AL'ADA MAI BAN MAMAKI: DALILIN RASHIN WANKA A KABILAR HIMBA
Sadiq Tukur Gwarzo, GGA
08060869978
Kabilar Himba da ke kasar Namibia rukunin wasu kaɗaitattun mutane ne waɗanda ɗabi'an su suka zamo bare, ko ace ababen mamaki ga sauran mutanen duniya.
Akan kira su da suna Ovahimba ko Omhimba, suna rayuwa ne a yankin Kunene cikin kasar Namibia.
Daga cikin al'adun su da suka sha banban da mafi yawan sauran al'adu, akwai al'adar su ta tarbar baƙo da mata domin yin jima'i da su, da kuma sanyawa jarirai tsakiya a wuya tun suna zanin goyo.
Sannan basu cika cuɗeɗeniya da sauran kabilu ba balle har a samu sauyin al'adun da suka yi gado kaka da kakanni, waɗannan mutanen suna matukar kokari wajen ganin basu yi aron wata baƙuwar al'ada ba komai kyawunta, don haka muna iya cewa mafi yawan ababen da suka yi riko tun na kaka da kakanni ne.
Sana'o'in da mazajen kabilar suka fi riko dasu sune kiwo da noma, matan su kuwa sunfi damuwa da shiga daji samo itacen hura wuta don girka abinci da kuma jigilar samar da ruwan sha ga ahalin su.
Suna bauta ne ga allolin iyayen su, sannan mazaje na auren mace sama da ɗaya, suna kuma yiwa yara mata aure tun da kuruciyar su.
Babban abin mamaki dangane dasu shine rashin yin wanka da ruwa. Yana daga al'adar da suka yi gado ta rashin wanka da ruwa kwata-kwata a rayuwar su, dalilin haka kuwa ance baya rasa nasaba da rashin kyawun yanayin yankin da suke raye. Yankin su ya shafi sahara ne, samun ruwa na da matukar wahala a tattare dasu. Don haka darajar sa ya sanya suke ganin tamkar asara ne a kwarar dashi wajen wanke gangar jiki.
Sai dai kuma hakan bai sanya sun zama ƙazamai munana ba, ta yadda suka bullo da wata dabara wajen tsaftace jikin su wajen amfani da albarkatun dake zube a yankin nasu.
Dabarun sune; goge jikkunnan su da wata irin kuɓewa ja dake fito musu, sai kuma yin sirace a kullum don tsaftace jikkunan su.
Yadda suke siracen shine, ana zuba garwashi a rufaffen mazubi mai cike da garin magani da kofa a sama, don haka da zarar hayaki ya soma tashi sai mutum ya durƙusa yana mai kara jikin sa ga tururin wanda zai rinƙa shiga sassa daban daban na jikin yana tsaftace shi.
Ƙabilar Himba na da matukar son baƙo, tare da kyautata masa, amma fa basa bari baƙuwar al'ada ta gauraya da tasu.
No comments:
Post a Comment