TARIHI: MULKIN FULANI A KANO, DA GWAGWARMAYAR RIKON SARAUTA.
Kashi na huɗu
Daga Sadiq Tukur Gwarzo, RN
08060869978
Sarki Ibrahim Dabo jarimi ne, mai kwazo da gwarzantaka a fagen fama.
Anace masa saifullahi saboda kafurai da dama sun mutu daga kaifin takobinsa.
Ya kashe 'yan taadda masu yiwa addinin Allah bore da 'yanfashi masu kwace dukiyoyin mutane babu adadi.
Da kansa yake hawa ya jagoranci yaki domin cinye gari. Kuma bai taɓa fita yaki baici nasara ba.
A zamaninsa ya tarawa kano gagarumar dukiya. Ya tara bayi da dawakai da kayan faɗa masu ɗimbin yawa.
Ya shimfiɗa adalci, an kuma samu zama lafiya, har takai mutane na barin kofofinsu da dare basa tsoron ɓarawo. Dabbobi kuwa na yawatawa a gari ba tare da maisu ba.
Sannan saboda kwanciyar hankali mutum na iya tasow tun daga Kukawa ta daular Borno ya riski kano babu fargabar fashi. Haka kuma tun daga kano har ya riski tafkin kwara yana cikin aminci.
Sarki Ibrahim Dabo ya mulki kano na tsawon shekaru 26 da watanni 2 da kwanaki 15. Ya rasu a ranar wata jumu'a, 9 ga watan safar gabannin sallar jummu'a.
A wannan rana, mutanen kano sun ɗauka karshen duniya ne yazo, don haka kowannensu mutuwa zaiyi, saboda tsananin kauna da shauki da girma-mawar da suke masa.
Allahu Akbar. Allah yajikansa da rahama.
Shi bafillatani ne mai kyan sura, wanda ya fito daga jinsin sulluɓawa.
Sulluɓawa kuwa jam'i ne na sulluɓe, kalmar da akace an samo ta daga kakansu ko ace asalin wanda zuriyar ta fito daga tsatsonsa mai suna Sisillo. Shikuwa Sisillo, ai miji ne ga bafullatanar nan ta jinsin Toronkawa mai suna Chippowo, kanwa ga bafullatani batoranke Mallam Usmanu Toroddo, waɓda yake kakan-kakan shehu Usmanu Mujaddadi ɗan fodio.
Don haka ake ɗaukar jinsunan sulluɓawa da toronkawa na fulani a matsayin 'yanuwan juna. (Ado-Kurawa 1989:45-49).
Asalin sulluɓawa wangarawa ne, watau ana iya cewar kakanninsu ne suka taɓa zuwa kano zamanin Sarkin Kano Muhammadu Kanajeji har suka kawowa garin musulunci. Amma suna da alaka da yarukan Mandigo dana Mandika na yankunan Mali.
Sunan asalin yarensu shine wakore, daga baya suka nutse cikin fulatanci yayinda suka mance yarensu suke yara fulbe (Usman 1974: 168-169).
Izuwa yanzu kuwa yana da wuya ko a gidan sarautar kano da jikokin marigayi mallam Ibrahim Dabo ke mulka kaji ana fulatanci, domin tuni sun rikiɗe izuwa hausa zuryan.
An kuma samu cewar jinsin sulluɓawa, sunfi kowanne jinsi tsari mai kyau acikin kabilun fulani tun kafin jihadin shehu Usmanu, domin kuwa suna da shugabancinsu mai suna 'Sarkin Sulluɓawa' a duk inda suke.
Kuma a zandam suka soma zama, daga bisani suka rinka kwararowa yankunan katsina, zariya, sokoto da rima da sauran yankunan hausawa.
Sannan kuma, tun da jimawa suna rike ne da addinin musulunci bisa kyakkyawar turba. Don haka da yakin jihadi ya ɓarke, 'yan kaɗan daga cikinsu ne suka goyi da bayan sarkin gobir, amma mafi yawansu suna cikin waɗanda suka bada gagarumar gudunmuwa wajen samun nasara, don haka nema ɗansu ya samu zamowa sarkin kano.
SARKI USMANU DAN IBRAHIM DABO
Bayan Allah ya karɓi ran sarki Ibrahim dabo, sai sarkin musulmi na lokacin Aliyu ɗan Muhammadu Bello ya naɗa Usmanu ɗan marigayi Sarki Ibrahim dabo a matsayin sarkin kano.
Ance shekaru uku akayi cif ana zaune lafiya da farkon mulkinsa, daga nan kuwa sai musifu suka rinka bayyanuwa.
Da fari dai wani mai suna Hamza shine ya soma yin bore. Ya tara tawaga yana kai farmaki ga mutane, amma daga bisani sai yabar kano izuwa kasar Bauchi. Amma duk da haka dai sarkin ya kafa runduna ya ajiyeta a Rumo ya sanya wani barde Guru na jagorantar ta.
An gama wannan kenan sai kuma da wani ɗan ta'adda daga Haɗeja ya bijiro yana uzzurawa mutane.
Can, Sai kuma ga sarkin Damagaram shima ya kunno da tasa fitinar.
Shi sarkin Damagaram ya sauka ne a Chiromawa tare da shafe watanni biyu yana kame mutane a matsayin fursunoni. Har sai da aka yake shi yana wannan garin sannan aka zauna lafiya.
An gama wannan kenan sai kuma ga Sarakunan Gobir, katsina dana Damagaram sun haɗa karfin dakaru suka nufo kano da yaki.
Suka nufo kano suna kashe musulmai.
Ance sun sauka a 'dukawa' ne tare da kashe dukkan musulmi da rushe gidajensu dake wurin. Amma sai Allah ya kuɓutar da musulmin kano suka koma da baya haka siddan ba tare da wani dalili ba.
Hakika a zamanin Sarkin Kano Usmanu, kano tasha wahalar yaki da rashin nasara daban-daban.
A zamaninsa ne Mallam Dabo Dambazau ya rasu, sai sarkin ya naɗa ɗansa mai suna Muhammadu kwairanga ya hau karagarsa. Haka ma da Madaki Ummaru ya rasu, sai ya naɗa ɗan uwansa Muhammadu Hadiri mukaminsa. Sannan da Alkali Ashafa ya rasu, nan ma sai ya naɗa Mallam Muhammadu Zangi a mukaminsa.
Kai bama suba, duk wani mai mukami daya rasu a zamaninsa sai daya naɗa ɗansa ko ɗan uwansa a kujerarsa, saboda cigaba da abinda mahaifinsa ya ɗorar.
Shi kuwa wancan bahaɗeje mai suna Buhari daya tashi fitinarsa sai daya kashe mutane da yawa, maza da mata da kananun yara.
Shine ma ya halaka jikan shehu Usman Danfodio mai suna Hassan ɗan Dambo. Don haka wasu ke danganta halayyarsa data Mu'awiyya wanda ya halaka jikan Manzon Allah (s.a.w).
Sannan kuma ya halaka mahaddata alkurani da dama.
A karshe sai Allah ya yiwa Sarki Usmanu ɗan Ibrahim Dabo rasuwa ana tsaka da wannn fitina bayan ya shafe shekaru 9 da watanni 9 yana mulkar kanawa.
Da fatan Allah yajikansa amin.

No comments:
Post a Comment