariri..
  Shi da kansa ya taɓa faɗin cewar da rancen Naira dubu ɗari biyar ya soma kasuwanci, wanda ya karɓa daga hannun ɗan uwan Mahaifiyarsa da sharaɗin zai biya a tsawon shekara, amma cikin nasara ya biya kuɗin a watanni shidda kachal saboda sa'ar daya samu a kasuwancinsa.
   A wajejen shejara ta 1972 miladiyya kuwa sai ya koma Legas inda ya shiga harkar Siminti a karkashin kawunsa Alhaji ƳUsman Dantata wanda akafi sani da 'A Makkah'.
  A wannan lokacin, ance Alhaji Aliko ya rinka safarar manyan Motoci daga kasar Amurka zuwa nan gida Nigeria, yana kuma shigo da kayyakin sufuri misalin sukari shinkafa da fulawa tare da fitar da kayayyaki irinsu coco, qaro ka kashu daga nan gida Nigeria zuwa waje.
  Daga nan kuma sai ya soma siyen hannayen jari daga manyan masana'antu. Inda ya soma da siyen hannun jari na kamfanin MTN, dana kamfanin Gishiri na jihar Ogun wanda daga baya aka siyar masa dashi kachokan.
  Haka kuma ance ya kafa bankin kasuwanci mai suna Liberty Merchant Bank wanda daga baya ya siyar dashi, ya kuma siyi hannun jari mafi tsoka a tsohon Bankin Gamji, sannan daga bisani a hankali ya buɗe kamfanin ɗangote cement a jigar Lagos. Tare da kafa kamfanonin fulawa a jihohin kano da calabar, da kuma kamfanin yin Taliya dana yin buhhuna a Lagos. Sai kuma kamfanin hako siminti a jihar kogi, da wani gagarumi wanda babu irinsa a Afirka dake Obajana.
  Haka kuma, ya shiga ɓangaren sufuri, wanda ance a kalla zuwa yanzu yana da Jirgin ruwa mai masa zirga zirga tsakanin kasashe, da kuma motocin tirela sama da dubu biyar.
   Babban darasin ɗauka a rayuwar Alhaji Aliko Dangote shine fafutika wajen neman arziki.
  Shi mutum ne mai faɗi-tashi, wanda yasanya lissafta hanyoyin shigowar dukiya a gareshi tana da wahala.
  Sannan kuma an sanshi da hangen nesa, domin ance a lokacin dazai kafa babban kamfaninsa na Obajana, sai daya siyar da kadarorinsa dake Ingila da wasu anan Nigeria, amma duk da haka kuɗin basu isa ba. Don haka daga baya sai ya nemi bashin Bankuna, yana mai rokonsu dasu tallafeshi ya samu nasarar kammala aikin daya faro, idan ba haka ba kuwa zai dulmiya ne baki ɗaya..
  Ai kuwa sai akayi sa'a suka sanya dukiyarsu acikin aikin saboda sun sanshi yana da kokari da hangen nesa a kasuwanci.
   A fagen kyauta kuwa shi gawurtacce ne, tunda an bayyana shi a Matsayin mutum mai matukar biyayya ga mahaifigarsa. Duk kuwa wanda yasan Hajiya Mariya Sunusi Dantata yasanta da ciyar da gajiyayyyu da taimakon marasa karfi a kullum. Wanda ance ita ke sanyawa yana bada dukiyarsa domin gudanar da waɗannan ayyuka na alheri. Sannan kuma sam baya mancewa da tsoffin aminansa.
  Akwai wani labari ma da wani abokinsa na yarinta ya taɓa bayarwa, inda yace akwai wani lokaci da yaso ya haɗu da Alh Aliko a lagos amma sai ya kasa saboda uzurorrika da sukai masa yawa.
   Sai wani direbansa na Tirela yace kazo ranar kaza, Maigida yana ganawa damu direbobinsa, anan zaka iya haɗuwa dashi.
  Hakan kuwa akayi, da ranar tazo sai mutumin ya kusanci Alhaji Aliko, ai kuwa da ganinshi sai Alhajin ya shaidashi. Bayan sun gaisa sai ya haɗa shi da masu kula da lafiyarsa, yace a sanyashi a tawaga zai neme shi daga baya. Daga nan Alhaji Aliko yaci gaba da harkokinsa.
  Mutumin yace bayan Alhaji Aliko Dangoye ya kammala aikinsa a wannan waje, sai suka ɗunguma har dashi ɗin a motoci izuwa wasu wuraren ya duba wasu aiyuka, sannan zuwa dare suka isa filin jirgin sama inda suka hau Jirgi mallakin Alhaji Alikon, wanda ya kaisu wata kasa ta turawa.
  Amma fa duk abinnan da ake, bai gana da Alhaji Alikon ba, domin ko acikin jirgin wurin da yake zaune daban, shikuwa Alhaji yana can nashi wurin daban.
  Mutumin yace sai kashe gari da dare, bayan an saukeshi a wani hotel an bashi abinci mai kyau ya huta, sannan akazo akace masa Alhaji nason ganinsa.
  Daga nan aka shigar dashi wani ofishi, inda yaga Ahaji Aliko zaune a kujera, a gabansa ga wayoyi nan burjik na amsa kira.
  Mutumin yace nan take Alhaji Aliko yayi masa maraba, sannan yace masa zasu gana na tsawon mintuna kaza, babu daɗi babu ragi.
  Ai kuwa nan take suka shiga firarrakin tsoffin abokanansu da ana tuno tsuhuwar rayuwa da yadda rayuwa ta canza. Alhaji Aliko ya rinka tambayarsa ina wane, ina wane, ya wane yake?
  Wani yaji ance ya mutu, wani kuma ace masa ba lafiya da dai sauransu.
  Da lokaci ya cika, sai Alhaji Aliko yacewa abokin nasa to yanzu za'a mai dakai gida, sannan za'a kawo maka tirela kaza ta abinci, ina so ka baiwa wane da wane da iyalan wane.. Kai kuma abu kaza da kaza ne naka.
  Mutumin yace ya nemi Alhaji Aliko ya bashi lambar wayarsa, amma sai Alhajin ya karɓi tashi yace yaje kurum zai nemeshi da kansa.
  Ai kuwa yace a ranar da ya kammala rabon kayayyakin da aka bashi bisa amana, da dare sai kurum yaga kira da lambar kasar waje. Yana amsawa yaji Alhaji Aliko yana masa godiya bisa yadda ya rike amana..
  Mutumin yace babban abin daya bashi mamki shine yadda har Alhaji Aliko Dangote yabi diddigin aikin daya bashi..
  'Ya'yayen Alhaji Aliko Dangote sune:-
Hajiya Mariya, Hajiya Halima da Hajiya Fatima.
  Dafatan Allah yayiwa dukiya albarka, ya kara masa tausayi da taimakon talakawa ami

No comments:

Post a Comment